Sako daga gare ni ‘Almajiri’ zuwa ga iyayena

Zuwa ga Baba da Inna. Ina godiya kwarai da kuka kai ni makarantarAllo saboda kwadayi da fatan da kuke da su na ganin na sauke Alkur’ani mai tsarki na kuma haddace shi. Na gode sosai da wannan fata taku. Amma Baba, ka dauko ni ka damka ni a hannu Malam a gidansa, to, yau ga […]

Sako daga gare ni ‘Almajiri’ zuwa ga iyayena

Zuwa ga Baba da Inna. Ina godiya kwarai da kuka kai ni makarantarAllo saboda kwadayi da fatan da kuke da su na ganin na sauke Alkur’ani mai tsarki na kuma haddace shi. Na gode sosai da wannan fata taku.

Amma Baba, ka dauko ni ka damka ni a hannu Malam a gidansa, to, yau ga ni a titi ina ta gararamba. Baba a lokacin da ka kawo ni, ba ka ga yanayi da halin da sauran yaran wurin suke ciki ba, ko ka dauka duk marayu, marasa iyaye ne a wurin?

Shi ke nan Baba, ni ma ga ni nan na saje, tamkar yaran nan da ka tarar a ranar da ka kawo ni, cikin tsumma da kazanta. Baba, a yau na kasance abin kyama, ba mai so in kusance shi saboda zarnin fitsarin da ke jikina, tun da har yanzu ban daina amalala ba. Ga shi ba damar in shiga masallaci don yin Sallah, tun da na ji an ce mai dauke da najasa ba zai yi Sallah ba, kodayake har yanzu ko ma Alwalla ban iya ba; tun da Malam bai fara koya mana komai a cikin ibada ba.

Inna, danki yana cikin matsananciyar yunwa amma ke ta yaya kike samun natsuwar zama ki ci ki koshi, alhalin ga danki a nan sai ya yi bara gida-gida kafin watakila ya dace da gidan da za a kira shi a sam masa dan abin da zai sa a bakinsa? Ko ya ishe shi ko bai ishe shi ba ma, oho! Babu wanda ya damu da ya san koshin cikina, Inna. Inna ki tuna, ke fa kullum sai kin dafa sabon abinci sannan ku ci ku koshi, ni kuwa ga ni a nan ba na samun komai sai kwananne ko wanda ya dauko lalacewa, kafin a kira ni a ba ni. Sai dai idan na yi kwadayin cin abinci sabo, to, sai in dauki jiki in tafi bara gidan mai tuwo-tuwon sayarwa, idan wani ya saya, ya ci ya raga, sai ya juye mani a kokon barana. Haka zan ci, tun da ba ni da zabi.

Idan na yi bara ban samu ba, Inna dole ne in garzaya gidan karuwai in tambaye su wanki. Haka za su jefo mani kayansu, har da kananan kayan jikinsu da ba su ma kamata ga mai kananan shekaru irina in gan su da idona ba amma su ba ruwansu, har da masu dauke da kazantar mata suke ba ni. Haka zan sa hannuwana biyu-biyu in wanke, don a biya ni, in samu in sayi abinci.

Inna, ya kike samun kwanciyar hankalin kwanciya a kan katifa ko tabarma har ki lulluba da bargo ko mayafi, alhalin ga danki a nan kwance a kan tantagaryar daben zauren gidan malam, ko tabarma babu? Domin tun ranar da Baba ya ajiye ni ya tafi, wani gardi ya kwace mani tabarma da mayafina.

Inna, na so a ce iwar haka a dakinki nake kwance, don in ji dumin jikinki. Inna, ki tuna fa ke ce kike kara lullube ni a yayin da na ture abin rufana. Inna, sanyi yana damuna, domin ana sanyi sosai a nan. Inna, ko na kwanta ciwo ba mai kula da ni balle ya ba ni magani. Idan ma ciwon ya yi tsanani, aka kawo ni cikin gidan Malam, haka matar Malam za ta yi ta daka mani tsawa, tana dukana idan ta tashe ni ina kurba ’yar furar da ta kawo mani.

Inna, idan na yi dare a waje wurin barar ’yar taliya da sauran shayi a teburin maishayi, na dawo sai in tarar Malam ya kulle zaurensa. Haka zan kwanta a titi a takure, a rakube har gari ya waye. Inna, kuma koda mun hadu da Malam da safe baya ma tambayata a ina na kwana, domin bai ma lura da cewa ban kwana a gida ba.

Baba da Inna, yanzu haka ba ni da takalmi a kafata. Haka nake tafiya ba takalmi, cikin karangiya da yashi, ga tsananin sanyi; duk sun taru sun fasa mani kafata da fasau.

Baba, na yi yunkurin in nemi na kaina amma matsalar da nike fuskanta ita ce, da na kusanci motocin kan titi ko gefen shataletalen hanya, sai mai mota ya daga gilashin motarsa, ko ka ji ya ce mani “Allah Ya ba da sa’a,” saboda tsana da kyamar da suke yi wa almajiri.

Baba, ba kowa ne ke jinkai da tausayin almajiri ba. Baba, wallahi nakan ji a zuciyata kamar ni kaskantacce ko wani masaki ne. wata rana ma nakan ji kamar ni rayuwata ba ta da wani amfani ga kaina ko ga jama’ata. Wata rana nakan ji a raina cewa, to, ai ni yaro ne amma kuma ba ni da wani tabbacin hakan, domin kunci, kadaici da rashin kula duk sun dusashe mani hasken kuruciyata.

Idan na hango yara irina sun yi dandazo suna wasa a wani fii, nakan so in yi hulda da wasa da su, to amma nakan yi tunanin cewa, ta yaya zan kusance su, alhalin su suna cikin kayan makaranta kuma ga su da kuzari da karsashin wasan, tun da sun sami damar yin karin kumallo mai kyau tun da safe.

Baba, ko wannan sakon takardar ma, daya daga cikin yaran ne na roka, ina gaya masa yana rubuta mani, domi in aiko maku. Baba, zuciyata cike take da burace-burace masu kyau amma ban ga ta yadda zan iya samun cikarsu ba, tun da ba ni da wata dama ko taimakon da zai sada ni da su. Ga shi dai ina cikin jama’a, to amma karancin shekaruna ya kasa bambance mani mutanen kirki da wadanda ba na kirki ba, domin sau da dama sai ka ga mutum ya ja ka a jiki amma ashe yana so ku shaku da shi ne don ya cuta maka.

Baba da Inna, nakan ji takaici da kaicon kawo ni da kuka yi nan wurin da sunan almajiranci. Da ma dai ba ku kawo ni ba! Da ma kun bar ni can a wurinku na rika zuwa makarantar Allon kauyenmu, ina dawowa a gabanku. Saboda yanzu duk wata tarbiyya da horon da kuka yi mani sun fara gushewa daga guna, a dalilin rashin kwaba da kulawar da ba na samu daga gun kowa.

Daga karshe, Baba da Inna, ina rokonku da ku yi kokari ku dawo da ni gida. Duk tsananin talaucinka Baba, abincin gida ya fiye mani dadin ci, domin shi Inna tana miko mani shi ne cikin dadin rai da so da kauna. Baba, tabarmar wundi da nake kwana a kai, ta fiye mani dadin kwanciya a kan daben zauren Malam. Baba, zuwa gona da muke yi tare da kai, ya fiye mani gararanbar yawon zuwa rafi wanka da zuwa neman kwalam da makulashe a kasuwanni da muke yi a ranar da ba karatu. Baba, kullum in kwanta in tashi in gan ku zai fi kara mani shakuwa da kaunar juna, ni da ku, a maimakon nisan da na yi maku kuma ga haushi da takaicinku da nake ta ji, ina ganin kamar kun yada ni ne kawai don ba ku sona.

Baba, ku sani yanzu rayuwata tana cikin tsananin neman kulawar wani mai sonta kuma ina ganin ba wanda ya dace ya nuna mata so, kauna da kulawa sai ku!