Sakon azumin Ramadan: Buhari ya nemi ’yan Boko Haram su ajiye makamansu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’ya’yan kungiyar Boko Haram su ajiye makamansu su dawo ga koyarwar Musulunci na gaskiya. Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a sakonsa na taya al’ummar Musulmin Najeriya fara azumin watan Ramadan a jiya Alhamis, inda ya yi kira ga masu tayar da tarzoma da sunan addinin Musulunci su […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’ya’yan kungiyar Boko Haram su ajiye makamansu su dawo ga koyarwar Musulunci na gaskiya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a sakonsa na taya al’ummar Musulmin Najeriya fara azumin watan Ramadan a jiya Alhamis, inda ya yi kira ga masu tayar da tarzoma da sunan addinin Musulunci su daina bata wa addinin suna.
Sakon da Shugaba Buhari ya fitar ta hannun kakakinsa Malam Garba Shehu, ya ce “A daidai wannan lokaci da muke kokarin magance matsalar Boko Haram a kasashen yankin Tafkin Chadi, zan yi amfani da wannan dama wajen kira ga ’yan uwanmu wadanda aka kawar da su daga hanya, su ajiye makamansu, su rungumi zaman lafiya, sannan su nemi ilimin addinin Musulunci na hakika a wannan lokaci da bayansa.”
Sai Shugaba Buhari ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi amfanin da wannan wata na azumin Ramadan wajen taimaka wa sauran jama’a, tare da aiki da darussa da bin sakonnin da addini ya tanada kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar.
Shugaba Buhari ya yi kira ga ’yan Najeriya a kan su yi addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban kasa a wannan lokaci da Musulmi ke fara azumin watan Ramadan na bana.
Shugaban ya yi addu’ar samun zaman lafiya a duk fadin kasar nan da duniya baki daya.
A jiya ne al’ummar Musulmin Najeriya suka bi sahun ’yan uwansu na kasashen duniya wajen fara azumin watan Ramadan na bana bayan da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bayar da sanarwar ganin jaririn watan azumin Ramadan a shekaranjiya Laraba da daddare.
Ya ce fadarsa ta samu labarin ganin watan ne daga Sarakunan Musulunci a sassan kasar nan da kuma kwamitin ganin watan.
Sarkin Musulmin ya kuma kara da jan hankalin al’ummar Musulmi kan su zage dantse wajen neman rahamar Ubangiji a watan na Ramadan.