Sako na musamman ga al’ummar Fulanin Najeriya

A yau, kima da darajar al’ummar Fulani a Najeriya tana neman dusashewa. Sunansu ya yi kauri a sassa daban-daban na kasar nan, musamman ma a yankin Arewa, inda ake zargin su da munanan ayyuka. Domin ankararwa da kuma domin ceto su daga wannan gurbacewa, IBRAHIM BABANGIDA SURAJO (08163439197) ya dauki alkalami ya aika masu wannan […]

Sako na musamman ga al’ummar Fulanin Najeriya

Matan Fulani

A yau, kima da darajar al’ummar Fulani a Najeriya tana neman dusashewa. Sunansu ya yi kauri a sassa daban-daban na kasar nan, musamman ma a yankin Arewa, inda ake zargin su da munanan ayyuka. Domin ankararwa da kuma domin ceto su daga wannan gurbacewa, IBRAHIM BABANGIDA SURAJO (08163439197) ya dauki alkalami ya aika masu wannan budaddiyar wasika. Da fatan ba Fulani kadai ba, kowa zai yi karatun-ta-natsu, domin gyara abin da ya lalace:

 

Zuwa ga al’umma mai daraja, al’umma mai nasaba, al’umma mai ilmi, al’umma mai jarumta kuma al’umma attajira. Al’ummar Fulani, assalamu alaikum.

Bayan gaisuwa irin ta addinin Musulunci, da farko na kira ku da suna al’umma mai daraja ne saboda a cikinku ne aka samu Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo. Waliyyin Allah wanda ya yi yaki ya jaddada addinin Musulunci a fadin kasarmu da ma wasu yankuna na wasu kasashen makwabta. Wannan kuma aiki ne wanda har duniya ta nade ba za a manta da shi ba. Wanda kuma har ya zuwa yanzu zuriyarsa ce da kuma ta almajiransa suke shugabantar jama’a tare da yi wa Musulunci hidima. Allah ya saka masu da alheri.

Haka kuma na kira ku da al’umma mai nasaba saboda na taba jin wani malami ya kawo wani hadisi, wanda ya ce Annabi Muhammadu (saw) ya fada, cewa “babu wani Annabi wanda bai yi kiwo ba…” Don haka ashe irin yadda rayuwarku take a kan kiwo wannan na iya sa wa a ce kuna da kyakkyawar nasaba. Haka kuma a wani hadisin ya ce “kunya wani yanki ce ta imani.” Ku kuwa kowa ya sani babbar siffar da aka san ku da ita ita ce kunya. Don haka watakila bayan Larabawa da Yahudawa babu wata al’umma da za mu iya cewa ta samu wannan kyakkyawar sifa ta nasaba face Fulani. Bugu da kari kuma tun kafin zuwan Larabawa da Turawa kasashenmu, a lokacin da al’ummar Hausawa da sauran kabilu da al’ummomi suke bautar Dodo da Aradu da Magiro da sauran tsafe-tsafe, ku ba a danganta ku da irin wannan shirka ba.

Na kuma kira ku da al’umma mai ilmi saboda kowa ya san cewa tun ma kafin zuwan Turawa da kuma ilminsu na boko a kasarmu, kakanninku sun iya karatu da rubutu. Haka kuma a wannan zamani kowa ya san a addinance da zamanance ba a bar ku a baya ba wajen yin fice ta fannin ilmi. Wannan kuwa bai rasa nasaba da irin kaifin basirar da Allah Ya sanya a kwakwalwarku. Yanzun haka akwai shehunnan malamai Fulani, wadanda suka yi fice ta bangaren ilmi da basira, wadanda ba za su kidayu ba. Kadan daga cikin misalai shi ne Shehu Dahiru Usman Bauchi  da Malam Kabiru Gombe da sauransu.

Haka kuma a cikinku aka samu shugabannin da suka yi fice wajen gaskiya da rikon amana irin Sa Ahmadu Bello Sardauna da Shugaba Buhari da Ahmadu Ahijjo da Sarkin Kano Sanusi na Daya da kuma wasu da yawa da ba zai yiwu a kawo sunansu ba a yanzu.

Na kuma kira ku da al’umma mai jarumtaka saboda kowa ya yadda ba a magaji da yaro haka ba a raggo jeji. Don haka ko ma ban ce komai ba, duk mutumin da yake rayuwarsa a dokar jeji inda ba ruwa ba wuta ba titi sai kuraye da sauran namun jeji kai ka san ba za ka alakanta shi da tsoro ko kasala ba.

Hujjata ta kiranku al’ummar attajirai ita ce, cewa tun fil azal duk wanda ya ga zabuwa da ma da zanenta ya ganta. Kabilar Fulani ne kadai za ka samu tun yaro yana ciki ba a haife shi ba yana da sa ko saniya ko kuma wata karamar dabba, kai wani lokacin ma yana da matarsa tana jiransa tun kafin a haife shi. Haka kuma abin yake ga ’ya mace. Sannan kuma kiwo na daya daga cikin sana’o’in da ake gada kamar su kira da jima da saka da sassaka da sauransu.

Haka kuma tun shekaru aru-aru ku ne kuke ciyar da kasarmu da nama, walau na shanu ko kuma na kananan dabbobi kuma har yau ba a kure ku ba. Ku ke wadatar da kowa da kowa da nono da kuma man shanu, a sha fura kuma a ci tuwo har ana santi. Ku ke bai wa dubbai masu sana’ar fawa aikin yi haka kuma kamfanoni masu sarrafa kashi da kuma masu sarrafa fatar dabbobi.

Duk wadannan bayanai da na yi shimfida da su, ina yi ne don in tuna maku irin baiwa da daukakar da Allah Ya ba ku da kuma irin yadda tarihi yake kallon ku a idon duniya. Don haka dai ina son kara fada maku cewa shi fa mutunci madara ne.

To sai dai kuma kash, wai ga wani abu nan a bisa kan matar sarki kuma da tana da ido da ta gani! Ga kakanni da iyaye sun yi gini a kan turba ta kwarai amma ga matasa a yanzu sun yi dimuwa sun shiga jeji suna faman barna har abin ya wuce min sharrin. To amma dai da yake ’yan zance sun ce wai rashin kira ne ya sanya karen bebe ya bata. To lokaci ya yi da manya da dattawa wadanda su ba su riga sun bebance ba, su fara kwala kira da karfi tun kafin matafiyan su yi nisan da ba za su taba jin kiran ba ko da an yi. Domin kuwa idan haka ta faru hakan na iya zama wata barazana da kuke yi da kanku ta kokarin shafe wannan al’umma daga doron kasa.

Na san akwai korafe-korafe da kuke da su da dama, musamman ga irin yadda abokan zaman ku ta kowane bangare na kasar nan suka sanya ku a gaba. Kama daga yadda manoma suka cinye burtaloli da kuma wawure dazuka suka hana ku samun hanyoyin wucewa da kuma wuraren kiwo. Kuma a hakan idan bisa ganganci ko kuskure dabbobinku suka taba masu amfanin gona, to kuwa ko ku ji a jikinku ko kuma a aljihunku, kai wani sa’in ma duka biyun. A irin wannan hali akan yi maku taron dangi, wanda kuma karshe dai labarin ba kyau.

Kai idan lamarin ma ya kai ga kotu, ko gaban alkali ko kuwa a gaban ’yan sanda ake yi maku tara ta garari tare da musgunawa da kuma dauri; duk a kan ba ku da mai tsaya maku.

Haka kuma ina sane da yadda kadda ke yin amfani da kudi da abin duniya wajen yaudarar matayenku, su dinga nemansu. Kuma ban manta ba da yadda dillalai suke ta damfarar ku ta yadda za ku kiwata dabba shekara da shekaru amma rana daya idan kun kawota kasuwa ku yi kashe-mu-raba da su.

Duba da yadda aka mayar da ku gajerar kuka mai dadin hawa shi ya sanya tun lokacin da mulkin dimokuradiyya ya dawo a nan kasar, duk wata al’umma ko kabila da take gani karfinta ya zo kuma ta kai bantenta to kuwa a kan ku da dabbobinku za ta yi gwajin makaman da ta saya domin kare kanta.

Za mu ci gaba