Sallah: Gwamnatin Nasarawa za ta biya albashin watan Yuni

Gwamnan ya umarni ƙananan hukumomin jihar su biya ma’aikata albashi albarkacin babbar sallah da ke tafe.

Sallah: Gwamnatin Nasarawa za ta biya albashin watan Yuni

Abdullahi Sule, Gwamnan Jihar Nasarawa

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce zai biya ma’aikatan jihar albashin  watan Yuni, gabanin bikin Sallah Babba da ke tafe.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a yayin taron ƙara wa juna sani da Kwamishiniyar Ayyuka ta musamman da ayyukan jin-ƙai, Magret Elayo, ta shirya a ranar Talata.

Ya bayyana hakan ne, a daidai lokacin da Gwamnan ya umarci shugabannin ƙananan hukumomin jihar 13, da su yi amfani da kuɗaɗen da suka tara wajen biyan albashin ma’aikata kafin bikin Sallah.

Ya ce, bikin Sallah mai zuwa ya bayar da damar gwada gaskiyar mahukuntan ƙananan hukumomin jihar game da kuɗaɗen ajiyarsu a banki.

“Yanzu ne nake ganin shugabannin ƙananan hukumomi da yawa, ba za ku ce shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ne, suka tilasta muku ba, na yi farin ciki da na ganku a nan, kamar yadda kuka sani ranar Lahadi za ta kasance ranar Sallah.

“Kuna da isassun kuɗin ajiya a asusun ajiyarku wanda ko kuɗi ba su zo daga Abuja ba, za ku iya biyan albashin ƙananan hukumomi daga asusunku na banki.”