Salisu Yusuf ya zabi kyaftin din Super Eagles

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da ke yin wasanninsu a gida (home base) Salisu Yusuf a shekaranjiya Laraba ne ya zabi kyaftin din dai zai jagoranci kungiyar. Kocin ya zabi golan kungiyar Ifeanyi Ubah Ikechukwu Ezenwa ne a matsayin kyaftin.  Haka kuma Ezenwa ne golan Super Eagles.  Ana sa ran shi zai jagoranci […]

Salisu Yusuf ya zabi kyaftin din Super Eagles

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da ke yin wasanninsu a gida (home base) Salisu Yusuf a shekaranjiya Laraba ne ya zabi kyaftin din dai zai jagoranci kungiyar.

Kocin ya zabi golan kungiyar Ifeanyi Ubah Ikechukwu Ezenwa ne a matsayin kyaftin.  Haka kuma Ezenwa ne golan Super Eagles.  Ana sa ran shi zai jagoranci kungiyar a wasan share fagen zuwa gasar cin kofin Afirka na masu yin kwallo a gida (CHAN) da zai gudana a ranar 11 ga watan gobe a tsakanin Super Eagles da Jamhuriyar Benin.

Wannan shi ne karo na 5 da ake gudanar gasar cin kofin Afirka na ’yan kwallon da ke buga kwallonsu a gida (CHAN).  Kuma ana sa ran a wannan karon gasar za ta gudana ne a Kenya a tsakanin 11 ga Janairu zuwa 2 ga Fabrairun 2018 idan Allah Ya kaimu.

Tuni koci Yusuf ya gayyato ’yan kwallo 30 da yanzu haka suke samun horo a Kano don tantance wadanda za su buga masa wasa da Jamhuriyar Benin.