Sake naɗa Sanusi Sarkin Kano ya fi komai daɗi a wajena — El-Rufai

El-Rufai ya ce wannan yanayi ya faranta masa rai fiye da komai.

Sake naɗa Sanusi Sarkin Kano ya fi komai daɗi a wajena — El-Rufai

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwarsa.

El-Rufai, ya bayyana hakan ne a yayin taron Arewa Tech Fest da aka gudanar a Kano ranar Laraba.

Taron ya tara ’yan siyasa da ƙwararru don tattauna ci gaban da ake samu a Arewacin Najeriya.

Manyan mutane, ciki har da gwamnonin jihohin Kano, Katsina, da Zamfara, sun halarci taron.

El-Rufai ya ce, “Dawo da Mai Martaba kan sarautar Kano, ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwata, kuma ina so na taya ku murna.”

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7