Sakonnin masu karatu – tes da imel (5)
Salaamun alaikum, da fatan kana lafiya. Don Allah ina so a sanar da ni hanyoyin da zan bi wajen koyon ilimin hada alaka tsakanin kwamfutoci, wato: “Networking”, don Allah Baban Sadik. Nagode. Sharhabil Aliyu: [email protected] Wa alaikumus salam, Malam Sharahbil da fatan kana lafiya. Ina kara ba ka hakuri sanadiyyar yawan tuntubata da kake yi […]
Salaamun alaikum, da fatan kana lafiya. Don Allah ina so a sanar da ni hanyoyin da zan bi wajen koyon ilimin hada alaka tsakanin kwamfutoci, wato: “Networking”, don Allah Baban Sadik. Nagode.
Sharhabil Aliyu: [email protected]
Wa alaikumus salam, Malam Sharahbil da fatan kana lafiya. Ina kara ba ka hakuri sanadiyyar yawan tuntubata da kake yi kan amsar tambayarka. A yau dai Allah Ya yi; ga amsar tambayarka nan a sama, kamar yadda in har ka karanta wannan shafi a yau, na san ka samu bayanan. Kana iya bin wadancan hanyoyi da na yi bayaninsu a tambayar da ke sama, don cimma burinka a wannan fanni da kake son koyo. Bayan haka, ka duba akwatin Imel dinka, na cillo maka wannan bayani daga farkonsa zuwa karshe, don ka samu dubawa cikin natsuwa. Ina yi maka fatan alheri a ko ina kake.
Sunana Badamasi Alhassan Shanono. Wato na yi kwakwar samunka fuska da fuska mu gaisa, amma hakan ya ci tura. Amma har gobe ina nan a kan hakan saboda idan har Allah ya hada ni da kai, to, na tabbata zan yi karuwar da tafi wacca nake yi ta kafar sadarwa.
Daga Elbass Zuba – [email protected]
Malam Badamasi barka ka dai. Ina fatan Allah ya hada fuskokinmu da alheri. A hankali wata rana Allah zai hada mu. Kana iya turo mini sakon tes ta lambar wayar da ke wannan shafi, in ya so ta nan sai mu tattauna mu ga abin da zai yiwu. Ina godiya da kyakkyawan zaton da kake yi mini. Allah sa mu dace baki daya, amin. Na gode.
Assalamualaikum. Da fatan kana lafiya; ya ya Sadik, kuma ya ya aiki? Na gode sosai, da kasidar (Bermuda Triangle) din da ka turo mini. Allah ya saka maka da Aljannar firdaus, ya kuma kara maka basira. Bayan haka don Allah ina so ka turo mini wasu kasidu kamar haka:Binciken malaman kimiya a kan yadda barci ke samuwa da mafarki, Tsarin gadon dabi’u da siffofin halitta a kimiyyance,Tsakanin kimiyar Alkur’ani da ta zamani ina aka hadu? da kuma kasidar jirgin ruwa mai suna (Titanic). Ta akwatin Imail dina:[email protected]. Sannan kuma idan akwai kasidu a kan na’ura mai kwakwalwa (Computer) da abin da ya shafeta don Allah ka turo mini, saboda suna da amfani a gare ni sosai. A taimaka mini don Allah. A aiko mini ta wannan Imel din. [email protected], da na turo maka sakon da shi na manta password din shi. Saboda haka na bude wannan sabon. Don Allah malam ka taimaka. Na gode.
Daga Junaidu Musa
Wa alaikumus salam, Malam Junaid ina godiya da addu’o’i, Allah saka da alheri. Ina fata ana karuwa da dan abin da nake aikowa. Babban burina a rayuwa shi ne ya zama abin da nake yi yana amfanar jama’a. A halin yanzu na tattara wadannan kasidu da ka bukata, kuma na aika maka ta adireshin karshe da ka aiko. Tabbas na ga sakonka na karshe, inda kake nuna ka manta kalmar sirrin akwatin Imel din farko da ka aiko mini. Sai ka duba na biyun. Allah Ya sa a dace, amin.
Assalamu alaikum Baban Sadik, ina karatun amsoshin tambayarka a jaridar AMINIYA. Don Allah ina son in canza sunan da nike amfani da shi wajen hawa shafin Facebook (Facebook Username) dina daga Imel zuwa lambar waya, amma na kasa. Don Imel din ya daina aiki, amma ina amfanidashi har yanzu wajen hawa shafin Facebook. Ina iya yin hakan? Nagode.
Daga Shafi’i Kilgori, Jihar Sokoto:[email protected]
Wa alaikumus salam, Malam Shafi’i. Idan na fahimci tambayarka, kana son sanin ko zai yiwu mai shafi a Facebook ya iya canza sunan da yake hawa shafinsa da shi ne, wato: “Username.” Eh, wannan abu ne mai yiwuwa. Daman, ko dai ya zama adireshin Imel ne kake amfani da shi wajen hawa, ko kuma lambar waya. Hanyar hawa facebook ta uku ita ce ta amfani da lakabin mai shafi, wato: “Facebook ID,” wanda ba kowa ba ne ya san wannan. Lakabin mai shafi dai hadakar suna ne ko sunaye ko kuma wasu lambobi da adadinsu ya kai 15, wadanda manhajar Dandalin Facebook ne ke bai wa kowane mai shafi bayan ya yi rajista. A takaice dai wadannan su ne hanyoyin kuma kana iya canzawa iya gwargwadon yadda ka so.
Idan kana amfani da wayar salula ne, da zarar ka hau shafinka, ka gangara can kasa daga gefen hagu ka matsa: “Settings” idan ta “browser” kake hawa, ko kuma bangaren dama daga sama, idan kana amfani da manhajar Facebook ne (Facebook App). Da zarar ka shiga bangaren “Settings”, sai ka shiga “General Account Settings.” Ka isa wurin za ka ga jerin bayanai kamar haka: “Name”, “Username”, “Contact” da dai sauransu. Tsakanin wadannan ne za ka iya gudanar da abin da kake so. Ka je bangaren “Contact”, za ka ga lambar wayar da kake hawa shafinka da ita. Sai ka matsa, shafi zai budo. A nan za ka ga inda aka rubuta: “Add another email or mobile number.” Kana matsa wannan alama za a budo maka inda za ka shigar da adireshinka na Imel. Da zarar ka shigar sai ka matsa alamar “Sabe Changes” dake can kasa, za a bukaci ka shigar da kalmar sirrinka (Password) don tabbatar da cewa lallai kai ne mai shafin. Da zarar ka sa, za a turo maka wasu lambobi guda 4 ko 6 zuwa akwatin Imel dinka, tare da budo wani wuri da ake son ka shigar da zarar ka dauko lambobin. Sai ka je can ka dauko su, ka shigar a inda aka tanada. Kana shigarwa shi ke nan! An gama (sunan tsohuwa a wani yare).
A duk sadda ka tashi hawa shafinka sai ka rubuta adireshinka na Imel maimakon lambar wayarka. Sai dai kuma wata fadakarwa: Yana da kyau ka san cewa, don ka kara adireshin Imel, wannan na nufin ba za ka iya kara hawa da lambar ba ke nan. A a. ka kara hanyoyin hawa shafinka ne kawai. Fa’idar hakan shi ne, a duk sadda ka samu matsala da shafinka har aka kulle aka hanaka hawa, za ka iya bukatar a turo maka lambobi ta Imel dinka, musamman idan ka daina amfani da lambar wayar da ka sa a farko, don tantanceka tare da bude maka hanya.
Idan har ba ka son ka ci gaba da amfani da lambar a shafin, da zarar k agama dora adireshin Imel din, sai ka koma bangaren “Profile” a shafinka, ka gangara bangaren “Contacts,” sai ka matsa inda aka rubuta: “Edit Contact,” za a budo maka lambar wayar. A kasa za ka ga inda aka rubuta: “Remobe Number” ko wani abu makamancin hakan. Da zarar an cire lambar wayar shikenan. Allah sa a dace, amin.
Baban Sadik dafatan ka yi sallah lafia. Ina neman alfarmar da ka turo mini kasidar da ka rubuta kan fannin “Genetics”, data Samuwar Mafarki a Kimiyya.
Daga mai kaunarka Sulaiman Yunusa Gumel: [email protected]
Malam Sulaiman barka dai. Ina matukar godiya da kaunarka. Allah Ya tara mu cikin rahamarSa baki daya, amin. Ka duba akwatin Imel dinka, na aika maka wadannan kasidu da ka bukata. Allah Ya amfanar da mu baki daya, amin.
Assalamu Alaikum Baban Sadik, ya kamata ka ja hankalin matasa akan yadda takamata mu gudanar da rayuwarmu a kafafen sadarwa na zamani.
Nasiru Kainuwa Hadejia. 08100229688: [email protected]
Wa alaikumus salam, Malam Nasiru barka dai. Lallai wannan shawara ce mai kyau matuka. Alal hakika ga dukkan masu bibiyar shafukan da nake rubuce-rubuce ko wannan shafi na jaridar AMINIYA, hada har da kasidu da makaloli da na gabatar da laccoci da aka gayyace ni a wurare daban-daban cikin kasar nan, zai ga lallai babu maudu’in da nafi bayar da mahimmanci a kansa irin wannan bangare. Bayan haka, lokaci zuwa lokaci nakan tabo wannan maudu’i, ko dai yayin amsa tambayoyi masu alaka da shi ko ta hanyar shafina na Facebook ga masu bibiyata a can. Don haka, zan ci gaba da gabatar da fadakarwa a duk sa’adda dama ta samu. Ina godiya da wannan shawara. Allah saka da alheri, amin.