Sakwara da miyar karfasa
Assalamu alaikum uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara da maigida? Tare da fatan ana hakuri. Allah Ya sa mu dace amin. A yau na kawo muku yadda ake sakwara da miyar kifi. Za a iya yi wa maigida wannan girki da rana ko dare ko don tarbar manyan baki. Abubuwan da za […]
Assalamu alaikum uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara da maigida? Tare da fatan ana hakuri. Allah Ya sa mu dace amin. A yau na kawo muku yadda ake sakwara da miyar kifi. Za a iya yi wa maigida wannan girki da rana ko dare ko don tarbar manyan baki.
Abubuwan da za a bukata
• Doya
• Kifi; karfasa
• Manja
• Barkwano
• Albasa
• Magi
• Kori
• Garin tafarnuwa
HaDi
Uwargida ta fere doya sannan ta wanke ta Dora a wuta har sai ta yi laushi. Sannan sai ta Dauko turminta tana jefa dafaffiyar doyar tana dakawa har sai ta yi laushi. Za ta iya zuba ruwan zafi domin samun sakwara mai laushi.
A yanka albasa sannan a daka barkono ya yi laushi sosai kuma a wanke kifi yadda ba za a ji karninsa ba. A Dora tukunya a wuta sai a zuba manja. Sannan a zuba albasa ta Dan soyu sannan a zuba jajjagen tumatir har sai ya soyu. Sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa da kuma dakakken barkono
A zuba kifin sannan ruwa kaDan. Sai a rufe bayan mintin talatin sai a sauke.