Sakonnin Sallah: Shugabanni sun bukaci a ci gaba da yi wa kasa addu’a
A yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da bukunwan Babbar Sallah a yau Juma’a, shugabanni sun bukaci jama’a su ci gaba da yi wa kasa addu’a domin samun zaman lafiya da karuwar arziki. A sakon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki wanda ke gudanar da aikin Hajji a yanzu ya bukaci mahajjatan Najeriya su mai […]

A yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da bukunwan Babbar Sallah a yau Juma’a, shugabanni sun bukaci jama’a su ci gaba da yi wa kasa addu’a domin samun zaman lafiya da karuwar arziki.
A sakon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki wanda ke gudanar da aikin Hajji a yanzu ya bukaci mahajjatan Najeriya su mai da hankali wajen yi wa Najeriya addu’a domin samun habin kan kasa da zaman lafiya da farfabo da tattalin arziki tare da rokon Allah Ya kara wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari lafiya. Ya ce, “Yin addu’a ga kasa da shugabanninta abu ne mai muhimmanci, domin idan ’yan kasa suka yi haka, kamar sun yi wa kansu addu’a ne, saboda duk alheran da suka samu kasa da shugabanni, nasu ne.”
Sanata Saraki, ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Kakakinsa, Yusuph Olaniyonu ya raba wa ’yan jarida.
Shi kuwa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, a sakonsa na Sallah, ya shawarci al’ummar Musulmi ne su kwato Musulunci daga hannun masu guluwi da suke bata wa addinin suna.
Jigon na Jam’iyyar APC ya bayar da shawarar ce a shekaranjiya Laraba domin taya al’ummar Musulmi murnar Babbar Sallah, inda ya ce al’ummar Musulmi suna fuskantar babban kalubale, musamman yadda wabansu masu tsattsauran ra’ayi suke kokarin cire tausayi da jinkan al’umma daga addinin.
Atiku ya nuna takaicinsa, kan yadda masu tsattsauran ra’ayi suka jawo kassara tattalin arzikin Arewa da jirkita zaman lafiya da jin dabin al’umma, musamman a Arewa maso Gabas.
Alhaji Atiku Abubakar, wanda shi ne Wazirin Adamawa, ya bukaci a tashi tsaye wajen tantancewa da baukar mataki domin shawo kan tsaurin ra’ayin addini daga balibai da sauran mabiya addinin.
Shi ma a nasa sakon Sallah, Kwamandan Hukumar Tsaro ta Sibil Difens ta kasa, Abdullahi Gana Muhammad, ya taya al’ummar Musulmi murnar Sallah sannan ya yi kira da su yi koyi da koyarwar Manzon Allah Muhammadu (SAW) a cikin al’amuransu na yau da kullum.