Sallar bana: Marayu sun more

Marayu kimanin 600  da ’ya’yan marasa karfi ne suka shiga sahun takwarorinsu yara masu iyaye wajen gudanar da bukukuwan sallah karama ta bana cikin farin ciki da annushuwa  bayan da gidauniyar tallafa wa marayu wacce Alhaji Umar Lawal Atana ya jagoranta ta yi musu  sha tara ta arzikii inda ta dunka masu sabbin kayayyakin sallah […]

Sallar bana: Marayu sun more

Marayu kimanin 600  da ’ya’yan marasa karfi ne suka shiga sahun takwarorinsu yara masu iyaye wajen gudanar da bukukuwan sallah karama ta bana cikin farin ciki da annushuwa  bayan da gidauniyar tallafa wa marayu wacce Alhaji Umar Lawal Atana ya jagoranta ta yi musu  sha tara ta arzikii inda ta dunka masu sabbin kayayyakin sallah masu  tsada da takalma da riguna ‘yan kanti da dogayen riguna na mata da na maza.
Alhaji Umar Atana ya shaida wa Aminiya cewa a baya mutane kan baiwa marayu tallafin kayan da in sun sanya daka gansu  zaka gane  marayu ne, domin kayan da akan basu ba masu armashi  bane don haka gidauniyyar tayi ƙoƙari  kawar da haka “mun basu tallafin kayayyaki masu nagarta, kuma dukanin kayayyakin ɗinkakkune goggagu da sawa kawai suke buƙata, mun yi hakan ne domin ganin sun amfana da kayayyakin,” inji shi.
daukacin Marayun da ’ya’yan marasa karfi ne suka halarci farfajiyar masallacin ƙofar gidan Alhaji Lawan Atana da ke  Agege cikin sabbin sutturu cike da farin ciki da walwala bayan da aka sauko daga sallar idi a ranar larabar da ta gabata,   inda Jagoran gidauniyar ya bai wa ko wannen su goron sallah. Ya ce ya yanke shawarar gayyato marayun ne domin ya ɗebe masu kewa ganin babu iyayensu da za su yi masu haka,  hakan ne zai sanya mutanen da suka tallafa wa gidauniyar gane wa idanunsu aikin da aka yi da gudunmawar tasu.
“Jama’ar Agege sun ba da taimko kamar yadda ya kamata, domin mun tara fiye da Naira miliyan 5 a ƙasa da makonni biyu , na kan fita kasuwanni da wararen tafsirin watan azumi don nema wa marayun tallafi, a duk sanda na fita na kan komo da aƙalla Naira dubu 100 zuwa 300, akwai mutum biyu abokan juna da kowannensu ya  ba mu Naira dubu 500, akwai wani mutum da ban san ko waye ba ya aiko da atamfa sama da bandir 30, don haka ba abin da za mu ce sai dai Allah Ya  biya su da mafi alherin abin da suka bayar.’’
A karshe, ya bayyana cewa a nan gaba gidauniyar za ta samar wa marayun jarin kudi da za a bai wa wadansu amintattun mutane su dinga juya masu, ta yadda idan buƙatar a taimaka masu ta taso ba sai an fita neman taimako ba. “Baya ga haka muna biyan kuɗin makarantun isilamiyya da na boko ga marayun da mariƙansu ba sa iya biya masu kuɗin makaranta, akwai wata  marainiya da ta zo don a tantance ta ’yar kimanin shekara 12, da na tambaye ta wane yare take ji, sai da ta lissafa min kimanin yare guda shida, a ciki akwai filatanci da hausa da yarbanci da yaran ibo, baya ga turanci da larabci, ko da na tambaye ta wace makaranta take zuwa, sai ta ce ta gama firamare amma babu halin shiga sakandare, hakan ne ya sanya na ware fom ɗinta domin mu tallafa mata, a haka ne za ka ga yara masu hazaƙa amma sun gaza cinma manufarsu saboda rashin hali, don haka muka yunƙuro don taimakonsu,” inji shi.
Alhaji Sani Shu’aibu Sardaunan Agege, wanda shi ne shugaban gidauniyar taimakon marayun, ya yaba wa jama’ar Legas ganin yadda suka bai wa gudauniyar kyakkyawar gudunmawa wanda hakan ne ya sanya marayun samun damar gudanar da bukukuwan sallah cikin walwala. Ya ƙara kira ga matasa, waɗanda ya ce a yanzu sune masu hannu da shuni a Legas, da su ƙara himma a duk lokacin da aka nemi taimakonsu a wajan gudanar da aikin gina jama’a.  
Haka kuma wamitin taimakon marayu da gajiyayyu na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa reshen karamar hukumar Jos ta  Arewa da ke jihar Filato ya tallafa wa marayu da gajiyayyu sama da dubu 5 da kayayyakin abinci da tufafi.
Da yake jawabi a wajen raba wa marayu da gajiyayyun wannan tallafi, fitattacen malamin addinin musuluncin nan, kuma jigo a kungiyar, Sheikh Alhassan Sa’eed Adam Jos, ya yi  kira ga  kungiyoyin addinin musulunci su rika taimaka wa marayu da gajiyayyu. Ya ce  wajibi ne ga dukkan wadanda suka samu sarari su taimaka wa marayu. Ko dafa kan maraya mutum ya yi, yana da wani matsayi a ranar tashin alkiyama.
Ya ce don haka wannan kungiya ta fito da wannan shiri na tallafa wa marayu da gajiyayyu. “Muna so mu dauki nauyin karatun marayu da tarbiyarsu, ba kawai ba su abinci da tufafi ba.’’
Shi ma a nasa jawabin, shugaban kungiyar reshen karamar hukumar Jos ta Arewa, Alhaji Ya’u Musa Maigado, ya bayyana cewa ganin irin dubban marayun da aka samu a garin Jos sakamakon irin  rikice rikicen da aka yi  garin ne ya sanya kungiyar ta fito da wannan shiri. Sai ya mika godiyarsu ga  shugaban kungiyar na kasa  Sheikh Abdullahi Bala Lau  kan kirkiro da wannan shiri na tallafa wa marayu, wanda shi ne ya ba su damar kirkiro da wannan shiri a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Ya ce  baya ga wannan kwamiti na marayu da kungiyar ta kafa a karamarhukumar Jos ta Arewa,  akwai kwamitin da’awa da kwamitin makarantu da kwamitin masallatai da kungiyar ta kafa a wannan karamar hukuma, wadanda suke gudanar da ayyuka a halin yanzu.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kwamitin na taimaka wa marayu da gajiyayyun na kungiyar a karamar hukumar Jos ta Arewa, Ustaz Ibrahim Idris Zakariya, ya bayyana cewa babban aikin kwamitin shi ne ya kwadaitar da mutane kan su taimaka wa marayu da gajiyayyu don a sanya farin ciki a cikin zuciyoyinsu. Ya ce babu shakka wannan kwamiti ya yi iyakar kokarinsa wajen gudanarda ayyukansa.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar Filato kan ta taimaka wa  wannan kwamiti don a samu a taimaka wa dubban marayun da ake da su a garin Jos. “Wadannan marayu suna cikin mawuyacin hali. Duk al’ummar da ba ta taimakon marayu da gajiyayyu wannan al’umma tana cikin bala’i.’’
Daga nan ya yaba wa shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau kan karkiro da wannan shiri. Ya ce babu shakka mun ga cigaba a kasar nan ta bangaren tallafa wa marayu sakamakon   kirkiro da wannan shiri.
A Kaduna ma an samu taimakon kudi da suturu a lokacin tafsirin azumin watan Ramadan, inda a masallacin ’yan taya da ke Tudun Wada Kaduna, wurin da Sheikh Kabiru Gombe ya gudanar da tafsiri a bana, aka tara makudan kudi da yaduka da suturu domin taimaka wa marayu. A masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, inda Sheikh Ahmad Gumi ya yi tafsiri, nan ma an tara kudi da suturu domin taimaka wa marayu.
Ga dukkan alamu marayu a jihohi da dama  na kasar nan sun yi bikin sallar bana cikin annashuwa sakamakon tallafa musu da aka yi.