Sakonnin waya (7)

Ta’aziyyar mutanen Mashema Assalamu alaikum  Editan Aminiya. Don Allah ku isar da sakonmu na ta’aziya zuwa ga al’ummar garin Mashema da ke karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara kan rasuwar ’yan uwa Musulmi sama da mutun 20 wadanda wasu mahara da ba a san kosu wane ne ba suka afka wa garin a ranar Litinin […]

Sakonnin waya (7)
Sakonnin waya (7)

Ta’aziyyar mutanen Mashema

Assalamu alaikum  Editan Aminiya. Don Allah ku isar da sakonmu na ta’aziya zuwa ga al’ummar garin Mashema da ke karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara kan rasuwar ’yan uwa Musulmi sama da mutun 20 wadanda wasu mahara da ba a san kosu wane ne ba suka afka wa garin a ranar Litinin da ta gabata. Allah Ya jikansu da rahama. Muna kuma mika sakon ta’aziya ga ’yan uwa, musamman Bello Shehu, mataimakin shugaban ’yan agaji na karamar Hukumar Maiyama da kanensa Aminu Shehu kan rasuwar mahaifinsu Malam Shehu Shugaba. Allah Ya jikansa da sauran ’yan uwa Musulmin da gafara. Amin.
Daga Nasiru A. Musa Maiyama da Malam Usman dankane Hunturu, Maiyama Jihar Kebbi [email protected]

Addu’a ga Buhari

Allah Ya kare mana adalin shugaba, to ’yan uwana ’yan Najeriya ku duba ku ga su Dasuki da Bafarawa da Bello Halliru da ire-irensu da yawa da ake zargi kan almundahana da kudin sayo makamai, jama’arsu, adinin u, yankinsu, kasarsu duk ko oho! Kansu da aljihunsu da  ’ya’yansu, su ne a gabansu. Alah Ka taimaki Buhari a kansu.
Daga Usaini Yaro Bichi 08086568466

Nasiha ga Baffarawa

Salam.  Editan jaridarmu ta Aminiya. Don Allah ka ba ni dama in maida martani  ga tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, kuma jigo a jam’iyyar adwa ta PDP.  Alhaji Attahiru Baffarawa,  ka ce wai Arewa ta hakura da maganar mulki ya dawo Arewa a wannan jarida ta Aminiya.  To, yau ga yadda Allah Ya yi wa  zabe.  Baffarawa, wato har karamar Hukumar Isah, har Jihar Sakkwato da Najeriya APC take mulki. Kuma yau ga inda PDP ta kai ka.  Don haka ’yan siyasa mu kula da yin alfahari  amma, duk da haka ku kula da abin da Allah Ya yi muku a hannun EFCC.  
Daga Malam  Murtala Amwa, Kanwuri Sakwato 080050332277.

Kira ga Hukumar FERMA

Aminiya ku gaya wa Hukumar Kula da hanyoyin Gwamnatin Tarayya FERMA da ta Jihar Katsina cewa, gidajen mai da ake ginawa a kan hanyar Katsina zuwa Dutsinma, masu gina su, sun tare hanyar ruwa a kofar shiga gidajen man nasu. Da fatan za ku je ku duba kafin damina ta zo. Domin kauce wa hadari  da ambaliyar ruwa ke iya kawowa idan ya hau kan kwalta. Da fatan za a duba domin gyara.
Daga Munir A Gambo Dutsinma.

Nasiha ga Baban al’umma

Assalam, Edita. ina yi mana fatan alheri gaba daya. Zan so a isar da wannan sakon ga Baba. Baban al’umma da ya ji tsoron Allah ya tuna da amanar da Allah, ya dora masa.Sannan za a tambaye shi amanar da aka ba shi. Don tsakani da Allah, al’umma na cikin wani hali a wannan.kasa a karkashin ikonka.
Daga Masoyanka, Mazunin Kudu. 07033929560

Ga kungiyar ZEDA
Salam, a gaskiya kungiyar ZEDA na zaluntar direbobi a bakin hanyar Zariya. Ya kamata ZEDA ta rubuta alamar ba a ajiye abin hawa a wuri, wato “No parking here,” wanda ya karya doka sai a ci tararsa, amma sai ka ga bako ko dan gari, wanda ya dawo daga wani gari yana sauka sai a kama shi a tilasta masa biyan tara. Kuma bai san an hana aje mota a wurin ba. Ina adalci a nan? Abin kamar fashi da doka.
Daga Bashir Sani Zariya, 08098582430.

Ga Dokta Mustapha Inuwa
Assalamu alaikum. Aminiya ku ba ni dama in yi jinjina ga tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Katsina, Dokta Mustapha Inuwa. Mu daliban Jihar Katsina mun yaba da salon mulkin lokacin kana Kwamishina. Allah Ya saka maka da alheri amin. Allah Ya sa ka zama Gwamnamu, amin.
Daga Lawai Aliyu Radda, karamar Hukumar Charanci.

Addu’a ga Aminiya

Salam. Edita ina yi maka fatan alheri Allah Ya kara daukaka Amintacciyar jaridarmu, amin.
Daga Ibrahim khaleel Jama’are. 08059465281.

Ga Minista Amaechi

Assalam. Don Allah ku gaya wa Minista Amaechi kada ya damu, da yardar Allah sai ya zama Shugaban Najeriya. Kuma daga nan Arewa ne mu za mu fara wannan yunkurin insha Allah.
Naka  Bala Aliyu Bodinga, Jihar  Sakkwato.

Kira ga Baba Buhari

Zuwa wasu kasashe alhalin ’yan kasa suna fama matsaloli nan da can, musamman bangaren man fetur da ya ki ci, ya ki cinyewa. Don haka muna kira gare ka da ka tsaya ka fara magance wadannan matsaloli da ’yan kasa suke ciki.
Daga Lawan Mailafiya Tumfafi, Kano, 08038703167 , 09093711445.