Sako zuwa ga Manjo Hamza Al-Mustapha (2)
Daga Imam Murtada Muhammad Gusau (Abu Mus’ab),Masallacin Juma’a na Nagazi Okene, Jihar Kogi Huduba ta Biyu: Bayan godiya ga Allah (SWT):Ya ku bayin Allah! Ku sani ba wani abu ne ya jawo ’yan Arewa suke dari-dari da duk wanda ya kusanci Jonathan da gwamnatinsa ba, illa irin yadda wannan gwamnati ta yi watsi da Arewa […]
Daga Imam Murtada Muhammad Gusau (Abu Mus’ab),
Masallacin Juma’a na Nagazi Okene, Jihar Kogi
Huduba ta Biyu:
Bayan godiya ga Allah (SWT):
Ya ku bayin Allah! Ku sani ba wani abu ne ya jawo ’yan Arewa suke dari-dari da duk wanda ya kusanci Jonathan da gwamnatinsa ba, illa irin yadda wannan gwamnati ta yi watsi da Arewa da jama’arta. Kashe-kashe da zubar da jinin bayin Allah suna addabar Arewa, amma gwamnatin Jonathan ta ki daukar mataki kwakkwara domin kawo karshen wannan bala’i. Kullum sai asarar rayuka da dukiyoyi Arewa take yi, amma sai aka sa siyasa cikin al’amarin don cimma wata manufa ta 2015. Babu abubuwan more rayuwa a Arewa, babu komai, kuma wallahi ana yi ne da gangan domin kawai wahala ta addabe mu mu yi ta fada da junanmu. Sannan ga shi wata hanya da aka dauko ta hada Musulmi da Kiristocin Arewa fada, inda za ka ga shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Mista Ayo Oritsejafor ya gayyato wasu daga Kiristocin Arewa zuwa Abuja da sunan wai sun kai masa ziyara. A yayin ziyarar zai kawo Naira miliyan biyu ko miliyan uku ya ba su, ya gaggaya musu maganganu domin ya hada su rigima da Musulmin Arewa. Ya rika cewa wai a Arewa ana cutar su ana danne musu hakki, saboda haka zai kwato musu ’yancinsu. Ko kuma wani makirci da aka dauko sai wani mutum ya tura wa kafafen watsa labarai wani sako da aka tsara da kyau, ya ce shi ne Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram, saboda haka suna yakar gwamnatin Goodluck Jonathan ne saboda yana Kirista. Kuma a cikin sakon wannan mutum sai ya ce sai sun kashe Kiristoci, ko kuma ya ce za su ci gaba da yakar Kiristoci. Wannan kawai domin a kara rikirkita Arewa da jama’arta ne. Ta wannan ne suke ganin za su cimma burinsu a shekarar 2015.
Daga cikin makirce-makircensu bayan wannan, akwai maganar za a yi amfani da kudi da mukamai don sayen wasu daga manyan Arewa, ko wasu daga masu fada –a-ji a Arewa.
Ya ku bayin Allah! Koma dai mene ne mu abin da muke cewa shi ne: “Lallai wayo ya san na ki.” Kuma wallahi Allah ba Ya barci.
Ku kalli maganar kasafin kudi na bana (2014) da Ministar Kudi Ngozi ta gabatar ga majalisu, inda aka ware wa Ma’aikatar Kula da Yankin Neja-Delta Naira biliyan 111, wannan fa ban da hukumar nan mai kula da yankin Neja-Delta (NDDC), Sannan ban da shirin yin afuwa ga tsageru (Amnesty). Kada mu manta fa kuma akwai kashi 13 cikin 100 da ake ware musu daga kason cinikin man fetur. Amma yankin Arewa maso Gabas da ke fama da rikice-rikice nawa aka ware masa? Ba Naira biliyan biyu kawai aka ware masa ba? Saboda haka shi ya sa ’yan Arewa suke neman canji a yau.
Ya ku bayin Allah! In ban da raina hankalin ’yan Arewa da aka yi mu kalli kasafin kudin jihohin yankin Neja-Delta sannan mu kalli na jihohin Arewa. Ba dole yunwa da fatara da tashe-tashen hankula da cututtuka su addabi Arewa ba? Saboda haka wallahi an sha mu mun warke. Malam Bahaushe yana cewa: “Idan maciji ya sare ka, to, ko tsumma ka gani za ka zura a guje.”
Ya kai dan uwa Manjo Hamza Al-Mustapha! Lallai ka sani wannan shi ne dalilin da ya sa ’yan Arewa ba za su taba saurara wa duk mutumin da ya ce zai hada kai da gwamnatin Goodluck Jonathan ya cuce su ba, koda kuwa daga yankin na Arewa ya fito, kuma ko shi wane ne.
Wallahi mu ’yan Arewa mun gaji! Mun gaji!! Mun gaji!!! Da irin wulakancin da wannan gwamnati take yi mana. Canji kawai muke so, kuma wallahi mutum ko shi wane ne ya kama girmansa, ya kiyayi kansa daga sayar mana da ’yanci don kwadayin mukami ko wani abin duniya. Kuma wallahi muna kiyaye da wadanda ke kokarin raba kan jama’a don a samu saukin cin nasara a kanmu, a ci gaba da cutar da mu.
Ya ku bayin Allah! Mu sani fa, shi mumini ba wawa ba ne, kuma ba soko ba ne. Ba yadda za a yi ya kasance an cuce ka yau, an cuce ka gobe, kuma ka bari a ci gaba da cutarka. Ko ka yarda a yi maka wani dadin baki ko romon baka don a ci gaba da cutar da kai.
Imamu Bukhari: 6,133 da Muslim: 2,998 da Al-Haakim da Baihakiy da Abu Dawud sun ruwaito Hadisi daga Abu Huraira (RA), ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ba a cizon mumini sau biyu a wuri daya (rami daya).” Wannan Hadisi ingantacce ne, Sheikh Muhammad Nasiruddeen Al-Albaniy ya kawo shi a Sahihul Jami’i, Hadisi na 7,779 da Silsilatul Ahadisus Sahiha, Hadisi na 1,175.
Daga karshe ina kira ga Manjo Hamza Al-Mustapha ya ji tsoron Allah ya hada kai da ’yan uwansa ’yan Najeriya masu son ganin an ceto kasar nan daga rugujewa ba masu son rusa ta ba. Ya kamata abin da ke faruwa a kasashe irin su Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya da Sudan ta Kudu da Somaliya da sauran kasashen da ake tashe-tashen hankula ya zama darasi a gare mu. Mu kasance masu hakuri da junanmu, masu yafiya, mu manta da abin da ya faru a baya, mu kalli gaba. Cewa za ka tona asirin abin da ya faru a baya tun daga 1974 zuwa yau, ba shi ne ba. Domin ba abin da hakan zai kara mana mu ’yan Najeriya. Shin wai ma a lokacin da aka yi kana ina? Ba da kai aka yi ba, idan ma an yi din? Me ya sa tun da can ba ka bayyana ba sai yanzu? Saboda haka don Allah tunda har ka ce ka yafe, to ka bar ta haka. Allah Ya yafe mana baki daya, amin.
Ya Manjo Al-Mustapha! Ina hada ka da Allah, don girman Allah, don Allah ka manta da abin da duk ya faru. Sannan don Allah kada ka yarda a yi amfani da kai ta kowace hanya a cuci al’ummarka. Sannan kai naka kura-kuran ka roki Allah Ya yafe maka, insha-Allah za ka samu Allah Mai rahama Mai jinkai. Kai kuma laifuffukan da wasu suka yi maka ka yafe musu, ka manta da duk abin da ya faru. ’Yan Arewa da ’yan Najeriya mu ji tsoron Allah, mu sani lallai kasar nan tana bukatar hadin kanmu, domin samun zaman lafiya.
Allah Ya albarkace ni da ku baki daya a cikin bin Alkur’ani Mai girma, Ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da zikirori. Ina fadar wannan magana tawa, ina mai rokon gafarar Allah ga kaina da ku da daukacin al-ummar Musulmi daga dukkan zunubai, ku nemi gafarar Allah, lallai Shi Mai yawan gafara ne Mai jinkai.
Imam Murtada Muhammad Gusau (Abu Mus’ab),
Masallacin Juma’a na Nagazi Okene, Jihar Kogi
08038289761