Sakonnin waya (2)
Munafunci dodo ne! Salam Edita ka ba ni dama in jaddada wa Sanata Ali Ndume na Borno da ya sani cewa munafunci dodo ne yakan ci mai yinsa. Gaba dai gaba dai Sanata Ahamed Lawan, jagoran al’ummar Yobe ta Arewa. Daga Garba Sabiyola Gashu’a Jihar Yobe 07066581437 Ga ’yan kasuwa Assalamu alaikum Aminiya ku ba […]
Munafunci dodo ne!
Salam Edita ka ba ni dama in jaddada wa Sanata Ali Ndume na Borno da ya sani cewa munafunci dodo ne yakan ci mai yinsa. Gaba dai gaba dai Sanata Ahamed Lawan, jagoran al’ummar Yobe ta Arewa. Daga Garba Sabiyola Gashu’a Jihar Yobe 07066581437
Ga ’yan kasuwa
Assalamu alaikum Aminiya ku ba ni dama na yi kira ga ’yan kasuwar Najeriya su yi wa Allah da manzonSa albarkacin wannan wata mai Alfarma na Azumi su rage kudin kayan masarufi musamman ma nan Arewa domin a gaskiya tsadar kayan abinci yanzu haka ya yi yawa a Najeriya musamman ma dankalin turawa da lemo da ayaba da kusan dukkan kayan buda baki. ’Yan kasuwa a ji tausayin talakawa. Daga Ahmadu Manager Bauchi.08065189242
Soke shingayen sojoji ya yi daidai
Salam Editan Aminiya! Hakika gaskiya bada umarnin soke wuraren binciken sojoji (Cheakpoints) da Shugaban kasa ya yi Muhammadu Buhari hakan ya yi dai-dai, kazalika muna godiya ga Garkuwan Arewa Mista Solomon Dalung wanda ya mika koken talakawa ga Baba Buhari kan a kwashe wuraren binciken sojoji a fadin Najeriya, wanda hakarmu ta cimma ruwa. Muna godiya gare shi. Daga Mudassir Ibrahim Mando Kaduna 08024122559
El-Rufa’i bai kyauta ba
Hakika jama’a da dama ba su ji dadin daukar matakin daina ciyar da talakawa abinci daga asusun gwamnati a lokacin azumi da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya yi a bana ba musamman idan aka yi la’akari da yadda wasu jihohi ke kokarin yawaita bude cibiyoyin ciyarwa a sassan jihohinsu amma sai aka samu akasain haka a Jihar Kaduna..Yin hakan ba tsantseni ba ne, kuma babu wani abu da ciyarwar za ta ragi asusun jihar da shi. Gaba daya nawa za a kashe wajen ciyarwar? Kwanaki nawa za a ciyar da har ake tunanin ciyarwar na iya barazana ga asusun jihar?. A gani na,babu wani abu da wannan ciyarwar za ta ragi asusun Jihar Kaduna da shi. Shawarata ga Gwamnan shi ne ya kafa kwamitin da zai rika lura da yadda ake ciyarwar don kaucewa almundahana, ba wai ya soke ciyarwar kwata-kwata ba. Daga Mansoor Sa’id PRP Kano 07039215954 .
Allah Ya jikan danmaraya
Muna mika sakon ta’aziya ga ‘yan uwa da abokan arzikin marigayi Alhaji Adamu dan Maraya Jos, Allah Ya ba su ikon jure wannan babban rashi, Allahumma Amen. Daga Abdulmalik Sa’idu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496
Jinjina Ga Buhari
Hakika yunkkurin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yi na bada umarnin a cire wasu shingayen sojoji dake duba ababen hawa akan manyan hanyoyin kasar nan abin a yaba ne, musamman a bangarorinda ake da zaman lafiya. Idon aka yi la’akari da yadda sojojin ke kawo cunkoso da takura wa al’umma wajen amsar nagoro akan hanyoyin. Kuma shingayen ba sa hana miyagu wucewa da makamai ko miyagun kwayoyi. Daga Haruna Muhammad Katsina, Shugaban kungiyar Muryar Jama’a. 07039205659
Yabon gwani ya zama dole
Na fara da wannan ne, doman iny i jinijina ga Gwanan Jihar Sakkwato Barister Aminu Waziri Tambuwal, bisa ziyarar ba-zata da yake kaiwa ma’aikatu daban-daban na fadin jihar.
Hakika wannan abun a yaba ne, kuma a irin wannan ziyarar b-azata da yake kaiwa a ma’aikatun jihar, zai sanya ma’aikata su rika gudanar da ayukkansu yadda yakamata. A karshe nake janyo hankalin sauran gwamnoni su yi koyi da irin wannan namijin aikin, domin ta wannan hanya ce kaddi zai sanya ma’aikata su gudanar da ayukkansu yanda yakamata. Daga Aminu dankaduna Amanawa. 09035522212.
Ta’aziyyar harin bam
Ya Allah ka jikan wadanda sunka rasa rayukkansu a harin bom din tashar mota, a Baga. Su kuma wadanda sunka jikkata Allah ya ba su Lafiya. Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496.
Ta’aziyya ga iyalan danma-raya Jos
Salam, ina mika sakon ta’aziyya ga iyalan danmaraya Jos bisa rasuwarsa. Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa Aljanna ce makoma. Daga Ibrahim Sirajo Makarfi
Ga Gwamnan Bauchi
Salam, Edita ina so na fada wa Gwamnan Bauchi ya ji tsoron Allah Ya karasa biyan ma’aikata hakkokinsu. Daga Abdulrazak Bappa Azare
Addu’a ga ma’aikatan Aminiya
Salam, Edita, ina maku fatan alheri. Da fatan Allah Ya karbi ibadunmu. Daga Muhammad Ahmed Idris A. Kabuga Kano
Ga Gwamnan Bauchi
Aminiya don Allah muna son a mika mana sakonmu zuwa ga Gwamnan Bauchi da ya yi wa Allah ya biya wa ma’aikata albashin da suke bi har na tsawon watanni biyu su kuma masu aikin sharar hanya suna bin albashin watanni biyar. Daga Abbati Nesta Azare
Ga ’yan majalisa
Salam, Aminiya ku gaya wa ’yan majalisa kan talaka ya waye. Tunda mun gane ungulu da kan zabo kuka yi mana ku saurari kiranye daga mazabunku. Kuma girma da kimarku ya zube, tun da ba ku girmama uwar jam’iyyar da ta kawo ku majalisar ba. Sai hadamar mulki wanda ba shi muka tura ku ba. Daga Fatima daga Katsina
Solomon Dalung ya cancanta
Edita, ina son a baiwa Barista Solomon Dalung Shugaban Hukumar EFCC. Daga Hassan Babayo Direban Tanka Gombe.