Sako na musamman ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Ya mai martaba Sarki, ina fata kana lafiya tare da iyalinka da fadawanka masu kima. Yaya aka ji da al’amuran mulki da hidimar al’umma? Da fatan Allah Ya kara yi maka jagora, Ya ci gaba da haskaka maka al’amuranka, ta yadda za ka ci gaba da jagorar al’umma bisa fa’ida da nasara, amin. Bayan haka, […]
Ya mai martaba Sarki, ina fata kana lafiya tare da iyalinka da fadawanka masu kima. Yaya aka ji da al’amuran mulki da hidimar al’umma? Da fatan Allah Ya kara yi maka jagora, Ya ci gaba da haskaka maka al’amuranka, ta yadda za ka ci gaba da jagorar al’umma bisa fa’ida da nasara, amin.
Bayan haka, na zabi in rubuto maka wannan sakon ne ta wannan hanya, musamman ganin cewa ita kadai ce hanyar da Allah Ya huwace mani, wacce zan iya isa zuwa gare ka da dinbin al’ummarka cikin sauki da sawaba.
Ya mai martaba, tun daga ranar da aka sanar da cewa kai Malam Muhammadu Sanusi II ne ka gaji marigayi Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano, na samu natsuwa da kwanciyar hankali, musamman ganin cewa martabar sarautar gargajiya za ta farfado, kasancewar ka kasance muzakkari ne ta fannoni da dama. Kai mutum ne haziki, zakakuri, mai ilimin addinin Musulunci da kuma na zamani. Kai mutum ne mai akida da ra’ayi na kashin kanka. Mutum ne kai wanda ba ka raini kuma ba ka yarda da raini ba.
Na dade da sanin nagartarka da kishin al’ummarka da kiyaye addininka. Ba zan mance da irin yadda ka yi ta gwagwarmaya ba a can baya, inda ka sadaukar da lokacinka wajen yin rubuce-rubucen wayar da kan al’umma. Kacokan jaridar Weekly Trust ta ba ka shafi na musamman, inda a duk mako kake rubuce-rubuce babu gajiyawa. Wannan kokari naka ya taimaka sosai wajen sassaita tunanin al’umma da yi masu jagora.
Ba zan mance ba, akwai lokacin da wasu gafalallu suka taso ka gaba, suna cewa wai kana hada gudu da susar katare, ma’ana kana hada aikin banki da jaridanci. Kai kuwa babu abin da ya shalle ka, ka yi kunnen uwar shegu da su, ka ci gaba da fadakarwarka ba tare da shayin kowa ba. Hakan kuwa ya ci gaba da yin tasiri, domin dai gaskiya ka tsaya wa, kuma masu iya magana sun ce, ciki da gaskiya, wuka ba ta huda shi. Shi ya sanya kaifi da dafin wukar makwangwara bat a yi tasiri a kanka ba.
A lokacin da Allah Ya ba ka dama ka zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ka yi aiki wurjanjan wajen ganin al’amuran kudi da kasuwanci sun daidaita wajen bunkasa al’umma. Ka hana zaluncin da bankuna suka rika yi wa al’umma, inda suka rika zabtare wa mutane Naira dari daya ga duk kudin da suka cira da katin ATM. Ka jajirce wajen dakile wasu azzaluman shugabannin bankuna da suka kware wajen satar dukiyar al’umma. Ka tsaya tsayin-daka har sai da aka kafa bankin Musulunci, wanda ya tsayu bisa adalci ga al’umma. Ka tsaya wajen fada wa Shugaban kasa gaskiya, inda ka bankado yadda ake sace dukiyar al’umma a kamfanin mai na kasa (NNPC). Irin wadannan jajirtattun ayyuka, su ne alkiblarka kuma kansu ka tsaya har ka samu nasara, ka zama abin misali ga kowa.
A makon jiya, ka ba da wata sanarwa, wacce ba kasafai sarakunanmu ke ba da irinta ba. Ya mai martaba Sarki, ka mayar da martani ne ga abin takaicin da ke faruwa a Arewa, inda ’yan Boko Haram ke kashe al’umma suna yankan kauna yadda suka ga dama, a yayin da jami’an tsaron gwamnati suka gaza tabuka komai. Ka yi kira ga al’umma, musamman ’yan tauri, maharba da sauran jarumai da suka girku da tsimi da su mike tsaye su kare al’umma da baiwar da Allah Ya ba su.
Wannan namijin kokari da ka yi, abin yabo ne kuma ka yi sara a kan gaba. Sai dai duk da haka, ina ganin da sauran aiki; domin kuwa ina ganin cew bai kamata mai martaba sarki ya tsaya a nan kawai ba, ya kamata ka ci gaba da wannan aiki kamar haka:
Ya dace ka hada kai da Sarkin Musulmi da Shehun Borno da Lamidon Adamawa da Sarkin Fika da ma sauran sarakunan Arewa da kake ganin za su ba ku goyon baya, ku zauna ku tattauna yadda za ku rika ba talakawanku karsashi da kwarin gwiwa, yadda za a tunkari wannan matsala ta Boko Haram. Ku tuna cewa Mujaddadi Shehu Usman danfodiyo ya bar muku gadon gaskiya da jaruntaka.
Ya dace Sarki ya hada kai da kungiyar ACF da sauran kungiyoyin kare muradun Arewa, domin ku nemo hanyoyin da za a karfafa dakarun gargajiya na Arewa da za su ci gaba da fafatawa da Boko Haram har su samu nasara.
Ya dace mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya hada kai da malaman addinin Musulunci da na Kirista da ke Arewa domin tattaunawa da daukar matakan kare al’ummar Arewa daga wannan balahira ta Boko Haram.
Ya dace Sarkin ya hada kai da gwamnonin Arewa, musamman wadanda yankunansu ke cikin wannan bala’i, domin ganin yadda za a kare yankin da jama’arsa.
Ya dace Sarkin kuma ya ci gaba da magana irin wannan ba kaukautawa, sannan ya ci gaba da jan ragamar kishin talakawa da raunana, ba tare da shayin kowa ba. Mun san babu abin da yake tsoro kuma babu abin da zai yi masa cikas in sha Allah!
Muna bayanka mai martaba Sarkin Kano Muhammmadu Sanusi II! Muna yi maka fatan alheri!! Muna yi maka addu’ar Allah Ya kare ka!!!