Sako na musamman ga al’ummar Fulanin Najeriya (2)
A yau, kima da darajar al’ummar Fulani a Najeriya tana neman dusashewa. Sunansu ya yi kauri a sassa daban-daban na kasar nan, musamman ma a yankin Arewa, inda ake zargin su da munanan ayyuka. Domin ankararwa da kuma domin ceto su daga wannan gurbacewa, IBRAHIM BABANGIDA SURAJO (08163439197) ya dauki alkalami ya aika masu wannan […]
A yau, kima da darajar al’ummar Fulani a Najeriya tana neman dusashewa. Sunansu ya yi kauri a sassa daban-daban na kasar nan, musamman ma a yankin Arewa, inda ake zargin su da munanan ayyuka. Domin ankararwa da kuma domin ceto su daga wannan gurbacewa, IBRAHIM BABANGIDA SURAJO (08163439197) ya dauki alkalami ya aika masu wannan budaddiyar wasika, inda muka kawo kashi na daya a makon jiya, yanzu kuma ga karashen kashi na biyu. Da fatan ba Fulani kadai ba, kowa zai yi karatun-ta-natsu, domin gyara abin da ya lalace:
Na san kuma jami’an tsaro da ’yan banga sun rika cutar da ku a kan laifin da ba naku ba. Wani lokaci ma sukan kashe wasunku ba tare da kai su gaban kotu ba, don a tuhume su da laifukan da ake zargin su.
Haka kuma ’yan siyasa da suka gan ku a hargitse sai wasu bata garinsu wadanda suka san cewa dokin mai baki ya fi gudu da gangan suka dauki sunanku kacokan suka yi masa fenti baki kirin, ta yadda da zaran an aikata wata aika-aika sai a ce ku ne.
Ga uwa-uba kuma yadda gwmnati ta yi biris da duk wani lamari da ya shafi al’ummarku ta Fulani, walau na ci gabanku ko kuwa na hakkinku. An bar ku ba ilmi, ba ruwan dam, ba na burtsatse, ba wurin shan maganinku ballantana kuma na dabbobinku, ba kasuwa ba kasuwanci, da dai sauransu.
Na san cewa tura ce ta kai bango, shi ya sanya ku ma kuka sake dabara, inda da farko kuka fara sayen ’yan makamai na kare kai. To sai dai kuma fa matasan wannan al’umma sun zarce iyaka, yanzu ba ma batu ake yi na ramuwar gayya ba, a’a, abin ya wuce nan domin kuwa mummunar dabi’a ce suka dauko wacce kaf a tarihin kasar nan ba a taba samun al’umma da ta taru ta fada rudu da dimuwa ba kamar ku.
Ta yaya za a ce matasanku wadanda su ne kashin bayan al’ummarku sun rungumi fashi da makami da kuma garkuwa da mutane su zama sana’a?
Ina kuma matukar mamakin yadda kuna Musulmi kuma wadanda ake dangantawa da kabilar Shehu har a cikin jin dadi da isa kuke daukar bindiga kuna yin kisan gilla ga ’yan uwanku Musulmi da kuma makwabtanku kuma abokaninku Hausawa. Kuna kashe mutane manya da kanana irin kisan da ko dabba bai dace ku yi mata haka ba a matsayinku na Musulmi.
Shin kun yanke kauna ne daga rayuwarku da ta zuriyarku mai zuwa ne? Shin ba ku san cewa idan hankali ya bace hankali ne ke nemo shi ba? Shin za ku yi amanna da ingiza mai kantu ruwan da wasu makiyanku ke yi maku ne na cewa ku ba ku da yafiya? Gami da na san kun san cewa duk mutumin da ba ya yafiya to kuwa ba shi da imani.
Shin ina dattawan al’ummar Fulanin suke, ko kum bar jagorancin rayuwarku da ta zuriyarku wajen wasu matasa wadanda Shaidan ya sa wa mari a wuya ne? Ina kuma kungiyoyin Fulani irin su Miyetti Allah, shin sai wajen fidda ’yan takarar Shugaban Kasa ne kawai ake jin su ko kuwa?
Kamata ya yi a ce wannan kungiyoyi sun fitar da wani kwamiti wanda zai shiga tsakanin tsagerun matasan Fulanin da gwamnati da kuma sauran jama’ar gari. Ya zamanto sun su hada kai da sauran ardo-ardo, su kai gwauro su kai mari daga wajen hukuma zuwa cikin dazukan da matasan suka yi sansani don a samu a warware wannan matsala.
Hausawa na cewa hannunka ba ya rubewa ka tsinke shi ka yar. Ya kamata shugabannin Fulani, musamman mazauna yankunan Katsina da Zamfara da Sakkwato da Kaduna da Binuwai da Filato da Neja da da Abuja da kuma Kogi su kalli wannan lamari da idon basira, su hada taro a tsakaninsu; ta yadda za su tsawata wa ’ya’yansu da kannensu domin su kauce wa yunkurinsu na kare kansu da kansu. Wanda ya yi taurin kai ya ki ji su da kansu sai su dauki mataki a kansa. Wannnan haka yake domin kuwa duk wanda ya daura niyyar fada da hukuma ai ba zai yi nasara ba kuma bai kama hanya mai bulewa ba, domin duk irin yadda suke ganin sun yi tanadi sun shirya, to ita ta ninka su shirin sau dari da goma.
Ya kamata kangararrun matasan Fulani su sani, rayukan da suke halakawa na mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kauyukan Zamfara da Katsina da sauran wasu sassa, idan suna yi ne don bata wa gwamnati suna ko bata mata rai, to da farko dai su sani dan uwansu ne ke Shugaban Kasa. Ko suna so ko ba su so, in ya yi da kyau za a fadi cewa wannan Bafillatanin ya yi kokari. Haka ma idan ya yi akasin haka. Sannan kuma abu mafi girma shi ne su sani wadannan rayuka dai na Allah ne kuma Yana son su kuma Ya yi hani da zubar da jini. Ba abin da ya fi dadi irin zama lafiya, domin kuwa ko kudaden baragurbin matasan na Fulani masu fashi da kuma yin garkuwa da mutane suke karba a hannun mutane ai ba za su ji dadinsu ba matukar suna a boye a daji.
In kuwa gaskiya ne cewa abokanin adawar siyasa ne suke amfani da su don kawo wa gwamnati cikas, to kuwa sun yi abin kunya sannan kuma an kai su an baro. Haka kuma in akwai kanshin gaskiya cikin zargin da ake yi wa wasu jiga-jigan ’yan siyasa wajen daukar nauyin wadannan ayyuka na ta’addanci don kawai su saci kudin al’umma kuma su saci ma’adanai to nan ma an sake dabawa, domin kuwa kura ce da shan duka gardi kuwa yana kwashe kudin.
Matasan Fulani musamman kangararru, ku sani ci gaba ba ya samuwa sai da zaman lafiya. Shin ba ku fatan ku ma ku hayayyafa ku yadu cikin zaman lafiya da walwala? Ko kuwa wane irin tarihi kuke so ku kafa wa ’ya’ya da jikokinku? Kuma ma shekara nawa za ku yi kuna boyo a cikin dajin kuna wannan aika-aika?
Daga karshe ina fatan za ku dauki shawara ku dawo a yi tafiya tare kamar yadda aka saba a baya cikin mutunta juna da son juna da kuma hulda ta arziki don ku fitar da kawunanku daga matsi da takura da zaman dar-dar na gaba kura baya sayaki. Da fatan Allah Ya karyo da zukatanku albarkacin wannan wata mai alfarma na Ramadan.