Sakonnin waya (91)
Kirana ga gwamnati Edita ka ba ni fili in yi kira ga gwamnatin tarayya da jihohi su yi kokari su sawo magunguna Malaria, wato zazzabin cizon sauro. Saboda mutanen Najeriya na fama ga zazzabin cizon sauro, manya da yara ba ma kamar kananan yara. Domin cutar tana shanye musu jini. Saboda haka iyaye mata a […]
Kirana ga gwamnati
Edita ka ba ni fili in yi kira ga gwamnatin tarayya da jihohi su yi kokari su sawo magunguna Malaria, wato zazzabin cizon sauro. Saboda mutanen Najeriya na fama ga zazzabin cizon sauro, manya da yara ba ma kamar kananan yara. Domin cutar tana shanye musu jini. Saboda haka iyaye mata a ci gaba da kwana cikin gidan sauro. Riga kafi ya fi magani. Daga Alhaji kasim Funtuwa 08063169007
Mu koma ga Allah
Addu’a ta ga Allah ya ku ’yan uwana talakawan Najeriya mu koma ga Allah, shi ne mafita ga rayuwarmu. Ka da mu yi biyu babu, bamu da kudi ba mu da mulki ba mu da ilmi; mu da ’ya’yanmu kun dai ga yadda malamai Musulunci da na Kirista da sarakuna da ’yan siyasa suke bal da mu. Sai mun tashi domin kauce wa fadanci da tumasanci, mu dogara ga Allah mu samu mafita. Daga Usaini Yaro Kano Bichi 08086568466
Murna ga Farfesa Mahmud Yakoub
Ina taya Farfesa Mahmud Yakoub murnar nada shi da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaben ta Najeriya (INEC). Da fatan Allah ya taya shi riko, tare da fatan zai yi koyi da shugaban da ya gada akan wannan kujera, Farfesa Attahiru Jega, wajen jajircewa akan gaskiya wajen gudanar da ayyukansa. Daga Isah Ramin Hudu, Hadeja. 08060353382
Jinjina ga Gwamna Masari
Salamu alaikum. Edita ina so ka ba ni dama na jinjina ma gwamnamu mai kishin talakawan jahar katsina da tai makon da zaibawa talakawansa masu sana.a da kudi da zai bada in allah ya yarda allah kate maki Gwamnanmu Aminu Bello Masari da burin alheran da yake so ya yi wa talakawan Jihar Katsina. To, jama’ar Katsina sai mun saurara. Daga Abdulraz Tukur kankara Unguwar Alhaji Hamza
Shari’ar Sambo Dasuki
Assalamu alaikum fatan flkairi ga dukkan masu karanta wannan jarida Edita kubani in tofa albarkacin bakina dangane da dage shari’ar Kanar Sambo Dasuki da wata Kotu a Abuja ta yi. A gaskiya mu ’yan Najeriya mun kagu mu ga an kammala wannan shari’ar. Domin kuwa kowa ya zuba Ido ne ya ga yadda za ta kasance. Muna fatan In har wannan zargin da ake yi masa ya tabbata Kotu za ta yi masa hukunci yadda ya dace da laifinsa. Muna addu’ar Allah ya ba mu zaman lafiya a kasar mu Najeriya , da ma duniya baki daya Amin. Daga Saidu Abdullahi Damaturu +2348039517322 [email protected]
Allah ne ya ba mu zaman lafiya
Bayani da ka yi cewa da Allah yana kama mutane domin laifinsu da ko dabba ba ta a bayan kasa, Ga wata ayar Allah ya ce ka da ku yi barna a cikin kasa bayan Allah ya gyarata. Wai kuma amincewa da shan kaye da Jonathan ya yi a ka samu zaman lafiya. Ina addinin mai wannan magana? Idan kare ya ga kashi mai maiko, kuma kura ta ga kare, ko karen nan ya dauki kashin ko kada ya dauka, dole kura ta yi gaba da shi. Abin nufi a nan ko Jonathan ya so, ko kada ya so sai Baba ya hau mulki. Wallahi Allah ne ya ba mu zaman lafiya ba amincewar kayen Jonathan ba. Baba Buhari kada ka yarda da duk mai cewa ka yafe wa azzalumi. Daga S D Kanam
Haba kungiyar Miyatti Allah!
Edita ka isar da sakona ga ‘ya’yan shuagabannin kungiyar Miyatti Allah ta Najeriya, ya kamata ku tsayar da gaskiya da adalci a cikin kungiyarku, domin hakan dai ne zai kawo hadin kai a kungiyar taku ta Fullani makiyaya a Najeriya. Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu, Gusau. 08069807496 [email protected]
Mun amince da kiran Sarkin Kano
Hakika mu talakawan Nigeria mun amince da kiran da mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II ya yi a kan cire tallafin man fetur ganin yadda tallafin ba ya isa ga talakawan Nigeria, kuma idan har gowmnatin za ta tashi tsaye domin tabbatar da an gyara matatun man Nigeria mu kuma talakawan Najeriya mu kara hakuri na dan wani lokaci za mu ga alfanun cire tallafin da fatan shugaba Muhammadu Buhari zai duba kiran na Maimartaban. Daga Salim Abubakar Imam Jingir, Shugaban kungiyar Muryar Talaka Reshen Jahar Filato.08067922200
Jinjina ga Aminiya
Salam Edita ka ba ni dama domin in yi jinjina ga jaridar Aminiya farin cikin al’umma, wadda ta zamo hantsi leka gidan kowa. Da fatan Allah ya kara daukaka Amin. Daga Garba Sabiyola Sa’idawa Gashu’a Jihar Yobe [email protected] 07066581437
Mun gamsu da wakilan Katsina
Gaisuwar fatan alheri da dukkan ma’aikatan Amintacciyar Jaridarmu mai albarka, gaisuwa ta musamman ga babban edita da fatan kana lafiya. Don Allah ka ba ni dama inyi jinjina da nuna goyan bayan al’ummar mazabar Katsina ta tsakiya ga dan majalissar wakilai ta tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya Hon. Sani Aliyu danlami. Hakika talakawan Katsina sun gamsu da yadda kake shiga cikinsu ba tare da nuna kyama ba. Sannan ka dauko matsalolinsu kana magancewa. Allah yayi jagora kuma yakara zuciyar tausayi da temakawa al’ummar jiharmu ta Katsina amin. Adamu Aliyu Amo Katsina. Sakataren kungiyar Muryar Jama’a, reshen Jihar Katsina.09097300909. [email protected]
Kira ga Gwamna Masari
Assalamu alaikum Edita. Don Allah ina kira ga Gwamna Masari da ya yi wa Allah ya sa a gyara ko kuma a yi face-facen babbar hanyar Katsina zuwa Kano, domin tun daga Charanchi har Katsina duk hanyar ta mutu, kullum sai an samu hadari a dan tsakanin. Kuma ga shi hanyar ta jama’a ce. Daga Gambo Isah Tudun-Kadir, Rimi L.G 09037313131, [email protected]
Kira ga Gwamna Lalong
Assalamu’alaikum. Edita don Allah ka ba ni dama in yi kira ga mai girma Gwamnan Jihar Filato dangane da ta’addancin da ke faruwa a kananan hukumomin Mangu da Barikin Ladi har ma da wani bangare na karamar Hukumar Riyom, ganin yarda a ’yan kwanakin nan hare-haren sai kara ta’azzara suke yi. To a gaskiya Mai girma gwamna ya kamata ka sake zage damtse, domin magance wannan matsalar da ta addabe al’ummar yankin ganin yarda a kullum sai kara samun asarar rayuka ake yi. Da fatan wannan kiran nawa zai isa ga Mai girma Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Bako Lalong. A karshe ina addu’ar Allah ya zaunar da jihar mu lafiya da ma Najeriya baki daya amin. Daga Salim Abubakar Imam Jingir, Shugaban kungiyar Muryar Talaka Reshen Jihar Filato 08067922200. [email protected]
A kawar da cutar cizon sauro
Ya Allah kawo muna karshen cutar cizon sauro a kasashen nahiyar mu ta Afrika. Kuma ya kamata gwamnatocin mu su kara dagewa, kamar yadda suka kawar da cutar shan inna (polio) a kawar da cutar cizon sauro a Afrika. Daga Naziru Abubakar [email protected]