Sallar bana ba yabo ba fallasa
A ranar Talatar da gabata ne musulmi suka gudanar da bukukuwan sallah a ko’ina a fadin kasar nan inda shugabanni suka yi amfani da wannnan lokacin suka yi kira ga jama’arsu da su cigaba da zama lafiya a tsakaninsu tare da sadaukar da kai wajen taimaka wa juna kamar yadda Babbar Sallah da suka yi […]

A ranar Talatar da gabata ne musulmi suka gudanar da bukukuwan sallah a ko’ina a fadin kasar nan inda shugabanni suka yi amfani da wannnan lokacin suka yi kira ga jama’arsu da su cigaba da zama lafiya a tsakaninsu tare da sadaukar da kai wajen taimaka wa juna kamar yadda Babbar Sallah da suka yi take koyarwa.
A lokacin bukuwan, shugaba Jonathan Goodluck ya bayyana cewa majalisun tarayya ne za su tabbatar da shawarar da taron kasa ya amince da ita, tare da tabbatar wa jama’ar kasa ba shi da wata manufa ta boye, kamar yadda wadansu ke zargi.
A bana dai ma’aikata ba su ji dadin sallar ba saboda ta zo ne a farkon wata lokacin da ba a biya albashi ba, wanda hakan ya shafi masu sayar da raguna wadanda suka ji jiki a bana saboda rashin ciniki.
Sarkin musulmi ya roki malaman jami’a
Daga Sakkwato wakilinmu Nasir Bello ya ruwaito Mai martaba Sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku yana yin kira ga malaman jami’oin kasar nan da su janye yajin aikin da suka share tsawon wata hudu ana gudanar da shi, “ina kira ga malaman jami’o’in Nijeriya da su janye yajin aikin da suke yi su koma teburin shawara, hakan zai fi kyau ga kasar nan, ita kuma gwamnati ta saurare su.”
Alhaji Sa’ad ya kara da cewa, yajin aiki ya yi yawa, “ga likitoci ma suna cikin yajin aikin, ka ga wannan ma marasa galihu ne abin zai shafa inda za su rika samun salwantar rayukansu, su ma likitocin kasar nan ya kamata su yi la’akari da wahalhalun da masu karamin karfi ke ciki su kawo karshen wannan lamarin.’’
Mai martaba ya ce rashin tsaro da ke addabar kasar nan abin damuwa ne ainun wanda ya dace a magance wannan musibar ta hanyar samar wa matasa aikin yi, domin wadannan fitintinun mafi yawa suna faruwa ne saboda rashin aikin yi ga matasa.
Sarkin ya kuma jawo hankalin ‘yan siyasa, inda ya yi nuni da cewa, ‘Yan siyasa ba sa sanya gaskiya da tsoron Allah a cikin harkokinsu don ganin su inganta rayuwar tallakawa, wanda hakan ci baya ne ga harkar siyasa.
Mai alfarma Sarkin musulmi ya yaba wa hukumar alhazai ta Nijeriya kan tsari mai kyau da ta gabatar wanda har hukumar Saudiya sai da ta yaba. Sai ya kara ba da hakuri ga wadanda aka rage bisa ga umurnin gwamnatin Saudi Arebiya.
A jihar Sakkwato an samu gudanar da shagulgulan sallah lami lafiya ba tare da samun wani rahoton yamutsi ko tashin hankali a dukkan sassan jihar ba.
Saudiyya ta raba wa marayu da talakawa naman sallah a Kaduna
Daga Kaduna kuma wakilinmu Muhammad Yaba ya ruwaito cewa a lokacin bikin sallar kungiyar agaza wa Musulmi ta duniya da ke kasar Saudiyya (IIRO) ta raba wa marayu da mata da mazajensu suka rasu naman sallah kyauta a Kaduna, saboda koyi da koyarwar Manzan Allah Annabi Muhammad (SAW) wanda ya ce duk wanda ya taimaka wa maraya zai zauna kafada da kafada da shi a aljanna.
Babban daraktan kungiyar Shaikh Isma’il Ishak Hausawi ya ce,” Akalla mutane sama da dari bakwai ne suka amfana da wannan taimako. Sannan kuma akwai wadansu marayun da wadansu marasa galihu a kananan hukumomin kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu da kuma Zariya da su ma aka raba musu naman kyauta.’’
Sallar bana ta fi ta bara armashi a Damaturu
Daga Damaturu kuma wakilinmu Sani Gazas Chinade ya ce an gudanar da sallar cikin kwanciyar hankali tare da tsaurara matakan tsaro a dukannin masallatan idi da ke garin Damaturu fadar gwamnatin jahar Yobe.
Aminiya ta lura cewa a kusan duk masallatan idin da ke garin na Damaturu an samu mutane masu tarin yawa da suka halarci sallar, wanda hakan ke cewa harkokin tsaro ya inganta, sabanin yadda aka gudanar da bukukuwan sallar a shekarar da ta gabata.
A cikin hudubarsa, babban limamin masallacin idi na rukunin gidajen Waziri Ibrahim, Malam Ibrahim Muhammad Damaturu ya yi kira ga al’ummar musulmi ne da su rika yin addu’ar samun zaman lafiya a jahar da kuma kasa baki daya, ganin cewa jahar a baya ta shiga halin tabarbarewar harkokin tsaro. Ya kuma hori al’umma da su rika kula da hakkokin marayu da masu karamin karfi da ke cikinsu, ‘domin yin hakan na iya sanya Allah (SWT) ya tausaya mana ya fitar da mu daga cikin halin da muke ciki na tabarbarewar harkokin tsaro.’
Limamin ya kuma kalubalanci gwamnatin Jahar Yobe bisa ga yadda take fitar da kudade masu yawa wajen biya wa masu hannu da shuni kujerun aikin hajji, maimakon su juyar da wadannan kudaden wajen gina al’umma, kasancewar al’ummar na cikin bakin talauci, hakan shi ya fi, domin mutanen da ake biya musu kudaden aikin hajjin za su iya biya wa kansu da kansu.
Sai dai kuma hidimar bikin sallar ba ta yi armashi ga masu karamin karfi da ma’aikata ba, wanda hakan ya sanya da yawansu suka kasa sayen abin da za su yanka.
Bursunoni 20 sun samu ’yaanci a Gombe
Daga Gombe kuma wakilinmu Rabilu Abubakar ya ruwaito cewa, Shugaban karamar hukumar billiri Mista Iliya Bello Samya ya fitar da wadansu masu zaman gidan kaso 20 daga gidan yarin billiri a matsayin goron Sallah.
Mista Iliya Bello Samya wanda ya biya tarar da ke kan mutane ashirin din da laifuffukansu ba masu yawa ba ne, ya ce ya yi hakan ne domin su samu ‘yancin gudunar da bukukuwan sallah tare da ‘yan
uwa da iyalansu kamar kowa.
Shugaban ya kuma gargadi wadanda suka samu ‘yancin da su guji sake aikata wani laifin da zai yi sanadiyar sake komawarsu gidan Yarin.
A jawabin kwanturolar gidajen yarin na jihar Gombe Misis Dorathy Agur Atajiri ta ce hakan wani hobbasa ne da zai rage cunkoso a gidajen yari cikin sauki.
Ba a yi hawan sallah a masarautar Hadeja ba
Daga Dutse wakilinmu Akilu Majeri ya ce ba a gudanar da hawan Sallah a masarautar Hadeja ba saboda umarni da Mai martaba sarkin ya bai wa daukacin Hakimai da Dagatai da sauran masu unguwanni na yankin masarautar tasa domin juyayin rashin da aka yi amasarautarsa na wadansu manyan dogarawansa, domin a duk lokacin da ake gabatar da wani biki a fadar hankalin Mai martaba Sarkin ya kan dugunzuma saboda tunawa da wadanda suka rasun.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sakataren Sarkin Alhaji Maina Kawu, wanda shi ma Allah ne Ya tsirar da shi daga hadarin da ya ritsa da dogarawan da suka rasa ransu a kwanakin baya, ya ce wannan al’amarin da ya shafi masarautar ta Hadeja ba karamin abu ne da za su manta da shi a lokaci kankani ba.
An yi Sallar idi lafiya a garin Jos
Daga Jos kuma Wakilinmu Hussaini Isah Daga ya ce an gudanar da bukukuwan sallar idin layya lami lafiya a garin Jos babban birnin jihar Filato.
Rundunar tsaro ta hadin gwiwa, mai aikin samar da zaman lafiya a jihar Filato [STF] ta girke jami’anta a dukkan hanyoyin zuwa masallatan idin tare da binciken abubuwa hawa da haramta wasanni wuta
don ganin ba a samu wata damuwa ba a lokutan gudanar da bukukuwan sallar.A sakonsa ga al’ummar musulmin jihar Filato, Kwamandan rundunar tsaron Manjo Janar Dabid Enetie ya taya al’ummar musulmin murnar ganin wannan lokaci na babbar sallah. Ya yi kira ga al’ummar musulmin su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’in zaman lafiya a jihar da Nijeriya baki daya.
Shi ma a nasa sakon, babban limamin Jos Sheikh Balarabe Dawud ya yi kira ga matasa ne da su ji tsoran Allah kuma su yi biyayya ga iyaye da malamai da shugabanni.
A nasa sakon, shugaban majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’kamatis Sunnah ta kasa reshen jihar Filato, Dokta Hassan Abubakar Dikko ya yi kira ga al’ummar musulmi ne da su yi wa Allah godiya da ya ba su rayuwar da suka kai wannan lokaci na sallar idin layya.