Sallah: Gwamna Abba ya ba wa ma’aikatan Kano kyautar N20,000

Tallafin ya biyo bayan kammala biyan albashin watan Mayun 2026, kuma an ware shi ne ga ma’aikatan matakai masu matakin albashi 01 zuwa 14 a ma’aikatun gwamnatin jihar da kuma ƙananan hukumomin jihar.

Sallah: Gwamna Abba ya ba wa ma’aikatan Kano kyautar N20,000

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da bayar da tallafin Naira 20,000 ga ma’aikatan gwamnati a faɗin jihardomin taimaka musu gabanin bikin Babbar Sallah mai zuwa.

Tallafin ya biyo bayan kammala biyan albashin watan Mayun 2026, kuma an ware shi ne ga ma’aikatan matakai masu matakin albashi 01 zuwa 14 a ma’aikatun gwamnatin jihar da kuma ƙananan hukumomin jihar.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Musa Tanko Muhammad, ya fitar, gwamna Abba ya bayyana matakin a matsayin nuna kulawa da tausayi ga ma’aikata.

Sanarwar ta ce tallafin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin wajen inganta walwala da martabar ma’aikatan gwamnati da ke taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin gwamnati a jihar.

“An ɗauki wannan mataki ne bisa la’akari da halin matsin tattalin arziki da kuma ƙarin buƙatun da bukukuwa ke haifarwa. Wannan tallafi zai taimaka wa ma’aikata su gudanar da bukukuwan Sallah cikin farin ciki tare da iyalansu,” in ji sanarwar.

Gwamnan ya ƙara da cewa matakin ya dace da manufar gwamnatinsa ta shugabanci mai haɗa kowa da kowa, tare da tabbatar da cewa babu wani ɓangare na ma’aikata da za a bari a baya wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka shafi jama’a.

Ya kuma sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da inganta jin daɗin ma’aikata, ƙara ƙwazon aiki da kuma gina ingantacciyar hidimar gwamnati domin amfanin al’ummar jihar Kano.

Haka kuma, gwamnan ya taya ma’aikata da al’ummar jihar murnar Babbar Sallah, tare da addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da albarka ga jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.