Sakonnin makaranta
Haurobiyawa da gama-garin gamin gambizar masu koyon watsattsake da tafiyar tsutsa, tare da falle shafuklan mujallau da makalu da jaridu a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, yau mu kwararo bayanan dalibai. Kuma dalibai Adon-gari da ba su hango sakonninsu na wulkitawa a allon makaranta ba, sais u tuhumi jami’in […]
Haurobiyawa da gama-garin gamin gambizar masu koyon watsattsake da tafiyar tsutsa, tare da falle shafuklan mujallau da makalu da jaridu a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, yau mu kwararo bayanan dalibai. Kuma dalibai Adon-gari da ba su hango sakonninsu na wulkitawa a allon makaranta ba, sais u tuhumi jami’in hulda da al’umma, wanda ya ki cillo mana bayanan Uwargida ‘’yar Santalusiya da ’Yar Taiwan; kai ko ma UWARGADA ce Haurobiyawa za su so jin batunka ko don su yi mata gyara. Kodayake muna jan na-zomon al’umma kan ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege.
’Yan makaranta a baje na-mujiya, a sha karatu cikin lumana lumui:
Ta’alikin fetsarar
Farin-biri
Mun gode Allah ya kara basira
Sani Muhammad Gumel, 08035212931
Martani: Taradaddin tabargazar Tarba-tarba
ASSALAMU ALAIKUM.
Bayan gaisuwa irin ta ma’abota kadaita Jalla Gwanin Sarki da bauta, da fatan Malam kuma jagoran watsattsake a farfajiyar Amintacciyar jaridar Haurobiya yana cikin koshin lafiya Allah ya kara inganta maka kwanyarka (BASIRA) ya kuma kara daukaka mai amfani da amfanarwa.
Haka ma sauran ‘yan uwa dodanni.
Ana ingarman doki ‘yan uwa Fullon kejo suna cikin halin cin na tsiren mata a cikin burtalolin Haurobiya.
Abin da zai taba maka kiraza shine irin yadda ita kanta kungiyoyin Fullon kejo suna tada yaggun wuya a matsayin ita ke kare hakkin su, amma idan ka baje na-mujiyar ba za ka gan shi a kar ba.
Hakan tasa wasu jagabobin jihohi da jama’ar su ke shin kau.da fullon kejo da nagge a Haurobiya.
Abin haushi da taba kalbu ga irin ta’addan ci wasu kabilun TARBA-TARBA, ga irin dukan uwa da ‘yar tare da riga uban kaiwa kara saboda su shafaffu ne da mai.
Amma ba’adu bayan haka ‘yan doka da ke kan gwadabobin mu ya kamata ku tausaya wa Fullon kejo sai ga shi duk jirgin da ya taso dauke da su sai ku sauke su a shingayen ku, har ma da cin zafi kai ka ce zomayen da Burburta a ke kashewa ne a dajin su Alanguboro.
Ana ingarman doki ya dace amutunta su saboda ai ba bakin haure bane cikakkun Haurobiyawa ne.
Kuma suna da abubuwan da ke inganta rumbun kasa, darajar YAMDU aka ce nama, kuma suke samar da shi daga nagge da karsanar da bujiminsu.
Muna rokon Rabbil Izzati ya kawo mana zaman lumana da bacci, tare da minshari cikin annashuwa.
Bugu da dadi babban jagoran Haurobiya da ke kwance muna yi masa addu’ar Allah ya ta da kafadarsa, ya komo Haurobiya don cigaba da shuka wa Haurobiyawa aikin alheri.
A intaha na ke cewa.
NJUNDE JAM WANI DANGRANGE JIHAL YEESO.
Daga Jagaban Jihar da Fullo-ke-damawa.
SABIU UBA YOLA. 07032385544
A daina wulakanta Hauro
Bayan Sallama irin ta addinin gaskiya,
Ina fatan dukkan dalibai da masu makalewa (‘yan kulallabo-kulabe) a kan katanga su na leke da satar kallon abin da ake yi makaranta, ina fatan dai duk muna amfana da karatun da Shehin shehunnan wannan makaranta, kuma Direban alli yake bayarwa ba tare da mu na bashi ko na ruwan-leda ba.
Ina kira ga jama’armu ta Haurobiya, musamman na nahiyar Arewatawa da mu kiyayi wulakanta Hauro, wannan abu yana ci min tuwo a akushi, idan na ga yadda jama’a ke dukungunawa da yaga su, ba a shiryasu yadda ya kamata, mu samman hauron na leda, mai muttala da fan-biyar da fan-biyu da sule biyar. Mai duka ya sa mu gane mu gara mu alkinta Hauro.
Fatanmu Mai-ni-da-kai, Mahaliccin sammai da kassai ya yi masa jagoranci akan dukkan rayuwarsa tare da Hukumar Kamfanin dab’i da buga Amintacciyar Jaridar da suka ba da wannan dama ta ilimantarwa.
Kamar yadda aka sani dai ga mai sha’awar zama daya daga cikin ‘yan kungiyar wannan makaranta na reshen Jihar Tumbin giwa mai iyaka da ta Dikko Dakin kara da Jihar Jijjiga ciyawa, da ma kasar Haurobiya yana iya neman mu ta lambobin kurtun maganarmu: Mal. Aliyu Mukhtar Sa’id (IT) – 08034332200, Umar M. Abdullahi – 08067676454.
Daku Umar Muhammad BUK.
08067676454