Sakonnin makaranta(A)
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wa-barkatuhu ‘yan uwana dalibai. Bayan gaisuwa irin ta masu fuskantar alkibla wajen bauta wa Mahalicci sili, Ina fatan babban malaminmu, kuma shugaban wannan makaranta, wato babban direban alli, malam DODO uban Dodanni yana lafiya tare da karamar Dodanniya, wato Nana As’ma’u. Haka kuma ‘yan uwana dalibai ina fatan kuna halin ‘koshin lafiya. […]
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wa-barkatuhu ‘yan uwana dalibai. Bayan gaisuwa irin ta masu fuskantar alkibla wajen bauta wa Mahalicci sili, Ina fatan babban malaminmu, kuma shugaban wannan makaranta, wato babban direban alli, malam DODO uban Dodanni yana lafiya tare da karamar Dodanniya, wato Nana As’ma’u.
Haka kuma ‘yan uwana dalibai ina fatan kuna halin ‘koshin lafiya. Kamar yadda malam ya yi darasi a makon da ya arce mai taken “Ciwon Cibin-Boko”, To lallai wannan darasi ya ja hankalina kuma ya fargar da ni domin yin watsattsake a wannan farfajiyar makaranta mai albarka.
A matsayina na shugaban daliban wannan makaranta, ina mai Allah wadai da tir da wannan al’amari da ake ta batunsa, wanda ya dami Haurobiyawa, wato na wafce Adon-gari sama da dari karamin lauje a makarantar sakan-ni-in-diri da ke garin Cibin-boko.
Kamar yadda kowa ya sani a ciki da wajen Haurobiya, babu abin da za ka ji ana ta batu a kafafen yada labarai na akwatunan magana mai hoto da mara hoto da kuma watsattsakewa a mujallu da jaridu da mashakatar lilo da tsallake-tsallake kamar wannan batu na wafce Adon-gari. Kuma ma wani abin da ya dada tayar da hankali da kura akan wannan al’amari shi ne; na fitowar shugaban masu haramta bobo da kwambon bokoko a wani majigi da suka aika ta mashakatar lilo da tsallake-tsallake, da ke ikirarin cewa su suka wafce wadannan Adon-garin, kuma ya yi barazanar za su sayar da su ga masu bukatar mutum don yin kwadago.
Hakika a matsayinmu na dalibai kuma masu koyon watsattsakewa da buda wagaggen littatafai a wannan makaranta na Dodorido, muna matukar nuna alhini da jaje ga iyayen wadannan Adon-garin da dalibai da kuma Haurobiyawa baki daya.
Kuma muna kara kira da babbar murya ga Jatau Mai-gudun Loko da ya yi duk abin da ya kamata don ganin an ceto wadannan Adon-garin, duk da cewa mun san ya gaza. Eh! ya gaza mana.
Saboda a yanzu ya fito fili ya fada wa duniya a wajen taron Tsimi-da-Ta’adi ga lukudi ga cinye kudi na duniya da aka gudanar a Haurubja babban birnin Haurobiya a makon da ya arce, cewa: kasar su Uban-mama jikan kenyawa jagoran Amurkawa da kawayenta sun amince da gayyatar da ya yi musu don taya shi ceto wadannan Adon-gari da kawo karshen masu tayar da kayar baya a kasar nan baki daya.
Ita kuma Damo Hakuri, muna nan mun zuba na mujiya, mun baza na zomo, domin jiran ranar da za ta jagoranci Banga-Banga a garin Cibin-boko da ta sha alwashin yi, domin gwamnan garin su Alan-guburo ya fiddo da wadannan Adon-gari, kamar yadda tanu shakku da batan dabon da suka yi da kuma jefa azargagiyar zargi ga gwamnan cewa ai yasan inda suke, a yayin da ta mance da cewa mai gidanta Mai-gudun loko shi ne shugaban baraden kasar nan kuma wanda alhakin tsare dukiya da rayukan Haurobiyawa ya rataya a wuyansa.
To matukar da gaske take yi, kuma ta tabbatar wa duniya da cewa ba kukan zuki-ta-malle ta yi ba, to muna jiran zuwanta wajen Banga-Bangan in ta shirya. uhm! To kun ji.
A karshe muna kira ga shugaban masu haramta Bobo da kwambon Bokoko da su yi wa Mai-duka da su sako wadannan Adon-gari da suka wafce, duk da cewa mun ji kun sake cillo majigin da yake nuna wadannan Adon-gari a halin koshin lafiya, amma kuma kun bada sharadin kafin ku sako su sai Gwamnatin Mai-gudun loko ta sako naku baraden. Toh! Mu dai anan sai dai mu ce Mai-duka ya kawo mana karshen wannan tashin-tashinan da yake lakume rayukan Haurobiyawa da ba su ji ba, ba su gani ba, Amin. Wassalam!
Daga Shugaban dalibai, Uncle Bash, Jimeta-Yola. [email protected] 07037133338
Addu’a Maganin Bala’i
Assalamu Alaikum. A zahiri lamura sun fara ziyartar aje-gunle wajen jagwal-gwalewa, wanda hakan bazarana ce gagaruma ga talakawan Haurobiya. Sai dai ina kara tunatar da mu cewaa bayan dukkan tsanani akwai sauki, don haka ya kamata mu dukufa rokon sauki daga Mai-duka. Allah Ya ba mu sauki a wannan kasa Amin. Daga Saddik Tukur Gwarzo 08060869978 [email protected]