Sakkwatawa sun yi maraba da sabon Waziri
Sakkwatawa sun yi murnar nadin Sabon Wazirin Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid da Gwamnatin Jihar Sakkwato karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ta yi. Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta mika sunayen mutum uku ga Gwamnatin Jihar Sakkwato domin ta zabi mutum daya daga cikinsu, sannan gwamnatin ta dauki Farfesa, wanda hakan ya […]

Sakkwatawa sun yi murnar nadin Sabon Wazirin Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid da Gwamnatin Jihar Sakkwato karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ta yi.
Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta mika sunayen mutum uku ga Gwamnatin Jihar Sakkwato domin ta zabi mutum daya daga cikinsu, sannan gwamnatin ta dauki Farfesa, wanda hakan ya yi wa fadar da al’ummar jihar dadi.
Za a nada sabon Wazirin ne gobe Assabar tare da wasu hakimai guda uku, Alhaji Kabiru Cigari da Alhaji Nasiru Shehu Usman da Alhaji Sada Abubakar Dikko, a matsayin Sarkin Sudan na Wurno da Sarkin Yamman Dogon Daji da Hakimin Gande.
Wadannan bayanai suna kunshe ne a wata takarda da Sakataren Majalisar mai alfarma Sarkin Musulmi Umar Faruku Ladan ya sanya wa hannu, sannan aka raba wa manema labarai, sannan kuma nadin ya fara aiki ne tun daga ranar 29 ga watan Nuwaban da ya gabata.
Kafin nadin, sabon Wazirin malami ne a Jami’ar Usman danfodiyo a bangaren harshen Larabci kuma shi ne shugaban kwamitin tattara bayanan ganin wata na fadar Sarkin Musulmi.
Murtala Sambo Bazzah ya nuna farin cikinsa kan nadin Waziri, inda ya ce mutum ne mai kamala da mutunta jama’a.
“Wadanda suka yi nadin sun yi zurfin tunani da suka zakulo shi, domin ba zai ba su kunya ba, domin halinsa na dattako da rike alkawali da aiki tukuru. Halinsa ne ya sanya Sakkwatawa suka yi murna da farin cikin nadinsa, domin sun san an yi abin da ya kamata don zai kara daga martabar Jihar Sakkwato,” a cewarsa.