Sako na musamman ga kungiyar Gwamnonin Arewa

Wannan budaddiyar wasika, na yi nufin aika ta ne a matsayin tuni, zuwa ga Gwamnonin Arewa, ta hannun shugabanta, Dokta Mu’azu Babangida Aliyu, CON, Gwamnan Jihar Neja.Kafin ku hadu da Allah:A shekarar da ta gabata, na rubuta muku irin wannan budaddiyar wasika, don haka a wannan karon, tuni ne nake kara yi muku. Dalilai biyu […]

Sako na musamman ga kungiyar Gwamnonin Arewa
Sako na musamman ga kungiyar Gwamnonin Arewa

Wannan budaddiyar wasika, na yi nufin aika ta ne a matsayin tuni, zuwa ga Gwamnonin Arewa, ta hannun shugabanta, Dokta Mu’azu Babangida Aliyu, CON, Gwamnan Jihar Neja.
Kafin ku hadu da Allah:
A shekarar da ta gabata, na rubuta muku irin wannan budaddiyar wasika, don haka a wannan karon, tuni ne nake kara yi muku. Dalilai biyu ne suka sanya na ga cewa ya kamata in kara yi muku tuni, game da sakona na baya. Na farko dai na san cewa kwana 365 sun ishi mutum ya iya yin tariya da nazarin waccan wasika da na rubuto, wadda a cikinta na bijiro da irin matsalolin rayuwa da na tattalin arzikin kasa da suka addabi Arewacin Najeriya. Nazarin dai zai sanya a gano cewa shin wadannan matsaloli sun kau ne ko kuwa sun ragu ko kuna suna nan yadda suke? Na biyu kuma, makonnin da suka gabata, sun kasance lokutan da aka yi yayin rubuce-rubucen wasiku ne tsakanin tsofaffin shugabani da masu ci a yanzu da kuma ma’aikatan gwamnati. Shi ne nake ganin cewa kafin a ce wata wasikar ta kara fitowa daga hannun manya, bari in aika wa gwamnonin na Arewa da wannan ’yar tunatarwa.
Kamar waccan, ba na dakon amsa daga daya daga cikinku, domin kuwa sakon da ke cikinta, ba zai yi wa kowannenku dadi ba, domin kuwa ba kirari ne nake muku ba. Dukkanku, har ma da Limamin Kwankwasiyya, wanda ga alama yana dan kamanta ayyukan raya al’umma fiye da ku da kuka zama jidali ga dukiyar jihohinku.
Ya ku masu girma, idan ma na ce zan buga muku tamburan yabo, musamman idan muka yi la’akari da matsalolin rayuwa da na tattalin arziki da suka addabi jihohinku, ai kamar na amince ne da gazawar ku ke nan. Ba ku nuna da’a da misali a aikace, ga halin ko’in kula da kuke nunawa da al’amuran jama’ar yankin Arewa. Wadannnan munanan halaye, su ne suka taimaka wajen durkusar da Arewa, suka sanya ta cikin mugun yanayin lalacewa da tabarbarewa.
A gaskiya ya ku masu girma gwamnoni, duk irin matsalolin da na zayyana suna addabar yankin Arewa, a waccan wasikar tawa ta bara, suna nan ba su tafi ko’ina ba. Hasali ma, sun kara kazancewa ne. Idan da za ku tuna baya, a wasikar tawa, na bayyana muku yadda muggan gwamnonin da kuka gada suka lalata yankin, suka durkusar da shi kasa, ta hanyar mulkin ballagaza da suka gudanar. A lokacinsu ne suka lalata harkar noma, suka lalata masakun da ke yankin, suka lalata al’amuran ilmin da aka san yankin da shi tun can dauri, suka cefanar da duk wani abu mai tasiri da yankin ke tokabo da shi. Ga shi yanzu babu abin da ya yi saura a yankin Arewa, daga talauci sai kamfar aikin yi da ke gallabar al’umma gaba daya.
A halin yanzu, idan mutum ya ziyarci unguwannin da kamfanoni suke a manyan biranen Arewa, sai takaici ya kama shi, domin kuwa sun koma kamar makabarta. Yanzu babu abin da za ka gani sai kamfanonin buga bulo, sai kuwa na buga ruwan leda, sai kuwa dinbin almajirai suna bara. Babu abin da yankin Arewa ya kware a yanzu sai kyankyashe badukai da masu gadi da yaran gida da ’yan tura baro da yaran mota da ’yan acaba, suna cika biranen Kudancin Najeriya. Ga shi kuma yanzu wata masifar ta karu a yankin, inda shaye-shayen muggan kwayoyi ya zama ruwan dare ga matasa.
A sanadiyar muggan kwayoyi, muggan laifuffuka sai hauhawa suke a yankin Arewa. Wadannan kuwa sun hada da fashi da makami, fyade, sace mutane don garkuwa da su da sauransu. A can baya, wadannan muggan al’amura, sai dai a ji labarin faruwarsu a wasu yankunan. Ya ku masu gurma, wadannan munanan al’amura da ke faruwa a Arewa, ya kamata a ce suna damun ku, idan dai har kuna da kishin al’umma a zukatanku.
A bara kamar yau, wani daga cikinku ya yi kididdigar cewa zai kashe biliyan masu yawa a kasafin kudin jiharsa. Ga shi yanzu bayan watanni 12 da yin haka amma babu wani aikin ku-zo-ku-gani da ya aiwatar, wanda ya yi ko kusa da wadannan makudan kudi da ya kasafta kuma ya kashe. Ku dukan ku, a Arewa kaf, babu inda za ka duba, ka ga wani aikin ci gaban da zai nuna maka cewa ya yi daidai da makudan kudaden da ake jibgo muku daga asusun Gwamnatin Tarayya.
Kamar yadda na fada a waccan wasikar ta bara, aikin da dukkanku 19 kuka yi a yau, idan aka hada shi wuri guda, bai kai kima da darajar aikin da marigayi Sardaunan Ahmadu Bello ya aiwatar ba, a lokacin da yake Firimiyan Jihar Arewa. Ba dukiya ce kawai ta sanya ya yi nasara ba, domin kuwa babu ita ma kamar yadda take a yau. Babban abin da ya sanya ya yi nasara shi ne, kishin al’umma, gaskiya da rikon amana da kuma iya ririta albarkar da Allah Ya hore wa yankin wajen yi wa al’umma aiki.
Babban abin da nake tunatar da ku, ya ku masu girma gwamnonin Arewa, shi ne ku sani cewa akwai ranar sakamako na nan zuwa tana jiran mu duka. Allah Ka yi mana jagora zuwa ga aiki nakwarai, amin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos