Sallamar malaman da ba su kware ba ya kamata a yi daga aiki ko a kara horar da su?
A kwanakin baya ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da sanarwar cewa za ta sallami malamai da suka fadi wani jarabawar tantancewa da ta shirya, sannan ta maye gurbinsu da wadansu da za ta dauka. Wannan lamarin ya kawo rudani a tsakanin al’umma, yayin da wasu ke ganin ai ya kamata a sallame su a […]
A kwanakin baya ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da sanarwar cewa za ta sallami malamai da suka fadi wani jarabawar tantancewa da ta shirya, sannan ta maye gurbinsu da wadansu da za ta dauka. Wannan lamarin ya kawo rudani a tsakanin al’umma, yayin da wasu ke ganin ai ya kamata a sallame su a dauko wadanda za su koyar da kyau, wasu kuma suna ganin ai kamata ya yi a horar da su. wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayin jama’a, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:
Ya kamata a sallame su
– Malam Bashir R/Zaki
Daga Umar Akilu Majeri, Jigawa
Malam Bashir R/Zaki: “Ni a ganina bai kamata a bar bara gurbi suna aikin koyar wa ba tunda dai kowa ya san basu chanchanta ba, kuma irin wadannan malaman makaranta da alfarma ce ta kaisu ba chanchanta ba, su ne suke kawo nakasu a harkar ilimi a Najeriya. Don haka idan dai gwamnati da gaske take yi bai kamata a bar su suna aikin koyarwa ba domin babu abin da suke koya wa yara sai shirme da shirbici saboda da yawa daga cikin irin wadannan malaman ko sakandire basu kammala ba. Ta yaya wanda bai kammala makaranta ba zai iya koyarwa a sami karatu mai kyau, ballantana kwalliya ta biya kudin sabulu.”
Ya kamata a dawo da Kwalejin Horar da Malamai ne
– dan Sani
Daga Aliyu Baban Karfi Zariya
‘dan Sani Kakaki Zariya: “A ra’ayina bai kamata a koresu ba, a sake duba tsarin zai fi. Kamata ya yi a sake basu horo domin an dade ba a ba malamai horo. Kuma kamata ya yi gwamanati ta rika samar da kayan aiki a makarantu, da kuma kula da hakkokin malamai. Amma babban abin da ya kamata gwamanati ta yi shi ne ta maido da Kwalejin Horar da Malamai wato Teachers Collage, kasancewar nan ne ainihin tushen ingantaccen bayar da horo ga malamai.
Maganar kora ma ba ta taso ba – Malama Balkisu Malami
Daga Nasiru Bello a Sakkwato
Malama Balkisu Malami: “Maganar kora ma ba ta taso ba horo ya kamata a ba su. Ko a lokacin Sardauna ya yi ta daukar mutane aiki ba takardar kwarewa, sai ya ce a koya masu aikin, kuma suna yi da kyau. Yanzu ma kamata ya yi duk wanda aka samu bai da kwarewa a horar da shi. Kuma malaman da ba su kware ba din, za ka ga suna da fahimtar lamarin. Don haka idan aka horar da su, za su fi wadanda za a dauka.”
Bai kamata a kore su ba – Yusif Umar
Daga Umar Akilu Majeri, Jigawa
Yusif Umar Manajan Ultimate Café Jigawa : “Ni a ganina bai kamata a kore su ba. Kamata ya yi irin wadannan malaman a sake turasu karatu, sai a mayae gurbinsu da kwararrun malamai a daukacin makarantun da suke koyarwa. Su kuma aje a ci gaba da basu horo har sai sun samu kwarewa. Idan sun kammala karatu, a tura su wasu sabbin makarantu domin su ci gaba da aiki ba wanda suke koyar a da ba. Kasancewar kora daga aiki zai iya kawo tarnaki arayuwarsu tare da samun karuwar marasa aikin yi a kasa. Su kansu malaman da za a dauka ba a san wadanna iri bane tunda ai alfarma ce ke bata komai tun a wajen daukan aiki.”
Duk wanda ya fadi jarabawa a sallame shi – Gambo Dila
Daga Aliyu Baban Karfi Zariya
Gambo Dila Layin Baba Ahmed Tudun Wada Zariya: “Matakin da gwmanati ta dauka na sallamar malaman da suka kasa cin jarabawa shi ya dace, a canza su da wadanda suka cancanta, ba wai a tsaya wani bata lokaci ba wajen tura su karatu. Domin su kansu ba ‘ya’yansu a makarantun da suke koyarwa, na kudi suke turasu saboda son zuciya. Kuma su kansu sun yanke wa kansu hukunci saboda rashin karantar da ‘ya’yansu a inda suke. Don haka a ra’ayina a sallamesu a dauki kwararru.
Kamata ya yi a a horar da su – kasimu A. Sardaunan Matasan Assada
Daga Nasiru Bello a Sakkwato
kasimu Aliyu Sardaunan Matasan Assada: “Ya kamata a horar da su domin samun ci gaban ilmi. Horo ne ke mayar da wanda bai iya ba ya iya, ya samu ci gaba a fannin da yake. Idan ka ce ba za ka horar da wanda bai iya ba, to kwararrun ma za su kare. Kowa na son sanin makamar aikinsa, kuma horo ne kadai zai taimaki mutum ga hakan. Gwamnati ta ba da horo ga malamai shi ya fi batun kora domin hakan zai iya jefa kasar nan cikin karin masu rashin aikin yi a kasar nan. Dona haka gwamnati ta kula ta san abin da za ta yi.”