Sakonnin waya(9)

Kira ga Gwmnan YobeAssalama alaikum. Edita ina so ka ba ni dama in mika sako ga Gwamnan jIhar Yobe Alh Ibrahim Gaidam.  Akwai marasa aikin yi, ya kamata ka ba da aikin yi ga jama’a Maigirma Gwamnan Jihar Yobe.  Daga Adamu AC Potiskum. 07069383878. Godiya ga Gwamna MasariAminiya mun fara gani a kasa mu talakawa. […]

Sakonnin waya(9)
Sakonnin waya(9)

Kira ga Gwmnan Yobe
Assalama alaikum. Edita ina so ka ba ni dama in mika sako ga Gwamnan jIhar Yobe Alh Ibrahim Gaidam.  Akwai marasa aikin yi, ya kamata ka ba da aikin yi ga jama’a Maigirma Gwamnan Jihar Yobe.  Daga Adamu AC Potiskum. 07069383878.

Godiya ga Gwamna Masari
Aminiya mun fara gani a kasa mu talakawa. Ranar Asabar an ba da taki a garimmu, Jihar Katsina kan kudin  N1800 kacal. Godiya ga Allah. Muna godiya Gwamna Masari.  Daga Dr, Hamza Dan Kgdm CRC.

Ga Shugaban kasa
Salam Edita ina son ka ba ni dama in yi tsokaci a kan hana tawagar jami’an gwamnata da shugaban kasa ya hana ba wani abu ba ne illa barnar kudi saboda ba su da amfani sai zaman shan shayi. Na goyi bayan tawagar malaman addini, su ne kan gaba da kuma likitoci masu duba lafiyar alhazai. Wannan gaggarumin ci gaba ne.  Daga Alh Babangida M/fashi      08176135707.

An zalunci soja
Salam Editan Aminiya. Ina mai farin ciki ga shugaban kasa yake nuna aiki da gaskiya, sai dai kash, ina mai rokonsa da ya duba baya, ya tuna ko ya duba irin zaluntar sojan da ya sa suka bayar da takardar barin aiki, don kuntatawar kwamandojinsu. Wadanda suka bauta wa kasa a ciki da waje, har da yakin ECOMOG. amma sai ga shi ladar sallamarsu (pay up) an biyansu #201,329.69k na shekara 8.kai inda zai taimaka mai so ya koma, ko a yi musu hanyar samu a karkashin kasa.bslm.  Daga S. Ya’u Fayakwal, Jihar Ribas  07033145873.

Tsokaci ga Amniniya
Edita, ina son a ba ni dama don tsokaci a jaridarku mai albarka. Sace dukiyar talakawa ta zama ruwan dare mai gurbata kasa, Baba Buhari muna goyon bayanka. Allah ya taimake ka ameen.  Daga Lawal Mohd.Hayin Ojo Zariya.

Ta’aziyyar mutanen Yobe
Salam  Edita  Aminiya. Don  Allah  ku mika mana  sakon ta’aziyar  mu  ga  al-ummar  garin Damaturu  sakamakon  harin  kunar  bakin  wake  a tashar  mota,  wanda ya yi  sanadiyar  asarar rayuka  da dama.  Allah  ya jikan  su  da  rahama,  kuma  ya gafarta  musu;  Ya ba  wadanda  suka  jikkata  lafiya;  kuma  ya kiyaye  afkuwar  haka  nan gaba.  Mu kuma  idan ta mu  ta zo  yasa mucika  da kyau da  Imani.  Daga  Alhaji  Umaru  Foreber  Gashuwa. 08108003333.

Ta’aziyyar Sheriff Maulaya
Salam. Edita. Ka ba ni dama in mika sakon ta’aziyyata ga ’yan uwa da masoyan Sheriff Maulaya da ke Jihar Katsina da sauran kasashen Afirka. Allah Ya ba mu hakurin wannan rashi Ya kuma jikansa. Mu kuma in tamu ta zo Allah Ya kyauta karshen mu. Amin.   Daga Nasiru Galadanci 08035999108.

Ga Gwamnan Zamfara
Salam.Edita don Allah kabani filì a wanna jarida mai albarka don in isar da sakona ga Gwamna Shaihi ka yi wa Allah,  ka bai wea ilmi (EDUCATION) mahimmanci. Daga sulaiman m yusuf 08169964201.

Kira ga Shugaba Buhari
Salam Edita Aminiya ka taimake ni ka mika sako na ga Maigirma Shugaban kasa Muhammadu Buhari  da ya yi wa Allah ya dawo da doka da oda a Najeriya,  saboda bakin haure mata da suke zuwa da yara kanana  a Najeriya.  Wallahi abin takaici sai ka ga yara kamar na kasar Togo,  ’yan shekara  12 da 13 suna yin cikin shege. Akwai yara kanana masu yawa, wadanda ba ta hanyar aure aka same su ba, Musamman a biranen da suka hada daLegas da Ibadan da Ogun. Yara abin tausayi, kuma sakacin gwmnatin ba a ce domin ba ta kula da doka da oda shi ya sa muke kira da Shugaba Buhari da ya duba wannan lamari.  Daga Alhaji Jinjiri Mile 12 Legas  08111389999.

Ga Hukumar SSS
Aminiya ki ba ni dama  in sanar da Lawan Daura, ya yi  binciken ritayar da aka yi, a hukumar, sss cikin shekarar  2005.   Daga AbdulrRashid Rabi’u.      

Edita ban yi fushi ba
Salam. Edita me yas a ba ka son buga sakona? Na sha aiko da sako, amma ban taba gani an buga ba. Ban yi fushi ba, ina yi maka fatan alkairi. Daga ibrahim khalil jama’are 08059465281.

A bjarabawar Kanoiya kudin
Assalamu alaikum.  Aminiya ina kira ga hukumomin da abin ya sha fa da su dauki mataki akan matsalolin da  aka samu a jarabawar waec, har yanzu akwai wanda sakamakonsu  ya makale sakamakon kin biyan hukumar jarabawar kudin rajista dalibansu da wasu jihohi suka yi ciki, har da Kano. A halin yanzu daliban suna cikin wani hali mara dadi. Don Allah a duba wannan maganar da na yi a dauki mataki. Daga Abdulrashid dandago Kano  0703830403

Jinjina ga dan majalisa Kabir Shu’aibu
Saalm Edita da fatan kana cikin koshin lafiya amin. Don Allah ka ba ni dama in yi jinjina ga Kabir Shu’aibu dan majalisa mai wakiltar Charanchi da Rimi da batagarawa a kan kyautata wa jama’ar sa da yake yi. Allah ya tayaka riko amin. Daga Hon. Shamsu Muhammad Katsina. 07039878892.

Kira ga Gwamnan Katsina
Zuwa ga Edita bayan gaisuwa mai yawa da fatan alkhairi Allah ya sa haka amin bayan haka a  yau ina so a ba ni dama, domin in yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina a kan wani abu da yake faruwa, wanda ya dade yana ci wa mutane tuwo a kwarya. Ya maigirma gwamna a nan cikin garinmu Daura akwai mata wadanda suke aiki a karamar Hukumar Zango da Mai’aduwa, wanda a kullum idan suka je bakin titi suka tsaya tun karfe 7:30 na safe sai su kai har karfe 9:30 na safe a bakin titi. Daga nan kawai sai su koma gida. kuma wasu malaman makaranta ne wasu malaman asibitine amma kuma basason zuwa gurin aiki Kuma idan ba su samu wanda zai rage musu hanya ba, to ba za su je wurin aiki ba. Ya Maigirma gwamna don Allah ka tura wasu mutanenka su je su gani, amma abin yana bata wa mutane da yawa rai. Muna fatan za a yi maganin wannan a duk fadin Jihar Katsina baki daya.  Wassalam. Daga Hadi Tsohon Sarki, Daura-08148442241- 08085127726-08074O48751.

Muna goyon bayan Buhari
Aminiya  ’yar  amana  don  Allah  ku shaida wa jam’iyyar  PDP  cewa,  mu talakawa  muna  goyon  bayan  Shugaban  kasa   Buhari  akan  kokarin  da yake  na yakar  cin  hanci  da  rashawa  dari  bisa  dari.  Daga  Musa  nguwar Maiyasin,  danja  Jihar  Katsina  08155648155.