Sako zuwa ga Manjo Hamza Al-Mustapha (1)
Huduba ta Farko:Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya wajabta ’yan uwantaka da kauna da soyayya a tsakanin Musulmi.Ya fada a cikin LittafinSa Mai girma: “Abin sani kawai, muminai ’yan uwan juna ne……” (Al-Hujurat:10).Kuma ina shaidawa lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Kuma ina […]
Huduba ta Farko:
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya wajabta ’yan uwantaka da kauna da soyayya a tsakanin Musulmi.
Ya fada a cikin LittafinSa Mai girma: “Abin sani kawai, muminai ’yan uwan juna ne……” (Al-Hujurat:10).
Kuma ina shaidawa lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Ya sauke nauyin amanar da Allah Ya dora masa, kuma ya isar da sakon Allah. Ya yi nasiha zuwa ga al’umma, kuma ya yi gwagwarmaya a tafarkin Allah, gaskiyar gwagwarmaya. Ya bar wannan al’umma a kan tafarki madaidaici, fari sal. Darensa kamar ranarsa yake. Ba wanda zai karkace daga gare shi sai halakakke. Allah (SWT) Ya yi dadin tsira da aminci a gare shi da dukkanin iyalansa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! A yau maudu’in hudubarmu zai kasance sako ne zuwa ga dan uwanmu a Musulunci wato Manjo Hamza Al-Mustapha tsohon shugaban dogaran marigayi Janar sani Abacha (Allah Ya jikansa da rahama, amin). Wanda Allah (SWT) cikin rahamarSa da tausayinSa Ya kubutar da shi, bayan ya shafe shekara 14 a tsare, sanadiyyar addu’o’in bayin Allah ’yan Najeriya.
Ya kai dan uwa mai daraja Manjo Hamza Al-Mustapha! Kwanakin baya wata jarida daga cikin jaridunmu na Hausa masu albarka da ke Arewa ta yi hira da kai inda kake cewa kai babu ruwanka, kuma ba ka damu da dukkan zarge-zargen da ake yi maka ba. Sannan kwanan nan, sashin Hausa na Muryar Amurka (bOA) ya yi hira da kai, inda a cikin hirar kake karyata zarge-zargen da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi. Wannan hira da bOA suka yi da kai, kafafen watsa labarai na yanar gizo irin su Premium Times da jaridu irin su Daily Trust duk sun ruwaito mana ita. Sannan na saurari hirar da kunnena. Manjo Hamza Al-Mustapha, ka sani duk zarge-zargen da ake yi maka wallahi kada ka zargi kowa face kanka. Wannan ba don komai ba, sai saboda wasu dalilai.
A Musulunci, haramun ne mutum ya rika munanta zato ga dan uwansa, ko ya rika zarginsa da wasu laifuffuka haka kawai ba wani dalili. Amma idan wasu take-take suka bayyana daga bangaren mutum, to ko a Musulunci ba laifi ne ba don an tuhume shi. Illa kawai bayan an tuhumce shi, sai gaskiyarsa ta kubutar da shi a gaban shari’a. Allah (SWT) Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato, lallai sashin zato laifi ne…” (Al-Hujarat:12).
Kuma Hadisi ya tabbata daga Abu Huraira ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ina yi muku kashedi game da zato, domin lallai zato shi ne mafi karyar labari, kada ku yi bin diddigi ga juna, kada ku yi wa juna leken asiri, kada ku yi wa juna hasada, kada ku juya wa juna baya, kada ku yi kyashin juna, ku zamo bayin Allah ’yan uwan juna” Bukhari: 6,064 da Muslim: 2,563.
Ya ku ’yan uwa Musulmi! Wadannan nassosi suna karantar da mu hani a kan munanta zato ga dan uwa Musulmi. Amma duk da wannan, Manjo Hamza, dalilan da suka jawo a zarge ka suna da yawa, amma ga kadan daga ciki:
Ranar 21 ga Yulin shekarar 2013 kafar yada labarai ta yanar gizo ta Sahara Reporters ta buga wani labari cewa Fasto T.B. Joshua da ke Jihar Legas bokan Goodluck Jonathan ne, yana yi masa duba a yawancin al’amuransa. Kuma a cikin rahoton aka ce Jonathan ya yi imani sosai da T.B. Joshua, wanda ko kara ya gicciya masa ba zai tsallaka ba. An ce shi ne ya yi wa Jonathan duba cewa idan yana son cin zabe a shekarar 2015 sai ya saki Hamza Al-Mustapha. Kasancewar a kan maganar 2015, Jonathan komai yana iyayi, shi ne sai ya saki Al-Mustapha. Daga kudaaen da aka kashe har zuwa alkalan da suka yi aiki a kan aiwatar da umarnin Shugaba Jonathan na sakin Al-Mustapha duk wannan labari ya ruwaito. To, mu ’yan Najeriya mun kasa kunne mu ji fadar Shugban kasa, ko shi Hamza Al-Mustapha ko wani na hannun damarsa ko Fasto T.B. Joshua sun karyata wannan zargi, amma ba su yi ba. Bayan haka, babban abin da ya kara tsorata ’yan Najeriya shi ne; kwatsam daga fitowar Al-Mustapha, Fasto T.B. Joshua na daga cikin mutanen farko da ya ziyarta ya yi wa godiya. Ka ga a nan me ’yan Najeriya za su ce? Za su ce ashe wannan rahoto na Sahara Repoters gaskiya ne ke nan?
Yaku ’yan uwa Musulmi! Bayan wannan, Sahara Reporters din ta sake buga wani rahoto cewa, Hamza Al-Mustapha ya rubuta wa Goodluck Jonathan wasikar godiya a kan sakinsa da ya sa aka yi. Fadar Shugaban kasa ko Hamza Al-Mustapha babu wanda ya karyata wannan zance, ko su yi karar Sahara Reporters.
Bayan wannan, ranar 26, ga Yulin shekarar 2013 kafar sadarwa ta Premium Times ta ruwaito ziyarar da tsohon Ministan Ilimi a gwamnatin marigayi Abacha kuma dan takarar Shugaban kasa a karkashin rusasshiyarJami’iyyar ANPP a zaben shekarar 2011, kuma shugaban kungiyar Dattawa da Matasan Arewa (Northern Elders and Youths Forum), kuma mamba a kwamitin da Shugaba Jonathan ya kafa a kan taron kasa da za a yi, wato Alhaji Dauda Birma, ya kai ga Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Bamanga Tukur a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja shi da tawagarsa. A wannan ziyara, Alhaji Dauda Birma ya tabbatar wa duniya cewa lallai Goodluck Jonathn ne ya yi ruwa, ya yi tsaki don a saki Manjo Al-Mustapha. Wanda ban da ma kafar sadarwar Premium Times, yawancin kafafen watsa labarai sun ruwaito wannan ziyara, irin su Daily Trust da sauransu, inda Dauda Birma ya yi godiya ga Bamanga da Jonathan a kan sakin Al-Mustapha.
Ya ku Bayin Allah! Sannan duk wani dan Najeriya yana sane da irin cin mutunci da wulakanta Arewa da ’ya’yanta da mutane irin su Asari Dokubo da Dokta Fredrick Fasheun shugaban OPC da cif Ralph Uwazuruike shugaban MASSOB da ke fafutikar ballewa daga Najeriya suke yi. Amma sai ga shi Manjo Hamza Al-Mustapha ya kai wa wadannan mutane ziyara da sunan wai a hada kai. Alhali wallahi ’yan Arewa suna kallon wannan haduwa ce kawai don a yaki Arewa da ’ya’yanta. Domin karin bayani a kan wannan ziyara, ka samu jaridar Daily Trust ta ranar Juma’a 13 ga Satumban shekarar 2013. Kuma sannan sai ga shi labari ya watsu cewa Goodluck Jonathan yana son ya yi amfani da Al-Mustapha don cimma burinsa a zaben 2015.
Bayan haka, sai rade-radi da ake ta yi na cewa za a sake farfado da wata kungiya ta makasa, wadda wai irin ta ta yi tashe a lokacin mulkin marigayi Abacha, domin maganin ’yan Adawa da gwamnatinsa. Wannan kungiya ana cewa an yi horar da wakilanta a kasar Isra’ila da Koriya ta Arewa. Saboda haka, yanzu ma Goodluck Jonathan zai sake farfado da irin wannan, domin shi ma ya yi maganin ’yan adawa da takararsa a shekarar 2015. An dade ana wannan zargin, kai har ma kafafen watsa labarai na yanar gizo da jaridu sun sha buga wannan labari, amma ba a taba fitowa aka karyata wannan labari ba, ko kuma a kai karar masu yada shi a kotu. Sai ga shi kwatsam Obasanjo ya ambaci wannan zargi da ake yi wa gwamnatin Jonathan a wasikarsa ta ran 2 ga Disamban, 2013 mai shafi 18.
Ya ku bayin Allah! Ku sani, duk wadannan bayanai ba wai na kawo su ba ne a hudubata don ina adawa da sakin Manjo Hamza Al-Mustapha daga kurkuku, a’a, wallahi! Ko kusa ba haka ba ne. Ina ganin alkunuti da addu’o’in da muka yi a wannan masallaci domin a saki Al-Mustapha sun isa su zama shaida a kan haka. Kawai na yi wannan huduba ce domin mu fahimci cewa, ko dan uwanmu ne yake neman kaucewa, to, za mu yi masa nasiha ya ji tsoron Allah, idan kuwa ya ki ji, to, za mu bar shi komai kusancinmu da shi. Sannan kuma komai nisanmu da mutum idan ya zo da gaskiya za mu karbe ta mu yi aiki da ita, domin wannan shi ne koyarwar addinin Musulunci.
Ya Allah Ka nuna mana gaskiya kuma Ka ba mu ikon bin ta. Ka nuna mana karya, Ka ba mu ikon guje mata. Kuma ina rokon Allah Mai kowa Mai komai Ya gafarta mana baki daya, amin.