Sakonnin waya 15
Jinjina ga Gwamnan JjigawaShugabannin kananan hukumominmu na Jigawa ku tuna fa da cewa gwamnatin rabon gado ta wuce, ku yi wa talakawa aikin ci gaban raya karkara don kun san zuwan Mai girma gwamna alfarma ce gareku. Ku shugabannin kananan hukumomi tunda ansarara muku ga shi kuna kan kujerunku na mulki kada ku sake satar […]
Jinjina ga Gwamnan Jjigawa
Shugabannin kananan hukumominmu na Jigawa ku tuna fa da cewa gwamnatin rabon gado ta wuce, ku yi wa talakawa aikin ci gaban raya karkara don kun san zuwan Mai girma gwamna alfarma ce gareku. Ku shugabannin kananan hukumomi tunda ansarara muku ga shi kuna kan kujerunku na mulki kada ku sake satar kudinmu don da kuna da hankali da kun yi aiki, amma mu matasan masarautar Gumel, mazauna Abuja, to wallahi ku shiga taitayinku don ba za mu yarda mu bar miyagu a cikin jama’aba. Nagode. Daga Mohammad Sagir Maigatari
’Yan mata a bi iyaye
Dan Allah “yan mata ku rika bin umarnin iyayenku game da zaba muku mazajen aure. Ku daina kashe kawunanku, don an hanaku auren wanda kuke so. Allah Ya ba mu hakurin bin iyayenmu sau da kafa. Daga Abdul Aziz Maska Funtua 07039117305
Gwamna Ganduje ga malamai
Salam dan Allah Edita ina so a ba ni dama in yi wa Gwamnan Kano Ganduje tuni a kan malaman makarantar da tsohuwar gwamnati ta dauka na wucin gadi (temporary). Yau wata takwas ba albashi, ba takardar daukar aiki ta dindin (permanent offer) da aka yi musu alkawari. Gwamna a duba kukanmu.Daga Shehu Mansur Sule Getso, Jihar Kano
Shawara ga Shugaban kasa
Salam, Edita ka isar mini da shawarata ga shugaban kasar mu, Muhammad Buhari kan ya sa ido a kan sojojin da suke hanyoyin Abuja, saboda ana zarginsu da neman matan mutane, da kuma amsar cin hanci, da kuma takura wa masu hawa babura da ke neman na abinci. Saboda haka ni ke bai wa shugan kasa mai adalci shawara, ya kara sa ido a kan irin takurawar da ake yi wa talakawanshi. Daga Nafisat Hussein sunshine Birnin Gwari kaduna
Kira ga Shugaba Buhari
Edita don Allah ka ba ni dama inyi kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari a kan masu kira ya janye tallafin mai, ya tuna halin da talakawa za su shiga idan aka cire. Kuma ya dauki matakin toshe hanyoyin da tallafin yake zurarewa. Ya tuna irin son da talakawan Najeriya suke musu, kada ya yi abin da zai sa ya yi bakin jini, ya tuna irin zanga-zangar da aka yi a baya, lokacin da tsohon Shugaba Jonathan ya cire. Nagode. Daga PRO na zauren talakawan Arewa, wato Sanusi Khalifa Alhazawa 08063439892
Ta’aziyyar Tabature dandume
Edita ka ba ni fili in isar da sakon ta’aziyyata ga Gidan rediyon tarayya na Kaduna. Da kungiyar zabe ta Najeriya.da iyalinta da karamar Hukumar dandume da sauran mutanen da ke sauraron gidan rediyon Najeriya na Kaduna. Allah ya jikanta, ya sa ta huta amen. Daga Babangida M/fashi (Enb. Officer ) 08176135707
Mu yi wa Buhari addu’a
Allah ya ganar da talakawa Aminiya wai yaushe talaka zai gane cewa mun samu shugaba? a kasata ne gawa take rubewa a kan titi a baya, amma yanzu har akwai talaka da zai ce bai gani a kasa ba. Duk talakan da ya ce bai gani a kasa ba. To ya kalli sama zai ga soja a Sambisa. Muna yi wa Buhari addu’a Allah ya dafa masa a kan gina sabuwar Najeriya. Daga Usaini Yaro Kano Bichi. 08086568466
Bangajiya ga Sarkin Kano
Edita ina so ka ba ni dama in mika sakon bangajiya ga Ma martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi na 2, bisa ziyarar kwana 2 da ya kawo mana, mu al’ummar karamar Hukumar dambatta. Da fatan ya koma gida lafiya. Daga Auwalu Nakarkata, kofar Yamma dambatta (08102661967)
Kira ga Gwamna el-Rufa’i
Zuwa Ga Editan Aminya, Mai fadakarwa da ilimantar.da jama’a. Ko sai kun zabi sakon da ya yi muku ne .kuke turawa? A tura min sakona zuwa ga Gamnammu Malam Nasiru El-Rufai da ya ba ’yan adawa kunya da masu gajen hakuri; suna biye wa ’yan adawa da ya gyara mana.garinmu da Jihar Kaduna baki daya, kwatankwacin lokacint kana Ministan Abuja. Daga Nuri Officer.Total, P Z Zaria
Jinjina ga Aminiya
Salam. Edita ina so a ba ni dama in mika jinjinata ga Aminiya da iyaye da ‘yan uwa da ma shi kan shi Editan na gode. Amina Nasir K/Jaba Kano. 08106562103
A duba Sambo Dasuki
Allah Sarki,Talaka bawan Allah. Shin a duk Najeriya babu asibitin da za a duba lafiyar, Kanar Dasuki har sai ya je waje? To mu talakawan in rashin lafiyar ta same mu ai a gida ake duba mu, a cikin kangwayen da suke kira asibitoci. Don haka mu talakawan Najeriya ba mu goyon bayan wannan kotu. Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496 [email protected]