Sake tsayawa takarar Buhari rahama ce ga ‘Yan Najeriya
Assalam edita. Babu shakka bayyana aniyar sake tsayawa takara a zabe mai zuwa da Shugaba Buhari ya yi wani abun farin ciki ne da alfahari ga mu ‘yan Najeriya musamman ‘yan Arewa, la’akari da irin kyawawan manufofin dake kunshe a cikin zuciyar Shugaba Buhari. Kuma zabensa a matsayin shugaban kasa karo na biyu wajibinmu ‘yan […]
Assalam edita. Babu shakka bayyana aniyar sake tsayawa takara a zabe mai zuwa da Shugaba Buhari ya yi wani abun farin ciki ne da alfahari ga mu ‘yan Najeriya musamman ‘yan Arewa, la’akari da irin kyawawan manufofin dake kunshe a cikin zuciyar Shugaba Buhari. Kuma zabensa a matsayin shugaban kasa karo na biyu wajibinmu ‘yan Arewa ne koda kuwa sauran bangarorin sun ki shi a Najeriya, domin naka sai naka.
Dan haka ina kira ga ‘yan uwana ‘yan Arewa da mu baiwa wannan dattijo dukkanin goyon baya da hadin kai domin ganin ya sake lashe zabe a karo na biyu, domin samun damar ƙara sa ceto yankunanmu na Arewa da wasu miyagu suka mayar tamkar sansanonan yaki. A karshe muna fatar Allah Yasa wannan takara tasa karo na biyu ta zama alkhairi garemu ga kasarmu Najeriya baki daya ameen. Saƙo
Daga Ashiru Lawal Nagoma Ruwan Ɓaure Gusau, Jahar Zamfara. 08128828467.