Sakon Buratai ga Sojoji: Ku fada min matsalolin ku
Yayin tattaunawa da Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai, ya yi da Rundunar sojojin Operation Lafiya Dole, da ke yaki da ‘yan Boko Haram a Maiduguri babban birnin jihar Borno, ya bukacesu da su fada mishi matsalolin da rundunar ke fama da ita a fagen daga. Janar Buratai, ya jaddadawa rundunar cewa […]
Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai
Yayin tattaunawa da Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai, ya yi da Rundunar sojojin Operation Lafiya Dole, da ke yaki da ‘yan Boko Haram a Maiduguri babban birnin jihar Borno, ya bukacesu da su fada mishi matsalolin da rundunar ke fama da ita a fagen daga.
Janar Buratai, ya jaddadawa rundunar cewa sun bayyana duk irin kalubalen da suke fuskanta, don fuskantar yadda za a magance matsalolin su hakan zai iya sa a samu nasarar shirin yakar masu tada kayar baya da suka addabi yankunan Arewa maso Gabas a Najeriya.