Sakon da ke dauke da ruwan guba ya kona direba da fasinjoji 5

Direban wata mota da wadansu fasinjoji biyar sun kone da ruwan  guba da ake amfani da shi wajen yin katifa inda ya yi sanadin mutuwar wani dan kabilar Ibo daga cikinsu. Lamarin ya faru ne a karamar Hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa a kan hanyarsu ta zuwa Gombe daga Kano a ranar Larabar makon jiya. […]

Sakon da ke dauke da ruwan guba ya kona direba da fasinjoji 5

Direban wata mota da wadansu fasinjoji biyar sun kone da ruwan  guba da ake amfani da shi wajen yin katifa inda ya yi sanadin mutuwar wani dan kabilar Ibo daga cikinsu.

Lamarin ya faru ne a karamar Hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa a kan hanyarsu ta zuwa Gombe daga Kano a ranar Larabar makon jiya.

daya daga cikin fasinjojin da lamarin ya rutsa da su kuma Sufeton Hukumar Kwastam dan asalin Jihar Gombe, mai suna Usman Ibrahim, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe hudu na yamma.

Usman Ibrahim, wanda yanzu ake yi masa jinya a gidansa da ke Unguwar Tudun Wadan Pantami, Gombe ya ce a ranar Larabar makon jiya, ya je Kano don yi wa wani wansa ta’aziyar rasuwar ’ya’yansa 4 da sa suka kone a gobara a gidansa da kuma jajanta wa matarsa da take jinya a Asibitin Malam Aminu Kano.

Ya ce bayan ya gaishe su ne sai ya zo bakin Kasuwar Kwari, inda suka shiga wata mota kirar Golf 3 su biyar, biyu a gaba uku a baya, ashe direban motar ya karbi sakon sinadarin ruwan guba na yin katifa ba su sani ba, kuma suna cikin tafiya ne a daidai Gwaram sai wani mai babbar mota ya biyo ta hannunsu, kuma kaucewar da direbansu zai yi sai suka yi karo da turken fitilar kan hanya a nan ne ruwan gubar ya fashe ya kona su har da direban.

Usman Ibrahim, ya ce daga nan ne kawai sai ya samu kansa a wani asibiti a garin Gwaram zuwa lokacin da wani yayansu mai suna Auwal Adamu, Kakakin Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) ta Gombe ya je ya dauko shi. Ya ce fuskarsa ta kone ba ya iya gani amma kwayar idanun ba su tabu ba.

Ya ce bai san halin da sauran suke ba, sai dai ya san ruwan gubar ya kona su, amma daga baya wani dan kabilar Ibo ya tabbatar masa cewa wani dan kabilarsu daga Jihar Enugu da lamarin ya shafa wanda ya rasu.