Sakon Bagizagen Mako

Bakonmu na wannan mako, shi ne tsohon Shugaban Kungiyar Gizago na Najeriya, Malam Sharif Auwal Falala FCT-Abuja (GZG002ABJ), 07037627777. Ga sakon nasa da yake cewa:   “Gizagawa barkanmu da wannan lokaci, a kuma wannan rana ta yau mai albarka. Kun dade ba ku ji ni ba, kamar yadda ni ma na dade ban ji ku […]

Sakon Bagizagen Mako

Bakonmu na wannan mako, shi ne tsohon Shugaban Kungiyar Gizago na Najeriya, Malam Sharif Auwal Falala FCT-Abuja (GZG002ABJ), 07037627777. Ga sakon nasa da yake cewa:

 

“Gizagawa barkanmu da wannan lokaci, a kuma wannan rana ta yau mai albarka. Kun dade ba ku ji ni ba, kamar yadda ni ma na dade ban ji ku ba. Allah Ya sa alheri, amin.

“Lokaci ya yi da ya kamata in yi muku kaimi kamar yadda muka saba, dangane da irin hobbasar nan da muka saba yi na sadar da zumunci a tsakanimmu, kamar tallafa wa marayu, wadanda ibtila’i ya auka wa, kai ziyara gidajen yari, taimaka wa daliban makaranta domin shirya gasannin kacici-kacici, shirya tarurrukan Goron Sallah a duk lokutan bukukuwan Sallah karama da babba, shirya babban taron kasa na shekara-shekara da ziyartar juna, ziyartar iyayen kungiya na jihohi da na ƙasa, ziyarar taya murna da jaje da kuma auratayya a tsakanimmu da sauran ayyukan alheri da muka faro tun farkon kafuwarmu a shekarar  2009 zuwa wannan shekara da take dab da karewa (2019).

“Na yi mana wannnan tambihi ne don tunatarwa gare mu game da wannnan kungiya mai albarka, karkashin hazikin shugabanta, Muhammad Kabir Adam Gombe, mu tallafa masa da dukkan goyon bayanmu da iyawarmu don ganin mun kai ga gaci, domin taya su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, tare da ’yan majalisarsa da shugabannin jihohi na wannnan kungiya tamu mai albarka.

“Ina gode muku Gizagawa da yadda kuke juriya, musamman jajirtattun da ba sa gajiyawa.”

 

 

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara