Sallah: Yadda Mata Ke Shirin Kwalliyar Hijabi
Alamu sun nuna za a ci kasuwar hijabi a Karamar Sallar bana a wasu jihohin Arewa.
A shekarar 2021 mata sun dauki salon kwalliyar sallah da doguwar riga (Abaya), sai dai a bana alamu sun nuna hijabi ne zai ci kasuwarsa, musamman a Karamar Sallah.
Kamar yadda kowace shekara, bikin Sallah na zuwa da san salon kayan yayi da ake fitowa da shi, inda a bara aka yi yayin sanya Abaya, har ta kai ga aka dinga tsokanar wasu matan.
- Aisha Buhari ta yada bidiyon zargin sojoji da taimakon ’yan bindigar Zamfara
- Yadda aka sace Dala 50,000 a Hedikwatar APC a Abuja
A bana ma wani sabon yayin ya shigo, inda ake sa ran hijabi zai ci karensa ba babbaka da Kamar Sallah.
Aminiya ta zaga wasu wurare da ake sayar da yadikan hijabi, inda ta samu mata sun yi wa wuraren tsinke, ana ta hada-hadar sayen yadin dinka hijabi.
‘Da shi zan fita sallar Idi’
Maryama Ahmad, wata matashiyar ’yar kasuwa ce da ke sana’ar sayar da hijabi a unguwar Goron Dutse da ke birnin Kano, ta shaida wa Aminiya yadda kasuwancin nata a bana ya kaya.
“Ina sayar da hijabai tun ba yanzu ba, amma a bana yadda mutane ke sayen shi ya bambanta da na baya.
“Gaskiya ina samun ciniki a azumin wannan shekarar kuma da yawan wadanda suka sayi hijabaina sallar Idi za su je da shi.
“Ni kaina na tanadi wani guda daya mai kyau da shi zan fita Idi,
“Zamani ya sauya ana yin hijabai masu kyawun gaske, wanda idan mace ta saka za ka gan ta cikin mutunci,” in ji Maryam.
Farashinsa ya haura
Shi kuma dai Gaddafi Yusuf Sani, tela ne da ke siyarwa da dinka hijaban a kasuwar Rimi da ke Kano; ya ce hijabin ba shi da tsayayyen farashi a bana.
Ya kuma kara da cewa wanda aka fi saya domin bikin sallar shi ne wanda ake kira da dan Moroko ko Jilbab ko Egyptian.
Wani abin al’ajabi dai shi ne yadda da dama matan ke bayyana cewa kwaikwayon salon kawaye da kafofin sada zumunta na daga cikin abubuwan da suka bada gudummawa wajen haifar wannan sabon salon adon sallar.