Sakonnin masu karatu – tes da imel (6)
Salaamun alaikum, da fatan kana lafiya Baban Sadik. Don Allah ina so ka yi mini cikakken bayani game da kalmar “Paypal,” kuma shin, sai lalai ina da taskar ajiyar banki (Bank Account) ne kafin in yi amfani da shi ko a’a? Daga masoyinka a yau da kullum: Amiru usman: [email protected] Wa alaikumus salam, barka dai […]
Salaamun alaikum, da fatan kana lafiya Baban Sadik. Don Allah ina so ka yi mini cikakken bayani game da kalmar “Paypal,” kuma shin, sai lalai ina da taskar ajiyar banki (Bank Account) ne kafin in yi amfani da shi ko a’a?
Daga masoyinka a yau da kullum: Amiru usman: [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Amiru. Ina godiya matuka da kaunarka gare ni. Ina rokon Allah ya sa mu yi tarayya cikin alheri baki daya, amin. Dangane da tambayarka, shafin PayPal dai shafi ne da ke bai wa mutane damar aiwatar da cinikayya ta hanyar biyan kudin hajojin da suka saya a shafukan Intanet cikin sauki, tare da ba su dama har wa yau wajen aika wa ‘yan uwansu kudi kai tsaye, watau “Instant Money Transfer” ke nan. Idan kana da rajista da wannan shafi har wa yau, za ka iya karbar kudin cinikin da ka yi na hajojin da kake tallatawa idan kana da shafin sayar da kayayyaki a Intanet. A takaice dai, kamfanin PayPal dai dillalai ne kan hada-hadar kudi a duniya ta hanyar Intanet. Bai wai banki ba ne mai zaman kansa.
Asalin wannan shafi dai ne ya faro ne daga babban shafin sayar da hajoji a Intanet mai suna: “Ebay,” daga nan ya fara hada-hadar kudi ta hanyar baiwa jama’a masu sayan hajoji a shafin “Ebay” damar biyan kudin hajoji, da kuma baiwa ‘yan kasuwa damar karbar kudaden da ake biyansu na hajojin da suke sayarwa a shafukansu na Intanet. Daga nan wannan shafi ya habbaka. A halin yanzu dai akwai masu rajista sama da miliyan 188 a duniya. Kuma shafin na samun kudaden shiga ne ta hanyar cajin hidima da yake wa masu rajista dashi. A karon farko dai kamfanin yakan tara kudaden da yake karba a madadin masu rasjita dashi ne a bankuna, yana karbar kudin ruwa kai tsaye daga bankunan, tunda suna aiwatar da kasuwanci da kudin, kamar yadda yake a tsarin hada-hadar kudade na zamani a kasashen Amurka da Turai. Daga baya da masu rajista da wannan shafi suka gano haka, sai suka rufe “account” dinsu suna ficewa. Domin wannan, a tunaninsu, ci da ceto ne.
Wannan bore da jama’a suka yi ne ya sa ya canza tsarinsa. Inda ya rika dora wa masu rajista haraji kan dukkan hidimar da ya musu. Harajin masu sayar da hajoji daban da na masu karba ko aika kudade ga ‘yan uwa ko abokansu. A halin yanzu da wannan tsari dai kamfanin ke rayuwa. Idan ka kebe kasashen Indiya, da Ghana, da Japan, da Afghanistan, da Crimea, da sauran kasashen da kasar Amurka ta sanya wa takunkumi, duk sauran kasashen duniya na mu’amala da wannan shafi. A halin yanzu an kiyasta cewa, shafin PayPal na iya karba tare da aika takardun kudade sama da 25 daga cikin nau’ukan kudaden duniya.
Yin rajista a shafin PayPal ba wahala. Bayanan da za ka bayar sun hada da sunanka cikakke, da adireshin Imel, da adireshin inda kake zaune, da kasar da kake zaune, da lambar wayarka, sannan da lambobin katin ATM dinka. Dangane da tambayarka cewa ko dole ne sai kana da taskar ajiyar banki sannan za ka iya yin rajista? Amsar ita ce: eh! Domin za a bukaci lambobin katinka na ATM, wanda ta hanyar lambobin ne za a iya zuba maka kudi a taskarka ta banki da ke kasar da kake. Wannan shi ne takaitaccen bayani kan shafin PayPal. Idan kana bukata kana iya ziyartar shafin a: www.paypal.com. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum, yaya akaji da kokari? Ni ma a taimaka mini da bayani kan Tsibirin Bamuda da yadda zan yi amfani da password wajen kare wasu ayyukana daga miyagu.
Nagode. Muhammad Bala: [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai. Ka duba akwatin Imel dinka, na aika maka abin da ya sawwaka. Allah amfanar da mu baki daya, amin.
Assalamu Alaikum Baban Sadik da fatan kana Lafiya. Don Allah ina so ka fada mini shekarun “Farfesa Tim Bernes-Lee,” Wato Baban Internet.
Muhammad Izzuddin: [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai. Shekarun “Baban Intanet” dai a halin yanzu sun kai 61. Domin an haife shi ne a ranar 8 ga watan Yuni, shekarar 1955. Da fatan ka gamsu.
Assalama alaikum, don Allah Baban Sadik, ina so in san su wane ne ke da alhakin mallakar fasahar Intanet? Sannan, sai sun ba da umarni ne ake bude shafin yanar sadarwa (website)? Shin, idan sun ga dama suna iya rufe maka shafin yanar sadarwarka ne bisa wani dalili, kuma suna karbar haraji ne a gurin masu shafukar yanar sadarwa? Allah ya sa ka fuskanci tambayata, ya kuma baka ikon amsa min. Nagode. Allah ya kara basira amin.
Musa Ibrahim Gala: [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai. Babu wata kasa da ta mallaki Intanet gaba dayansa a halin yanzu. Duk da cewa fasahar ta samo asali ne daga kasar Amurka, amma a halin yanzu ta yadu ko ina a duniya. Babu wata kasa da za ta iya kulle ta gaba daya ta hana kowa amfana da ita. Amma kowace kasa na iya hana wani bangare na Intanet daga isa na’urorin mutanen kasar. Misali, kasar Saudiyya ta killace wasu shafuka na Intanet da suka danganci kasar Isra’ila, da dukkan shafukan batsa; ko da ka nemo wadannan shafuka a kasar ba za ka same su ba. Wannan shi ake kira “Cyber Censorship.” Na biyu, ba wata kasa da ke bayar da umarni kafin a bude wani shafin yanar sadarwa. Daga kwaryar dakinka, kana iya zama ka gina shafinka na Intanet, in har za ka iya, sannan ka biya kudin hidimar adana maka shi ga kamfanonin da ke wannan aiki, tare da yin rajistar suna ko adireshin gidan yanar, duk ba matsala. Babu wata kasa da sai an nemi izninta ake iya wadannan abubuwa.
Dangane da rufe maka shafi, ya danganci kamfanin da ke adana maka shafinka. Misali, akwai wasu shafuka masu dauke da bayanan da kasar Amurka ta haramta yada su, wannan ya sa hukumar kasa ta rufe shafukan, ta hanyar tursasa kamfanin da ke lura wa masu shafin da bayanansu, wato: “Web Hosting Company” ke nan. Wannan ya faru ne saboda kamfanin da ke dauke da shafin yana kasar Amurka ne. Amma da a ce kamfanin na kasar Rasha ne, sai dai kasar Amurka ta toshe adireshin shafin kadai, amma ba za ta iya hana wadanda ke wasu kasashen isa ga shafin ba.
Dangane da batun biyan haraji, babu wata kasa da ake biyanta haraji don bude shafin Intanet. Sai dai harajin cinikayya da kamfanoni ke biyan hukumomi, wannan kuma bai takaitu gare su kadai ba. Kudaden da za ka rika biya su ne kudin rajista na adireshin shafinka, da kuma kudin lura maka da shafi, wanda ta sanadiyyar haka ne ake iya neman shafinka a Intanet har a samu isa gare shi. Wadannan kudaden kuma za ka rika biyan kamfanin dake maka hidimar ne, ba wata kasa ba. Da fatan ka gamsu.
Salamu Alaikum, Baban Sadik, ya aiki? Da fatan kana cikin koshin lafia, Allah yasa haka amin. Don Allah Baban Sadik wai mutum zai iya saukar da babbar manhajar “Linud” akan babbar manhajar “Window”?Kuma zai iya amfani da wannan babbar manhaja a kan kowace irinkwamfuta, ko kuma akwai kwamfutar da baza ta iya dauka ba? Mungode da ka bamu damar aikomaka da tambayoyinmu kuma kana amsa mana, Allah ya karama daukaka da basira.
Shamsuddeen Kabir: [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai. Tabbas idan kana bukata za ka iya saukar da babbar manhajar kwamfuta nau’in Linud, har ma ka dora wa kwamfuta mai dauke da babbar manhajar Windows. Wannan abu ne mai yiwuwa, kuma shi ake kira: “Dual Booting” a ilimin kwamfuta na zamani. Sai dai kuma, dole ne ka tanadar wa babbar manhajar Linidu din wuri na musamman, ba wai a bangaren da babbar manhajar Windows take ita ma nan za ka jibga ta ba. Hakan ba zai yiwu ba. Misali, idan kwamfutarka mai dauke da babbar manhajar Windows na dauke da mizanin da ya kai 500GB, kana iya yanke kamar 150GB ka dora babbar manhajar Linud a kai. Wannan tsari na yanko wani bangaren babbar ma’adanar kwamfuta shi ake kira: “Partitioning.” Don haka, idan kwamfutarka ba ta da isasshen ma’adana, to, yin haka zai kuntata mata. Don haka, sai ka yi la’kari da yanayin girman mizanin kwamfutar taka tukun.
Kwamfutar da ba ta da isasshen ma’adana a babbar ma’adanarta (Hard Dribe), da wacce ba ta isasshen ma’adanar wucin-gadi (RAM), da wacce kuma kwazon sarrafa umarninta mai rauni ne (wato: Processor), duk ya kamata a guje wa dora musu kaya mai yawa. Domin yin hakan na iya hana su gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Kai kanka ba za ka ji dadin amfani da ita a wannan yanayi. Wannan kadan ne daga cikin abin da zan iya cewa a halin yanzu. Da fatan ka gamsu.