Sakonnin waya(12)

Jinjina ga Gwamnamu Lalon Salam Edita. Don Allah ka mika min jinjina ta ga gwamnamu Simon Lalon kan gyaran manyan tituna garin Jos da yake yi, da son cigaban Filato da al-ummarta. Allah ya taimake shi mun gode al’ummar Filato saboda mun ga canji.Daga Zainab Sani 08166056642 Kira ga Gwamna MasariAminiya, ku ba ni dama […]

Sakonnin waya(12)
Sakonnin waya(12)

Jinjina ga Gwamnamu Lalon
Salam Edita. Don Allah ka mika min jinjina ta ga gwamnamu Simon Lalon kan gyaran manyan tituna garin Jos da yake yi, da son cigaban Filato da al-ummarta. Allah ya taimake shi mun gode al’ummar Filato saboda mun ga canji.Daga Zainab Sani 08166056642

Kira ga Gwamna Masari
Aminiya, ku ba ni dama inyi kira ga mai girma Gwamnan Jihar Katsina, ya Maigirma gwamna sanin kowa ne cewar tsohuwar gwamnati ta kasa wajen samar wa matasan jiha aikin yi, sakamakon haka sai ta sayo motoci na daukar matasa zuwa cirani, kuma zuwa ciranin ya haddasa wa matasa mummunar illa, kamar shaye-shaye da sauran su. Muna fata za a duba. Daga Aliyu Abba  PRP S/Gari KKR 08136731410.

Ga Gwamna el-Rrufai,
Assalamu Alaikum ,ina jin dadin karanta jaridar ku, mai dimbin alkhairi, kuma mai kare hakkin ’yan Najeriya. Edita ina So a mika kukana zuwa ga Maigirma Gwamnan Jihar Kaduna da ya sulhunta Da Hukumar Jarabawar NECO, domin a sakar mana Sakamakon jarabawar da muka rubuta, kafin fitowar guraben karatunmu na gaba. Daga Muhd Aminu Ikara 07035060958

Ga  Gwamna Masari
Ina kira ga mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari da ya sani cewar lokaci ya yi da Katsinawa suka gaji da gafara sa amma ba su ga kaho ba, ma’ana lokaci ya yi da za a bar maganar gwamnatin da ta gabata, tun da an kasa yi mata komai, sannan a fuskanci matsalolin da suka dabaibaye jiharmu, domin magance su. Allah ya yi mana jagira amin. Daga Adamu Aliyu Amo Katsina. Sakataren Kungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina. 09097300909

A daina tsangwamar Fulani
A gaskiya zarge-zarge da tsangwame tsangwamen da kungiyar Yarbawa zallah  ke yi wa kabilar Fulani a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sam bai dace ba. Kuma a gaskiya ya kamata gwamnatin tarayya ta shiga lamarin. Daga Salim Abubakar Imam Jingir, Shugaban kungiyar Muryar Talaka, reshen Jihar Filato 08067922200

Haba Gwmmnan Badaru
Assalamu alaikum  zuwa ga gwmmnan Badaru Jigawa karkasa zawarawan Jigawa kin aure fa? Kuma mata masu aure su zama zawarawa. Haba gawmmna wannan  ba koyar da tarbiyaba ce. Daga Yahaya Dutse jigawa 07032696136

Ga Gwamnan Bauchi
Ga Gwamna Mohammed Abubakar .ya kamata ka rika fadin abin da za ka iya kafin ka fadi, saboda har yanzu ba mu ga komai a kasa na alkawarin da ka dauka ba. Daga Salim Abubakar Bauchi 07067540950
Ga dakarun soja
A gaskiya kiran da dakarun sojan Nigeria suka yi wa ‘yan ‘kungiyar Boko Haram na su gaggauta mika wuya tun kafin a biyo masu ta bayan gida, hakan ya yi daidai, amma fa ina so dakarun sojan Najeriya ku gane cewa, ’yan kungiyar Boko Haram mutane ne marasa imani da kuma Don haka yana da mutukar wuya su bada kai bori ya hau sai dai in tsanani suka ji. Daga Dan da ke bin akidar Sunnah, Ababakar Lawal Gidan danmaye a Jargaba 08097627776/08091053120

Jinjina ga Yariman Bakura
Salam, Editan Aminiya Ina son ka ba ni dama inyijinjina ga shugabana kuma jagorana Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura, Sardaunan Zamfara, a bisa kyawawan dabi’unsa na alkhairi. Mu ’yan Zamfara sai fatan alkhairi gareka, Ubangiji Allah ya kara maka lafiya da imani., Kuma ya kareka daga sherin makiya amin. Daga Bashar danauta Talatarmafara, Jihar Zamfara.08030691963

Jinjina ga Sarkin Kano
Salam. Edita ina jinjina masa kan tambayoyi guda biyu kan aikin Makka. “1. Dole ne a yi jifar shaidan? 2. Don me ye aka kai mu ‘yan Afirka nesa, har muka shiga Munzdalifa?” Ya kara da cewa “ba’a bukatar amsa da gaggawa sai an dawo gida a tara shehunnan malamai. Sheiks don samun mafita.” Wannan ya nuna shi shugaba ne mai hangen nesa, Kuma wallahi na ji dadi. Allah Ya kare Mai Martaba Sarki. Daga. Alhaji S.Sulaiman Lassi. Bauchi State.08069447205

Kuka ga Sufeto Janar
Aminiya don Allah ku mika min kukana ga Sufeto Janar akan maganar yaron da ya mutu a garin Giwa sakamakon dukan da ’yan sanda suka yi masa.wannan DSP Zubairu Abubakar din kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna karya yake. Wallahi dan sandan da ya yi dukan har yaron ya mutu an yi masa canjin wurin aiki zuwa Zariya. Daga Isah Giwa.07061387536

Kira ga Shekarau
Salam. Don Allah a mika min sakona ga tsohon Gwamnan Kano, wanda ya yi shekarau takwas aka zo zabubbuka ko kansila babu, da ya yi shiru a siyasar kasa da ta Kano ba ka da ta cewa. daga dansawaba Yahaya 08169302773

Muna kewar Kwankwaso
Allah sarki Kwankwaso talakawan Kano mun soma kuka da rashinka. Allah ya kara maka lafiya, Allah ya raya mana Mustapha. Kana Abuja muna tare da kai, duk wanda ka ce mu canja a Kano wallahi sai mun canja shi, har me dillin-dillin din Allah ya kai mu 2019 kano sai abin da kwankwaso yace amma ban da dillin-dillin. Daga Abdulkadir Abba Sulaiman dangoro 08068541420

Ta’aziyyar mutanen Getso
Assalam sakon ta’aziyya ga al’ummar Musulmi, musamman Najeriya ’yan uwanmu da suka rasu a kasa mai tsarki da kuma al’ummar garin Getso da kewaye na gagarumin rashin da aka yi mana a hadarin mota da ya rutsa da iyalan Alhaji Halilu Ahmad Getso su 13.Da fatan Allah ya gafar ta musu, ya yi musu rahama, ya kai haske kabarinsu, ya kyautata tamu bayan tasu. Musulumi mu ji tsoran Allah a duk inda muke. Daga Yusif Muhammad Maihoto Sabonlayin Kara 08022518535