Sakonnin waya 56

Matsalar man feturA gaskiya ya kamata Gwamnatin Najeriya da dillalan mai su dauki matakin gaggawa domin magance matsalar mai da ke addabar ’yan Najeriya. Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999. [email protected] Ga sababbin ministociSalam Edita ina yi maka fatan alhairi, koyaushe da addu’ar Allah ya daukaka gidan jaridarmu, abin alfaharinmu, Aminiya. Yau  ina so ka […]

Sakonnin waya 56
Sakonnin waya 56

Matsalar man fetur
A gaskiya ya kamata Gwamnatin Najeriya da dillalan mai su dauki matakin gaggawa domin magance matsalar mai da ke addabar ’yan Najeriya. Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999. [email protected]

Ga sababbin ministoci
Salam Edita ina yi maka fatan alhairi, koyaushe da addu’ar Allah ya daukaka gidan jaridarmu, abin alfaharinmu, Aminiya. Yau  ina so ka ba ni dama in taya daukacin ministocin da shugaba Buhari ya rantsar da su kan mukamansu. Ina  addu’ar Allah da fatan Allah ya sa su ba mara da kunya. Allah Ya sa su sauke nauyin da aka dora musu amin. Daga Muhd Ahmad Idris a kabuga Kano 08031818318

Kira ga Aminiya
Assalamu alaikum, Edita,  da fatan kana lafiya a wannan makon, zan yi kira ne ga wannan jarida Mai farin jini ta Aminiya da ta bude shafi na musaman da zai rika amsa tambayoyi game da, masarautu da kuma shahararun mutane, don mu kara sanin tarihin. Don kuwa duk al’ummar da ba ta san tarihinta ba, to tana tafiya ne a makance. Daga Bilya Tukur  Bakori  09033272527/07030225194 [email protected]

A taimaka wa ’yan gudun hijira
Salam  Edita . Don  Allah  ka ba ni  dama  in yi  kira ga  ga  Gwamnatocin Barno  da  Adamawa  da ma  Gwamnatin  Taraiyya  da su  taimaka wa ’yan gudun  hijira,  wadanda  suke  sansanonin  Adamawa  da  Barno. Domin  suna  cikin  wani  mawuyacin  hali  na rashin  lafiya  da karancin  abinci.  Daga  P R 0  na  muryar  talaka  na  karamar Hukumar  Bade. Daga Garba  Sabiyola  Gashu’a  07066581437  – [email protected]

Ta’aziyyar Mai aya
Kullu Nafsun zaikatul maut, Allahu akbar! Allah ya jikan Goggo mai aya. Ina taya ’yan uwanta da abokan arziki da ma abokan sana’arta bakin cikin wannan rashi. Allah ya sa ta huta, Ya sa Aljannar Fiddausi ce makomarta amin. Daga Kabir Sakaina Layin yangoro Malumfashi. 07039769596. [email protected]

Allah Ya jikan Mai aya
Inalillahi wa’inna ilaihi raji’un ! A madadin al’ummar garin Jingir, muna mika sakon ta’aziyyar mu zuwa ga ’yan uwan marigayiya, Hajiya Hafsa Sharada, wadda aka fi sani da Mai Aya kasancewarta haifaffiyar garin Jingir ce. Kuma muna amfani da wannan damar don  mika sakon ta’aziyyar mu zuwa ga Kamfanin shirya fina-finai na Kannywood daga karshe muna addu’ar Allah ya jikanta da rahama. Mu kuma idan tamu ta zo Allah yas a mu cika da imani amin. Daga Salim Abubakar Imam Jingir Shugaban kungiyar Muryar Talaka, reshen Jihar Filato 08067922200. [email protected]
Ta’aziya ga al’ummar Adamawa
Ta’aziya ga al’ummar Jihar Adamawa.Bisa ga rasa ’yan uwan su da suka yi a wannan makon.sanadiyar harin bom da wasu ’yan’ta’adda suka kai musu. Da fatan Allah Ubangiji ya jikan wadanda suka rasu ya bai wa wadanda suka jikkata lafiya, ya kuma tona asirin duk masu hannu a harin. Daga Haruna Muhammad Katsina.Shugaban kungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina.07039205659 [email protected]

Addu’a ga Shugaba Buhari
Allah ya sa wannan mataki da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na bada umarnin a kama dukkan manyan jami’an tsaro da ake tuhuma da hannu wajen badakalar sayen makamai, cikin shekarun da suka gabata ya yi tasiri wajen wajen magance matsalar tsaron da ke fuskantar kasar mu, yanzu haka. Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau, 08069807496. [email protected].

Tambaya ga Shugaba Buhari
Assalamu Alaikum Editan jaridar Aminiya. Don Allah ba ni dama in yi tambaya ga Shugaba Muhammadu Buhari a kan cewa, me ya yi zafi da ya sa aka kori manyan sakatarorin gwamnatin tarayya ba tare da an yi wa ‘yan Najeriya cikakken bayanin yin hakan ba. Da fatan dai babu wani lauje a cikin nadi. Daga Kwamared Nura Bello Daraja Kaset Gusau, Jihar Zamfara. 08032558025. [email protected]

Akwai barayin shanu a Katsina
Edita ka ba ani dama in roki Gwamna alhaji Aminu Bello Masari. Kan lallai ya yi wani kokari na kawar da barayin Shanu daga dazukan kasar Katsina. Domin idan ya cimma wannan kuduri, muka ribaci noma da kiwo a kasar Katsina kai har ma da Najeriya baki daya, to ya yi rawar gani. Kuma mun yaba da kokarinka kan yadda aka kwato dimbin shanun al’umma da aka sace a Runka da Batsari da sauran wuraren da makiyaya suke a jiharmu mai albarka. Allah Ya ba mu dawwamammen zaman lafiya da karuwar arziki. Amin. Daga Ibrahim kanen Mai-damu. 08054455268

Kira ga Gwmna Badaru
Don Allah a yi  mana ma’aikatar sarrafa fata da yin takalma da jakunkuna a kasar Hadeja. Domin in ka duba, a daukacin jihohin Arewa idan ka ga mai wanki da dinkin takalma, cikin mutum 10 bakwai ’yan Hadeja ne. Kai har ma a biranen Legas da Abuja. Gwamna Badaru sai ka duba Hadejawa. Daga Isa kwallu 09038945486.