Sakonnin masu karatu game da kishi

Abin takaici da bakin ciki, shi mijina, na kawo masa tafsirin Suratun Nur na sa ya ji, bai yi amfani ba.

Sakonnin masu karatu game da kishi

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa amin.

Ga sakonnin wasu daga cikin masu karatu a game da kishi da yadda ya kamata a yi shi. Ba ni son ta, shi yasa ba ni jin kishinta!

Na karanta bayaninku a kan irin kishin da ya halatta, sai dai ni na lura abu biyu ne ke sa ma’aurata su ji ba su kishin matan aurensu.

Na farko akwai karancin so da kauna, in ya kasance maigida ya rage son matarsa, ko kuma dama can ba son ta yake yi ba, to zai ba wani jin son ta a zuciyarsa.

Misalin ni din nan kin ga auren hadi aka yi mani, ba ni son matata, biyayyar iyaye ce kawai ta sa nake zaune da ita, don haka ba na wani jin kishinta gaskiya.

Abu na biyu da ke sa maza ba su jin kishin matansu shi ne, in ya kasance matar tasa ta sha gabansa da yawa, wato ta fi shi kudi ko wani matsayi, ko ya kasance ita ce take wa kanta komai, wani sa’in ma har shi maigidan ita ce take dawainiya da shi.

To kin ga ke nan sama ta dawo kasa, in ya ce zai yi kishi da kansa zai kwana ciki. Razanarwa game da rashin kishi.

Tambaya: Wai me ya sa mazan Hausawa ba su da kishi ne? Domin a iya nazarin da na yi, na lura namijin Bahaushe ba ya da kishi.

Hujjata ita ce, na tattauna da sauran ’yan uwana mata, sai na ga cewa irin matsalar da nake gani, haka sauran matan suka fada mani.

“Bahaushe ne mutumin da zai kyale kanensa ya shiga wajen matarsa, abokinsa ya shiga, kanen abokinsa ya shiga, abokan kannensa duk su shiga wajen matar kuma ba ya damuwa kuma koda ita matar ta nuna ba ta son haka, shi ba ya damuwa.

“Abin takaici da bakin ciki, shi mijina, na kawo masa tafsirin Suratun Nur na sa ya ji, bai yi amfani ba.

“Na kawo masa na Suratul Ahzab na sa ya ji bai yi amfani ba… “Abin karin bakin ciki, yawancin yaran da suke shigowa ko cikin kannen mijin, ko abokan kannen miji ko abokan mijin, wallahi za ka ga wani yaron ya fi mijinki kuruciya, ya fi shi ado, ya fi shi kwalliya amma fa ina fada da tsarkin zuciya…”

“Tambayata a nan ita ce:

1.Shin rashin imani ne ya sa Bahaushe ba ya kishin matarsa?

2. Ko rashin fahimtar addini ne ya sa Bahaushe ba ya kishin matarsa?

3. Shin me ya sa mafiya yawa daga mazajen Hausawa ba su damu ba da tsare mutuncin iyalansu?”

Amsa: Hakikanin gaskiya tambayoyi biyun farko: rashin imani ne? E, akwai raunin imani. Rashin fahimtar addini ne?

Kwarai da gaske, wannan shi ne tushen farko, domin dukkan mutumin da ya fahimci addini dole zai tsare matarsa.

In tana neman dalili na uku, bayan raunin imani, bayan rashin fahimtar addini sai kuma fifita al’ada a kan addini, domin a al’adance an saba kanin miji ya shiga gidan matar wansa ya yi wasa da ita har ma akwai wasan kanen miji; su yi ta kokowa duk babu komi.

Ya zauna ya yi hira da ita ana wasa da dariya, ya yi mata tsawa ta dafa masa abinci; ta yi wanka tana shafa mai a gabansa; ta canza kaya duk ba zai tashi ba kuma gashi baligi, ya zura ido ko kiftawa ba ya yi.

Kuma a al’adance, koda mijin ya zo ba ya jin haushi. Wannan ka ga al’ada ce, maguzanci ne, ba ya da alaka da addinin Musulunci.

Da ka’ida ta addinin Musulunci, ba wanda zai shiga wurin matarka sai kai, ko muharraminta – wanta ko kaninta, uwa daya uba daya, ko uwa daya kawai ko uba daya kawai.

Amma kai wanka ko kaninka, ba muharraminta ba ne, don haka haramun ne ya shiga wajenta sai bayan ta sa hijabi ta suturce kanta.

Haramun ne ya shiga wajenta a cikin wani hali da ba wannan ba; haramun ne ya je ya zauna su yi hira; haramun ne ya je ya zauna su ci abinci tare shi da ita.

Wannan bai halatta ba ta kowace irin fuska, wannan al’ada ce ba addini ba ne ba, don haka ya kamata mutane su kiyaye wannan.

Manzon Allah (SAW) ya razanar, inda ya ce: Dayyuz ba zai shiga Aljannah ba. Dayyuz shi ne mutumin da ba ya da kishi; mutumin da yake tabbatar da alfasha ga ahlinsa; mutumin da ba ya kishin matarsa; kanwarsa, ’yarsa ko yayarsa.

Dukkan wata muharramarsa ko matarsa ba ya kishinta. Bai damu ba ya ga wani ya kama kugun ’yarsa sun wuce ba; ko wani ya killata da ’yarsa ko yarsa ko kanwarsa duk bai damu ba.

Wannan Addayyuz ke nan, ba wai sai mata kawai ba, dukkan wadda kake da iko da ita, ya kasance ba ka damu ba, wani ya killata da ita a wurin da wani tsautsayi na iya faruwa kuma ba tare da kai ka ji wani abu ba, Manzon Allah (SAW) yac e ba za ka shiga Aljannah ba!!!

Don haka ya kamata a yi hattara. Kanin miji in dole sai ya ci abinci a gidanka, a ba yaro ya mika masa soro ya dauka.

Wa ya ce sai ya shiga ciki? In kuma ba yaron da za a turo, abin da aya ta ce shi ne: In za ku tambayi wani abu ku tambaya ta bayan katanga, ku tambaya ta bayan kyaure: Ya ce “Assalamu alaikum”

Ta ce “Wa alaikumus salaam.” “An gama abinci?” “Eh!” “To, a miko mani” Ta ce “to tsaya nan…” Sai ya tsaya ta miko kwanon ya dauka.

Amma ba sai ya shiga ciki ba. Wa ya ce ya shiga ciki? Wa ya ba shi izini kuma wa ya ba shi lasisi?

Daga cikin fatawowin marigayi Malam Ja’afar Mahmud Adam. Da fatan Allah Ya yi masa Rahama, amin.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara