Salihu Lukman ya fice daga Jam’iyyar ADC

Lukman ya bayyana hakan ne a cikin wasiƙar da ya aika wa Shugaban ADC na ƙasa, Sanata David Mark inda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya kira cin zarafi da nuna ƙyama

Salihu Lukman ya fice daga Jam’iyyar ADC

Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman ya fice daga Jam’iyyar ADC da kuma yin haɗakar jam’iyyun adawa.

Lukman ya bayyana hakan ne a cikin wasiƙar da ya aika wa Shugaban ADC na ƙasa, Sanata David Mark inda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya kira cin zarafi da nuna ƙyama da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu na kusa da shi ke yi masa.

Ya zargi El-Rufai da yin tasiri wajen ware shi daga harkokin shugabancin haɗakar adawa a Kaduna, duk da irin ƙoƙarin da ya ce ya yi wajen haɗa kan ’yan adawa a jihar.

Lukman ya kuma ce wasu shugabannin haɗakar sun fara amfani da irin salon siyasar da suka saba, abin da ya sa ya rasa ƙwarin gwiwar ci gaba da kasancewa cikin ADC.

Sai dai ya bayyana cewa, matakin da ya ɗauka ba ya nufin yana adawa da shugabancin jam’iyyar na ƙasa ba ne, illa dai yana da alaƙa ne da yadda aka riƙa mu’amala da shi a Kaduna.

 

Majalisar Ukraine ta amince da sabuwar gwamnati

Salihu Lukman ya fice daga Jam’iyyar ADC

Kotu ta hana FRSC tare motoci a titunan Kano

An gurfanar da wanda ya kashe matarsa da ƙona gida

Tags