Sakonnin Sallah: Gwamnoni sun bukaci Musulmi su ci gaba da dabbaka darrusan Ramadan

A yayin da aka gudanar da ake ciki gaba da gudanar da bukukuwan karamar Sallah da aka gudanar jiya Alhamis a duniya gwamnonin jihohin Arewa sun bukaci al’ummar Musulmi su ci gaba da dabbaka darussan da suka koya a cikin watan azumin Ramadan a sauran rayuwarsa.Daga Neja wakilnmu Aliyu M. Hamagam ya ce Majalisar Gwamnonin […]

Sakonnin Sallah: Gwamnoni sun bukaci Musulmi su ci gaba da dabbaka darrusan Ramadan

Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu Shugaban Majalisar Gwamnonin Arewa da Gwamna Mukhtar Ramalan Yero na Jihar KadunaA yayin da aka gudanar da ake ciki gaba da gudanar da bukukuwan karamar Sallah da aka gudanar jiya Alhamis a duniya gwamnonin jihohin Arewa sun bukaci al’ummar Musulmi su ci gaba da dabbaka darussan da suka koya a cikin watan azumin Ramadan a sauran rayuwarsa.
Daga Neja wakilnmu Aliyu M. Hamagam ya ce Majalisar Gwamnonin Arewa (NSGF) ta bukaci al’ummar Musulmi su ci gaba da aiki da koyarwar da suka samu a watan azumin Ramadan, musamman yawaita bauta ga Allah da bin koyarwar Manzon Allah (SAW) kamar yadda suka yi cikin azumin.
Shugaban Majalisar kuma Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ne ya yi wannan kira a sakonsa na Sallah dauke da sanya hannun Babban Sakataren Watsa Labaransa danladi Ndayebo.
Gwamna Babangida Aliyu ya shawarci al’ummar Musulmi su ci gaba da kyawawan dabi’u na hakuri da hadiye fushi da tawali’u da kamun kai da suka koya a watan azumin Ramadan.
Sanarwar ta ce ya kamata dukkan jama’a su dauki bukukuwan karamar Sallah a matsayin dama ta sake sadaukar da kai da mika wuya ga Allah Madaukaki.
Ya ce bai kamata Ramadan ya kasance kawo karshen aikata ayyukan alheri da kyakkyawan makwabtaka da hakuri da juna da Musulmi suka ‘nuna a harkokin rayuwarsu’ a cikin watan Ramadan. Sai sanarwar ta yi kira ga ’yan Najeriya su yi amfani da wannan dama wajen rokon Allah Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali domin fita daga matsalar tsaro da ke fuskantar kasar nan.
Daga Kaduna wakilinmu Ismail Mudashir, ya ruwaito Gwamnan Jihar Mukhtar Ramalan Yero yana kira ne ga Musulmin kasar nan su sadaukar da rayuwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya da lumana a tsakaninsu da mabiya sauran addinai, kamar yadda shugabanmu Annabi Muhammad (SAW) ya yi a lokacin rayuwarsa.
A sakonsa na Sallah dauke da sanya hannun Kakakinsa Ahmed Maiyaki Gwamna Yero ya ce akwai bukatar ’yan Najeriya su dage wajen addu’o’i da kuma yin ayyukan da za su karfafa zaman lafiya da dorewar kasar nan.
Gwamnan ya ce, “Ina kira ga Musulmi su ci gaba da nuna halin ’yan uwantaka kamar yadda Allah Ya yi umarni a cikin Alkur’ani Mai girma ta hanyar karfafa zaman lafiya da hadin kai da ci gaban kasa. Musulunci addini ne na zaman lafiya, kuma hakikanin manufar addinin shi ne tabbatar da zaman soyayya da jin dadi a tsakanin mutanen duniya.”
Sai Gwamnan ya yi kira ga al’ummar Musulmi su ci gaba da dabbaka da darussan da suka koya a lokacin azumin watan Ramadan a sauran harkokin rayuwarsu, inda ya ce a bangarensu gwamnati za ta ci gaba da sadaukar da kai wajen yin adalci da rashin nuna bambanci a tsakanin daukacin al’ummar jihar ba tare da lura da kowane bambancin da ke tsakaninsu ba.
 Daga Lakwaja wakilinmu Usman A. Bello, ya ruwaito Gwamnan Jihar Kogi Kyaftin Idris Wada yana kira ga Musulmi su yi amfani da bukukuwan karamar Sallah wajen yi wa kasa addu’o’in hadin kai da dorewar zaman lafiya, kamar yadda yake kunshe a cikin sakonsa na Sallah dauke da sanya hannun mashawarcinsa kan harkokin watsa labarai Mista Jacob Edi.
A cikin sakon Gwamnan ya kuma yi kira ga malamai da limaman addini su ci gaba da yi wa kasa addu’a, inda ya ce wannan lokaci ne day a kamata jama’a su rika yin abubuwan da za su kawo ci gaban kasa.  
Gwamna Wada ya yaba wa Musulmi da Kiristan jihar kan yadda sukie zaune lafiya, inda ya bukaci su ci gaba da hakan domin ci gaban jihar.