Sako na musamman ga talakan Najeriya

Dan talaka a kasar nan ba ya da makoma abin dogaro a rayuwarsa.

Sako na musamman ga talakan Najeriya

Najeriya

Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Malama A’isha Usman Liman, ta bijiro da wani zazzafan tsokaci, domin haskaka wa al’ummar Najeriya, musamman talakawa hanya, domin su gane ciwon da ke cin su, domin su gane matsalolin da suka yi masu cacukwi, suka hana su ci gaba, sannan kuma ta bayyana masu hanyoyi da matakan da suka kamata su dauka domin canza wa kansu makoma.

Ta dai bayyana a fili cewa dan talaka a kasar nan ba ya da makoma abin dogaro a rayuwarsa.

Manya da shuwagabannimu sun daura yaki da matasa a kaikaice amma sai mai hankali da lura ke ganewa. Sun tattara dukkan wani ci gaba na rayuwarmu sun mallaka wa kansu da ’ya’yansu.

Misali a nan, mu mu sha ruwan rafi, su su sha na kwalba. Su kunna janareto su ga haske, mu kuma mu kunna a-ci-balbal.

Su su je asibitocin kasashen waje masu tsada, mu kuma muna cikin kasa ciwo yana kashe mu, ba magani ba kayan aiki a asibitocinmu.

Su fita da yaransu kasashen waje su yi karatu mai inganci, mu kuma yaranmu makarantunsu ba kujeru ba kayan aiki.

Motocinsu sababbi, masu shanye dukkan gargadar sukuwar ramun titunan kasar nan, mu kuwa motocinmu duk daga bololin wasu kasashe suke, sun ci duniyarsu sun gaji.

Wani abin lura kuma shi ne, a lokacin da suke matasa kamar mu, ba haka shuwagabannin wancan lokacin suka gudanar da mulkin kasarmu ba.

Su a lokacin kuruciyarsu, da talaka da mai arziki da sarki da bawa duk a makaranta daya yaransu suka yi karatu, asibiti daya suka sha magani, kasuwa daya suka ci. Kai duk dai komi daya ne, ba bambanci.

A lokacin ba cin hanci da rashawa, ba kamar yanzu da aka maida shi wayau ba.

Ba tashe-tashen hankali da ya shafi addini ko na kabilanci, kowa yana girmama abokin zamansa.

Ba kirkirarrun cututtuka, ba jari-hujja, ba kamar yanzu da aka maida kudi madugu ba. A lokacin na baya, ba rashin tarbiya, ba kamar yanzu da aka maida ita abun ado ba. Ba kama-karya, ba kamar yanzu da aka maida ita isa ba.

Mu dai shuwagabanninmu na yanzu ba su da wani hali abin koyi a wurinmu, ba wata akida abin riko daga wurinsu, ba wani tarihi abin tunawa daga wurinsu.

Lallai ya kamata mu duba mu gani, mu san cewa yanzu matashi dan talaka baya da wata gata a wurin kowa, ba wani shugaba ko mai arziki da ya damu da me yake ciki ballantana makomarsa.

An bar shi da talauci da jahilci. Gaskiya matasa ya kamata mu farga, mu hankalta da halin da zamaninmu yake ciki ayanzu.

Mu tashi tsaye mu ceto makomarmu daga halin duhun da take ciki, domin ba wani haske da ke haska rayuwarmu da makomarmu a halin yanzu.

In kuwa har ba mu tsaya tsayin-daka ba, to za mu gama yi musu bauta ne a kuruciyarmu kuma mu koma bayin ’ya’yansu a tsufanmu.

Domin burinsu da tsarin manufarsu shi ne su gadar wa ’ya’yansu bautar da mu da suke yi a halin yanzu. Shi ya sa suka samar da babban gibi a tsakaninmu da yaransu, suna karatu mai kwari a kasashen waje, su dawo su karbi ragamar shugabancinmu; tunda iliminsu ya fi namu.

A karbi takardunsu ta ofis da ofis, mu kuma a bar mu a layin neman aiki, har muna kashe junanmu a sanadiyyar turmutsitsi.

Sai idan guguwar siyasa ta kada a neme mu, a ba mu wiwi da shalisho da adda da gariyo, mu yi musu bangar siyasa. Wai a lokacin ne aka san inda muke da kuma amfaninmu.

Mu kuma don sakarci sai mu ce ga mu. Mu yi ta ta’addaci da shashanci a banza, ana ba mu kudi kalilan muna kashe makomarmu da kanmu, alhalin da mai sa mu yi masa da wanda aka sa mu yi wa bangar, duk manufarsu daya ce a kanmu, domin in wannan ya sa wannan kungiyar matasa su yi masa banga, shi kuma wancan ya sa waccan kungiya ta yi masa.

Sai ka ga ’yan unguwa daya an gwara kansu suna ta aibanta junansu da kansu. Su kuma da ake yi wa bangar, da su da yaransu na can suna hango hasken rayuwarsu.

To, ta yaya za mu haska fitila ga wannan zamanin namu da rayuwarmu ta gaba?

Ta yaya mu ma za mu sama wa kanmu gata da kwanciyar hankali kamar irin wanda suka sama wa yaransu?

Wannan hanya mikakkiya ce, mai saukin bi kuma muna cikin lokaci mafi dacewa da za a iya kawo canji mai ma’ana.

Ba ga guguwar siyasa ta fara kadawa ba? To mu kuma sai mu dauka guguwar kawo canji ce ta fara motsawa. Ta yaya?

Ta canza al’amuran siyasarmu, ta yadda za ta fi yi mana amfani kuma ta yi daidai da mu.

A maimakon a ce dan takara kowane iri, (mai kyau ko marar kyau) ya yi zubur ya tashi, ya bullo mana, ya ce mu goya masa baya, wancan ma ya tashi ya ce zai kara da wancan, mu ya kamata mu mike neman mutanen kirki kwarara, mu roke su su zo mu zabe su, su shugabance mu.

Tun da mu muke son su, don haka muna iya tara kudi mu yi musu rajistar kungiya, mu saya musu takardar takara, mu rarraba su cikin jam’iyyu, mu tallata su a mazabunmu.

Ga mutanenmu, in dai kowa ya cire son kai, ya yarda da gaskiya cikin zabo su, za mu ga ba sai mun sha wahalar rabon shinkafa ko sabulai ba.

Iyakar mu yin hoton fosta, shi ma don sauran jama’ar mazabu su san cewa su ne muka fitar kuma za mu ga kowa na sanya albarka, domin an san cewa mutanen kirki ne muka tsayar.

Kun ga mun huta da gangamin watsa karairayi da ’yan siyasa ke yi mana a kan durom in sun zo kamfen.

Mun huta da watsa mana tsaba da ake yi kamar kaji. Mun huta da wani ya saye mu mu yi masa bangar banza, ta sakarci, idan ya ci kujerar ya manta da mu.

Tun da mu muka zabo su da kanmu kuma mun san mutanen kirki ne, mun huta da aringizon kuri’u da ake yi wa wani dan lelen siyasa, tun da za mu kasa mu tsare wa kammu.

Mun huta da shakkun da muke samu idan an gama zabe, tun da duka ’yan takarar tatattu ne; mun tantance abinmu da kanmu, ba abin da ya rage illa duk wanda Allah Ya ba cikinsu mu yi masa addu’a da fatan alheri, mu kuma ba shi shawarwari masu kyau a gare shi.

Sai mu koma gefe muna kallonsa yana yi mana ayyukan ci gaba kala-kala.

Kuma mu sa ido sosai ga kai da kawon su, kar mu yarda da duk abin da zai yi ba bisa tsari ba kuma kar mu yarda wasu masu fada a ji su hana shi rawar gaban hantsi don ra’ayi irin nasu. Mu ma kuma kar mu hana shi sakat, don muna ganin mu muka kawo shi kujerar.

In kuwa muka samu nasarar kawo irin wannan canji, to kuwa ba karamin gata muka yi wa kanmu ba, domin mun sa wa kanmu shugaban da muke so kuma mai adalci.

Mun huta da “ku zabe ni” sai dai “mun zabe ka.” Muna iya yin wannan tsarin tun daga mataki na Kansila har zuwa na Gwamna.

Na Shugaban Kasa kuwa idonmu na kan kuri’unmu har a gama kirgawa, muna wurin ba tsoro, ba rigima.

Ni ina ganin kamar mu talakawan kasar nan ba mu da wata matsala illa ta rashin sa’ar shuwagabannin kirki da muka yi kuma da mun tashi tsaye muka kawar da ita, to mun huta da dukkan muzancin da muke ciki kuma mun samu cikakken ’yanci.

To, wai ma me zai hana mu tashi tsayen tun da wuri?

Idan da za a duba yawan mutanen kasar nan, aka ware masu rike da mukamai na siyasa da shuwagabanni, in sha Allahu ba za su fi kashi biyar bisa dari ba, duk sauran talakawa ne amma kuma sun hana mu gaba sai dai kullum muna baya.

A karshe, ya kai talakan kasata, ya kamata ka yi nazarin tsokacin nan, ka yi wa kanka kiyamul laili domin ka huta da wulakanci.

Allah Ya ba mu sa’a, amin!

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara