Sallah: Aminu Ado ya gayyaci hakimai hawan sallah

Duk da tsige shi daga sarautar Kano, Aminu Ado Bayero ya gayyaci hakimai hawan bukukuwan sallah.

Sallah: Aminu Ado ya gayyaci hakimai hawan sallah

Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, wanda gwamnatin jihar ta tsige a baya-bayan nan, ya gayyaci hakimai zuwa hawan sallah da aka saba gudanarwa a jihar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, ya sanya wa hannu a ranar Talata.

Sanarwar mai kwanan watan 10 ga watan Yuni, 2024, ta umarci dukkan hakiman masarautar da su zo tare da masu unguwanninsu, mahaya dawakai da mawaƙa domin yin hawan sallah.

“Muna umartar dukkanin hakimai da su zo tare da masu unguwanninsu, mahaya dawakai da mawaƙa domin bukukuwan sallah.

“Kazalika, muna umartar dukkanin hakimai da su haɗu a fadar Aminu Ado Bayero da ke Gidan Nassarawa a ranar Asabar, Zhulhijjah 9, 1445 daidai da 15 ga watan Yuni, da misalin karfe 11 na safe don bayar da umarni ba tare da ɓata lokaci ba.

“Bayan zaman fada a ranar, Sarkin zai gana da dukkanin hakimai a fadar Nassarawa don yin ƙarin haske kan yadda hawan sallah zai gudana.”

Sanarwar ta ƙara da cewa an sanar da shugabannin ƙananan hukumomi game da shirin don taimaka wa hakiman samun damar shigowa Kano cikin sauƙi.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda