Sakkwato za ta kashe Naira miliyan 174 don ciyarwar azumi
Gwamnatin Jihar Sakkwato za ta kashe Naira miliyan 174 kan ciyar da al’umma a lokacin azumin watan Ramadan na bana, a cibiyoyi 84 da ke cikin birnin Sakkwao da wajensa.Gwamnan Jihar, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya sanar da haka a wurin bikin gidauniyar Naira miliyan 25 da kungiyar Izala ta shirya a matakin jiha […]
Gwamnatin Jihar Sakkwato za ta kashe Naira miliyan 174 kan ciyar da al’umma a lokacin azumin watan Ramadan na bana, a cibiyoyi 84 da ke cikin birnin Sakkwao da wajensa.
Gwamnan Jihar, Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya sanar da haka a wurin bikin gidauniyar Naira miliyan 25 da kungiyar Izala ta shirya a matakin jiha a Masallacin Rokon Ruwa da ke Unguwar Gayu a birnin Sakkwato.
Gwamnan wanda Kwamishinan Al’amuran Addinin Musulunci, Alhaji Tukur Alkali ya wakilta ya ce sun yi shiri gamsasshe domin taimaka wa al’ummar jihar a lokacin azumi da kuma sauran lokutan da ba na azumi ba, saboda a kowace shekara sukan kara kudi ne domin la’akari da bukatun al’umma musamman masu azumi.
A cewarsa, an kirkiro ma’aikatar ce domin taimaka wa jama’a ta fannin addini kuma sun gina makarantun Islamiyya da yawa a jihar da ba ladanai da limamai albashi a kowane wata da gyara gidajensu.