Sakonni: Mallam ya handame kaza a kwano

Assalamu alaikum,warahmatullah.Bayan sallama irin ta masu fuskantar alkibla da kadaita Mahalicci, tsiran Allah da aminci su kkara tabbata ga shugabanmu wanda aka aiko domin rahama ga ababen halitta, da alayensa da sahabbansa amin. Bayan haka ina kira lallai ga dalibai na farfajiyar wannan makaranta,da su baza na zomo suji abin da zan fada musu. A […]

Sakonni: Mallam ya handame kaza a kwano

 Babban mutum mai rawani na zane ‘yan rawa da masu dukan tamolaAssalamu alaikum,warahmatullah.
Bayan sallama irin ta masu fuskantar alkibla da kadaita Mahalicci, tsiran Allah da aminci su kkara tabbata ga shugabanmu wanda aka aiko domin rahama ga ababen halitta, da alayensa da sahabbansa amin. Bayan haka ina kira lallai ga dalibai na farfajiyar wannan makaranta,da su baza na zomo suji abin da zan fada musu. A batu na waskiya wannan wata daya arce wata ne na neman tuba da neman gafarar Mahalicci da neman ‘yan tarwa daga wuta.
Ina mai ja mana na zomo da mu ci gaba da bibiyar Mahaliccinmu, har bayan wata wata mai alfarma, kada mu ce tunda wata mai alfarma ya arce bari mu koma ruwa mu yi ta iyo kamar  kwadi. Kada mu zama kaza samu kiki dangi, kamar yadda Direban allinmu ya ba mu labarin labari makon da ya arce akan yadda wani mallam da ya handame kaza akwano. Haka zalika kada aje a rakashe da bikin sallah kamar yadda na mujiya ya gane mana ni da shagaba na Jihar Tumbin Giwa, a shekarar da ta arce a inda ake adana manyan dawa.Batu na waskiya anan muka ga su Zinaru da Zillaziyya ana ta wasa irin na mutanen hindu, kamar a mjigi. Idan zaka shiga wannan guri sai ka biya Hauro Babban Lauje da Zagaye,sannan ga dakarun kwankwatsa-tsiya,suna gadin wannan farfajiya. Sun zama kyanwar lami, Mai-duka ya kawo mana dauki amin.
Kuma ina kara jan na zomo ga dalibai akan wani da ke batu akan cewa shi sabon direban alli ne, a batu na waskiya dole ne mu an kare akan haka, amma sauran batu za ku jini a darasi na gaba.
Ina fatan kun je Gano har ku wuce zuwa Ghana. Daga Halliru Gogel

Jan na-zomo ga adon gari
Ya ku adon gari, ‘yan’uwa na mata masu canja launin fatar su (bleaching) ku ji tsoron Rabbi Madaukaki, ku daina, domin yin hakan bai dace ba, daga cikin illolin yin hakan
1. yana da illa ga lafiyar fatar jiki, dankuwa Rabbi sarki sili guda acikin litafin shiriyar nan guda yace: “kada da hannayen ku ku jefa kawunan ku zuwa ga halaka.” a wani bangaren ya ce “Allah shi ya fitar da ku daga mahaifar iyayen ku baku san komai ba, ya sanya muku ji da gani da kuma hankali domin ku gode masa.”
Allah shi ya halicci mutum ya kuma kyautata halittar tare da girmama ta, shida ya samar da ke shi ya fi sanin yanayin launin fatar da ta dace da ke.
2. Raina halittar da jalla gwani ya yi miki, hakan kuma na jawo fushin Jalla gwani guda, don kuwa koda mahaifin ki ne ya sayo miki sutur-turu suturar arzaki don kare mutuncin kanki da nasa dama zuri’ar sa, a bakacin ki yi masa godiya da wannan goma ta arziki, sai ki tattara ki ka mulmula ki ka cunkusa ki ka watsar da su, ki ka dauki kayan banza da na sharholiya ki ka rataya, ransa zai tarwatse (baci,) ballantana Allah da ya yi miki duk abin da ya dace da ke,
3. Annabi rahma SAW ya ce: “Allah ya tsinewa wacce ke canza halitta, da kuma wacce aka canza mata.”
Ya ke ‘yar uwa me kike nema a duniyar nan da har za ki tasrgade, ki  kai kanki ga azabar Ubangiji?
Miji ki ke so !, ko Hauron Haurobiya? ki roki Allah ba abin da ba zai ba ki ba, ki gyara zuciyar ki yadda ya kamata, ki sha mamaki.
Da fatan sakon ya isa ga inda ya dace.
Daga SABIU UBA YOLA. 07032385544 07055417766 Shagaban daliban Jihar da Fullo-ke-damawa

A tsunduma cikin Makarantar Malam Dodo
daya daga cikin Dalibai Ma’abota Sha’awar nutsewa tsundum cikin makarantar Malam-bude-mana-littafi yayi nazarin a karkashin Sharhinka Na ta’aziyya ga Editan Media Trust Mal. Sulaiman Muh’ammad hakika mun yi rashi, kuma muna fatan za mu koyar kamar yadda muka koya. Allah Ya sa za ku saka ni cikin rukunin ma’abota ra’ayin budewa da nazarin Wagagen litattafai. Sai na jiku. Na gode. Sani Sulaiman. [email protected].

Gaisuwar salla da ta’aziyyar dan uwanmu
Salamun alaikum. Gaisuwar Barka da Sallah, irin tama’abota fadfutikar tabbatar da abin da yake daidai, tare da baude wa karkatacciyar hanya, wato babban jagora, Malam Dodo. Allah Ya kara imani da basuira da kuma daukaka, tare da sauran ’yan uwa.
Bayan haka ina mai kwaye alhinina game da rashin sili guda daga cikin ’yan uwa dalibai na Jihar da Fullo ke- Damawa, mai amsa kiran sunan Abubakar Babani. A ’yan kwanakin da suka arce, ya koma ga Rabbu, bayn ya yi fama da rashin koshin uwar jiki na mikatin haske da duhu guda. Daga Sabi’u Uba Yola, Shagaban daliban Jihar Da Fullo-Ke-Damawa. 07032385544/07055417766

Mun kakaba tagiyar Malam Tunau
Assalamu Alaikum
Dukkan Godiya da jinjina sun tabbata ga Mai Duka, wanda ya yi sama da kasa ba tare da taimakon kowa ba, haka nan ya yi sama ba tare da dirkokin da suke rike da ita ba. AmincinSa ya kara tabbata ga Cikamakin Annabawa wanda ya zo mana da shiriya da hanyoyin karatu da ilimi.
Bayan gaisuwa irin ta masu bautar Fiyayyen Sarki daya tilo. Ina isar da babbar gaisuwata ga uban wannan makaranta Shaikh Malam Farfesa Dodo Uban Masu Karatu, da fatan an shiga ibadar azumi cikin nasara, haka ma ga daukacin daliban wannan makaranta mai albarka da tarin alkhairi na kasa dama na duniya baki daya.
‘Yan uwa na dalibai ina tunatarwar damu, da mu rika amfani da basirar da Allah ya horewa Uban Masu Karatu Farfesa Dodo, kamar yadda na tuna wata haduwa da muka yi da shi ya yi mana nasiha da mu riki wannan makaranta a matsayin wani waje da zai zama hanyar alkhairi gare mu da ‘yan uwanmu ta hanyar kyautata musu da taimaka musu yayin da bukatar hakan ta taso.
Wannan tasa na ke kira a garemu da kar watan azumi ya wuce ba mu rubanya ayyukanmu na lada ba, kar mu rena kyautar da za mu bawa dan uwanmu ko ‘yar uwarmu ko makwabcinmu ko abokinmu, duk kankartarta ko da tsagin dabino ne ka bayar domin ya zama ka karawa ladanka nauyi.
Kar na tsawaitaba da bayani na san tuni an je gano, ina yekuwa ga daliban Tumbin Giwa da mu kara jajircewa wajen gudanar da tafiyar makaranta.
Na gode,

Umar Muhammad Abdullahi (Abban Haidar)
Shugaban daliban Jihar Tumbin Giwa, Na Riko.
08067676454, 08099767645.