Sakonnin waya 6
Tallafin talaka APCEdita ka ba ni dama in yi tsokaci game da tallafin da Jam’iyyar APC ta Muhammadu Buhari ta yi wa talakawa na biyan Naira Dubu biyar a kowane wata ga masu karamin karfi. Hakika muna jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari dangane da namijin kokarinsa wajen ganin an tallafa wa matasa marasa ayyukan yi, […]
Tallafin talaka APC
Edita ka ba ni dama in yi tsokaci game da tallafin da Jam’iyyar APC ta Muhammadu Buhari ta yi wa talakawa na biyan Naira Dubu biyar a kowane wata ga masu karamin karfi. Hakika muna jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari dangane da namijin kokarinsa wajen ganin an tallafa wa matasa marasa ayyukan yi, amma kuma sai dai kuma kash! ’Rijiya ta ba da ruwa, guga ta hana.’ Dalilin da ya sa na ce haka kuwa shi ne, ganin yadda yan majalisu sukayi watsi da kudurin baiwa talakawa marasa karfi tallafin naira dubu biyar a kowanne karshen wata. Hakika hakan ya nuna mana cewa, ’yan majalisun mu na Najeriya ba sa kaunar talakawa a fili. Don haka mu talakawan Najeriya muna nan muna zuba ido su fito su yi mana bayanin dalilin da ya sa suka yi watsi da wannan batu na tallafa wa masu karamin karfi. Daga Mohammed Mai kaset cross Kauwa karamar Hukumar Kukawa Jihar Barno Najeriya. 08138775015 [email protected]
Amana ce ministoci
Salam Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci dangane da sababbin ministocin da sabuwar Gwamnatin Buhari ta nada. Hakika masu iya magana suna cewa, kowace kwarya da abokin burminta,’ duba.da irin hangen nesan da Shugaba Buharin ya yi wajen zakulo wadannan mutane tabbas mun gamsu da nada su. Kuma ya kamata su san an danka amanar jama’a ne a hannunsu. Kuma ya kamata su gane yanzu Najeriya ba abin da take bukata sai jajartattun mutane wadanda za su dawo da martabar kasar. A karshe ina rokon Allah ya sa wadannan ministoci su zama hanyar warware matsalar kasar nan. Daga Aminu Abdu Ba ka noma, Sani Mainagge Kano 08099479880. [email protected]
Murna ga Solomon Dalong
Salam Editan Aminiya! Don Allah ku ba ni dama in taya Ministan wasanni da harkokin Matasa murnar samun wannan mukamin, wato Barrister Solomon Dalong, Allah Ya taimake su. Daga Mudassir Ibrahim Mando Jahar Kaduna 08034371602 (Facebook: Hausa Daily News) [email protected]
Addu’a ga rundunar hadin gwiwa
Allah ya sa wannan yaki da rundunar hadin guiwa za su fara a watan Janairun badi ya taimaka wajen kakkabe ayukkan kungiyar Boko Haram, da dangoginta a kasashemu. Daga Abdulmalik Sa’idu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496. [email protected]
Taya murna ga sababbin ministoci
Murna da fatan albasa za ta yi halin ruwa su bai wa Shugaba Buhari cikakken goyon baya wajen cire wa ’yan najeriya kitse a wuta.Da fatan Allah ya ba su ikon sauke wannan nauyi da ke a wuyan su.Mu kuma ’yan Najeriya mu taya su da addu’ar fatan alheri. Daga Haruna Muhammad Katsina. Shugaban kungiyar Muryar Jama’a reshen Jihar Katsina.07039205659 [email protected]
Ga sababbin ministoci
To sababbin ministocin Najeriya mu dai talakawan Najeriya babban kiran mu a gare ku shi ne, a gaskiya ya kamata ku cire son zuciya da kwadayi domin ciyar da kasar mu gaba. Saboda ta haka ne kawai za ku nuna wa ’yan Najeriya kishin kasa ne da ci gaban Najeriya a gaban ku, da fatan Allah ya ba ku ikon sauke nauyin da Allah dora muku amin.Daga Salim Abubakar Imam Jingir shugaban kungiyar muryar talaka reshen Jihar Filato 08067922200. [email protected]
Matsalar fetur ta dame mu
Edita ka isar mana da kukan mu ga Gwamnatin Najeriya, a gaskiya akwai damuwa sosai a bangaren samun man fetur a gidajen man kasar. Bayan tsadar da man ke yi yanzu ma, man ba ya ma samuwa cikin jin dadi, domin wasu na da man, amma ba sa fiddo shi domin sayarwa. Da fatan Gwamnatin Shugaba Buhari za ta yi wani abu akai. Daga Habib Central Market Katsina 07038653945 [email protected]
Shugabanni a cika alkawari
Assalamu alaikum Edita don Allah ka mika da sakona zuwa ga wadanda abin ya shafa cewa don Allah shugabannin mu na kasa ku tuna lokacin da kuke yakin neman a zabe ku talaka ya zama zinariyar da kuke hako wa a kasa, amma kash! Yanzu ku ne ke gasa wa talaka aya a hannun sa. Yau ga shi man fetur ma da talaka ke kuri da shi, musamman wannan lokaci na noman rani, fetur ya yi wuya koda da kudin. Wannan kuma kun kasa cewa uffan kan hakan. A karshe ina tunatarwa zuwa ga ’yan uwana cewa mu yi burin talaka ya ce kun ga ranar wane, ba wai ace ba mu ga ranar wane ba, musamman a Jihar Kebbi. Kuma Allah zai tambaye ku kan amanar da ya danka muku. Daga Nasiru Musa Maiyama Jihar Kebbi 08062206733 [email protected]
Sabon Shugaban EFCC ya yi daidai
Nadin sabon Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi , ya dace. Allah ya sa albasa ta biyo halin ruwa. Daga Alhaji Umar Foreber Gashua. 08108003333. [email protected].
Gaskiya ta yi halinta a Taraba
Assalamu alaikum Aminiya, mai farin jini ku ba ni dama in mika sakon tayin murna ga Gaggo A’isha Jummai ta Jihar Taraba, bisa hukuncin da kotu ta yanke na soke zaben jihar da aka yi a watan Mayun da ya gabata, inda ta aiyana Aunty Jummai a matsayin wacce ta lashe zaben, maimakon Darius Ishaku da hukumar zabe ta bayyana. Da wannan nake kira ga Aunty Jummai da ta riki al’ummar Jihar Taraba a matsayin tsintsiya madaurinki daya al’umma daya, ba tare da nuna bambancin kabila ko siyasa a tsakaninsu ba. A karshe muna addu’ar Allah ya ba ta ikon kwatanta mulkin gaskiya da adalci a tsakanin al’ummar Jihar Taraba baki daya amin. Daga Adamu Aliyu Ngulde, a Jihar Barno, 08032135939
Kira ga Gwamnatin Bauchi
Assalamu alaikum, Don Allah Aminiya ku Isar mana da sakonmu zuwa ga Gwamnatin Bauchi, mun ji ta fara tattaunawa kan yadda za ta jawo mai a jihar.’ To, muna kira ga gwamna da ya yi mana adalci mu talakawa ya fara samar mana aiki, kafin ya fara wannan cuku cukun. Daga Shugaban Muryar Talaka reshen Ningi, Mudassir Ibrahim Ningi. Jihar Bauchi [email protected]