Sakkwatawa na fama da matsalar rashin ruwa

Al’ummar birnin Sakkwato sun shiga mawuyacin halin rashin ruwa bayan da kamfanin lantarki na kasa ya yanke wutar lantarki daga Hukumar Ruwa ta jihar saboda yana bin ta bashin Naira miliyan 54. Rashin ruwan da aka shafe kwanaki ana fama da shi, sakamakon gaza sasantawa a tsakanin bangarorin biyu, ya sanya jama’ar gari fita neman […]

Sakkwatawa na fama da matsalar rashin ruwa
Sakkwatawa na fama da matsalar rashin ruwa

Al’ummar birnin Sakkwato sun shiga mawuyacin halin rashin ruwa bayan da kamfanin lantarki na kasa ya yanke wutar lantarki daga Hukumar Ruwa ta jihar saboda yana bin ta bashin Naira miliyan 54.

Rashin ruwan da aka shafe kwanaki ana fama da shi, sakamakon gaza sasantawa a tsakanin bangarorin biyu, ya sanya jama’ar gari fita neman ruwan sha da na sauran ayukkan yau da kullum zuwa wasu sassa.
Wakilinmu ya gane wa idonsa yadda mutane ke doguwar tafiya a kafa da kan ababen hawa zuwa gulbin Sakkwato don debo ruwa tun misalin karfe 12:00 dare har zuwa 4:00 na safiya, inda a yanzu ake sayar da jarkar ruwa a kan Naira 20, a wasu bangarorin ma har Naira 100 ake sayar da ita.
Wata majiya ta kusa da hukumar ruwan da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa an yanke wutar hukumar ne saboda bashin Naira miliyan 54 da ake bin ta, kuma babu wani shiri na biyan kudin.
Aminiya ta nemi jin ta bakin Shugaban Hukumar Ruwa ta Jihar Sakkwato Alhaji Moyi Tambuwal kan wannan lamarin amma ya ki cewa komai, inda ya ce Kwamishinan Ruwa na Jihar ne ya kamata manema labarai su tuntuba kan lamarin, sai dai yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kwamishinan ya ci tura.