Sako da jan hankali ga Sanata Kanti Bello
Asakala dai ta sarke a Jihar Katsina, tsakanin Sanata Kanti Bello da dan takarar gwamnan jihar a APC, Alhaji Aminu Bello Masari. KABIR SAKAINA LAYIN ’YANGORO MALUMFASHI (08095968366), ya shiga tsakani, ga abin da yake cewa: Na dade da sanin Kanti Bello a dattijo ne mai dattako. Yana girmama duk wanda ya dace a girmama, […]
Asakala dai ta sarke a Jihar Katsina, tsakanin Sanata Kanti Bello da dan takarar gwamnan jihar a APC, Alhaji Aminu Bello Masari. KABIR SAKAINA LAYIN ’YANGORO MALUMFASHI (08095968366), ya shiga tsakani, ga abin da yake cewa:
Na dade da sanin Kanti Bello a dattijo ne mai dattako. Yana girmama duk wanda ya dace a girmama, sannan mutum ne mai saukin kai. Yana samun girmamawa daga Katsinawa da manya-manyan ’yan siyasa. Tarihin manyan ’yan siyasar Katsina ba zai cika ba har sai sunansa ya bayyana, musamman a Shiyyar Daura.
Lokacin da ya shiga cikin jerin masu zawarcin takarar kujerar gwamnan Jihar Katsina a jam’iyyar adawa ta APC, an ce an jiyo shi yana cew: “Duk wanda shugabannin jam’iyya suka tsayar a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani, za mu amince da shi, sannan za mu ba shi goyan baya dari bisa dari.” Har ya kara da cewa: “Mu mun san mulki na Allah ne, Shi ke ba da shi ga wanda Ya so, a duk lokacin da Ya so.”
Da yawan Katsinawa sun jinjina wa mai girma Kanti a kan wannan kyakkyawan kalami nasa, har ta kai ga ya kara samun daukaka a zukatansu.
Amma kash! Bayan kammala zaben fitar da gwani da aka gudanar, inda Allah Ya ba tsohon Shugaban Majalisa Aminu Bello Masari nasarar lashe zaben da, sai kuma aka jiyo Kanti na fadin wai tsohon Masari ba shi da cikakkun takardun makaranta da ya ce yana da su, har ma yana shirin kai kara kotu don a dakatar da shi.
A iya bincikena da nazarina, ina ganin wannan zargin ya samo asali ne tun daga dakile tazarcen Obasanjo da shi Masarin ya yi ruwa da tsaki. Bayan binciken da majalisa ta yi a kan zargin, gaskiya ta tabbatar da kyawun takardunsa, inda ya ci gaba da zama a kan kujerarsa ta Shugaban Majalisa.
A hankalce, babu yadda za a yi a samu dan majalisa da gurbatattun takardu, har shekaru 8, tare da rike mukamin Shugaban Majalisa da gurbatattun takardu, sannan ya ci gaba da jan ragamarsa. Tambaya a nan ita ce, rashin masu ilimi ne a majalisa ya sa suka kasa kakkabo jirgin Masari, suka bari jagoransu na jan su cikin rashin wadatar ilimi ko kuwa wani boyayyen al’amari ne ya sa suka kau da kai suka bar shi a babbar kujera da takardun bogi?
A lokacin da Masari ke Shugaban Majalisar Wakilai, Kanti na Majalisar Dattijai, haka kuma ba mu taba jiyo shi yana jan hankalin zauren majalisar na yiwuwar tsaftace majalisa da masu kyawawan takardu ba. Ya ja baki ya yi gum. Idan kuwa har haka ta tabbata (Masari ba shi da kyawawan takardu) amma ’yan majalisa (har da Kanti) suka yi rufa-rufa, kuka ja baki kuka yi shiru, to ban ga dalilin da za a tono wancan kashin da kuka binne don kar ya dame ku da wari ba, in dai ba ka shirya toshe hancin ka ba ne.
Tun da farko me ya sa kuka yarda, kuka aminta aka je aka yi zabe da wanda kuke zargin ba shi da kyawawan takardu? A matsayin Kanti na tsohon dan siyasa, wanda ya san gaba da baya, ya san ciki da bai, ya kuma san halin Katsinawa da halin da Katsinar take ciki na neman dauki daga kwararrun ’yan siyasa, masana masu burin ciyar da jihar gaba (irin Kanti), to bai kamata ya zargi Masari da rashin ingancin takardu ba.
Yau da Kanti tsayawa ya yi tsayin daka wajen ganin jam’iyyarsu ta APC ta kai ga cin ma nasara a babban zabe mai zuwa, na tabbata da ba za ka ji kalaman al’umma na yawo a kansa ba. Da alama zafin kaye ne ya sa shi sanbatun cewa wai Masari ba shi da kyawawan takardu.