Sakkwatawa 9 sun rasu a hatsarin mota a hanyar Legas
Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Asabar, yayin da matasan ke kan hanyarsu ta zuwa Legas.
Mutum tara ’yan asalin Ƙaramar Hukumar Yabo da ke Jihar Sakkwato, sun rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Legas.
An ce mamatan sun kan hanyarsu ta zuwa jihar domin gudanar da kasuwancinsu lokacin da hatsarin ya auku.
- ’Yan bindiga sun sace ’yan uwan juna 3 tare da gawar mahaifiyarsu a Benuwai
- Komawar Sadeeq Garo APC alheri ne ga Kano — Dankabo
Da yake martani kan lamarin, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar mazaɓar Yabo, Honarabul Abubakar Shamaki Yabo, ya bayyana alhininsa kan rasuwar matasan.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce rasuwar matasan babban rashi ne ga iyayensu, al’ummar Yabo da ma Jihar Sakkwato baki ɗaya.
“Na yi matuƙar baƙin ciki da samun wannan labari. Mun rasa matasa tara ‘yan Yabo masu ƙwazon neman na kansu. Wannan babban rashi ne ga iyalansu da al’ummar mazaɓar baki ɗaya,” in ji shi.
Ya ce matasan sun bar gidajensu ne da burin neman halal da inganta rayuwarsu, amma abin takaici suka rasa rayukansu kafin su isa inda suka nufa.
Yabo, ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansu da rahama, Ya kuma bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.
Haka kuma, ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su ƙara kula da hanyoyi domin rage yawan haɗuran mota.
Ya kuma shawarci matasa da su riƙa amfani da damammaki da ayyukan yi da ke jihohinsu, domin rage yawan tafiye-tafiye masu nisa.