Sallar Bana: Marayu sun more da kayan Sallah tare da kiwon lafiya a Legas
AJjihar Legas a daruruwan marayu ne suka amfana da kayan Sallah baya ga kulawa da lafiyarsu da kwamitin tallafawa marayu na jihar da ke karkashin kungiyar Izalatul Bidi’a wa Ikamatus Sunna reshen Jihar Legas ya dauki nauyi. Shugaban kwamitin Alhaji Umar Lawal Atana ya shaidawa Aminiya cewa, marayu 600 ne suka amfana da tallafin kiwon […]
AJjihar Legas a daruruwan marayu ne suka amfana da kayan Sallah baya ga kulawa da lafiyarsu da kwamitin tallafawa marayu na jihar da ke karkashin kungiyar Izalatul Bidi’a wa Ikamatus Sunna reshen Jihar Legas ya dauki nauyi.
Shugaban kwamitin Alhaji Umar Lawal Atana ya shaidawa Aminiya cewa, marayu 600 ne suka amfana da tallafin kiwon lafiya da kayan Sallah mazan su da matan su, ya ce sun baiwa kulawa da lafiyar marayun ne domin ganin sun yi bukukuwan Sallah karama cikin koshin lafiya.
“Mun lura a baya zaka ga an yi wa maraya kayan Sallah amma bai sami ikon sanya wa ba saboda rashin lafiya haka ne ya sanya muka fito da tsarin kulawa da lafiyar su tun gabanin ranar Sallah a shirin da muka faro tun daga bara sannan a bana mun fara kulawa da lafiyar su tun kafin tsayuwar watan Ramadan inda muka dauko likitoci da masu taimaka masu wadanda suka yi ta kula da lafiyar marayun inda suka tantance su duk mai fama da matsala aka yi masa magani, mafi aka sarin su kanzo da zazzabi wasu kuma kurajen jiki da dai makamantan su, an basu magungunu an kuma yi masu allurai akwai yaron da muka kai babban asibiti na Legas aka yi masa aikin gwiwa, akwai wanda jinin jikinsa ya yi kasa sossai shima an kai shi an yi masa karin jini, akwai matar da mijin ta ya rasu ya bar ta tana da juna biyu ita ma mun dauki nauyin kulawa da dawainiyar lafiyar ta da haihuwar ta a asibiti haka muka yi tayi domin ganin Sallah ta riski marayun mu cikin koshin lafiya,” in ji shi.
Ya ce, sun yi wa marayu sama da 600 kayan Sallah a baa kana sun shirya masu kwarya-kwaryar walima ta bikin Sallah domin daibe masu kewa.
“Marayun mu sun kasance cikin koshin lafiya da walwala, wannan shi ne burin mu, suma marayu sunyi Sallah cikin farin ciki tamkar takwarorin su masu iyaye,” in ji shi.
A cewar sakataren kwamitin marayun na Legas Malam Shu’aib Muhammad babban kalubalen da kwamitin ya fuskanta a bana shi ne rashin wadatattun kudi duba da yanayi na matsin tattalin arziki da ya addabi al’umma, “Amma duk da haka muna masu godiya ga Allah muna kuma jinjina ga mutanen da suka bada gudunmawar su ta yin amfani da dukiyar su da wadanda suka yi da karfin su da kuma lokacin su, mun gode masu, wannan tallafi da muke baiwa marayun ba mu takaitashi zuwa lokacin azumi ko Sallah ba, Ah A muna tare da su a ko wani lokacin muna kulawa da ilimin su da lafiyar su, a lokuta da dama ma har da lafiyar iyayen su mata domin idan iyayen basu da koshin lafiya baza su sami ikon kulawa da marayun su ba, domin mu anan ba mu da gidan marayu, marayun mu suna gidajen su ne tare da iyayen su mata ko ’yan Uwan su fatan mu nan gaba mu mallaki gidan marayun da zamu dinga kulawa da su a ciki, don haka aiki ne babba mai tartare da lada da rabauta kuma kofar mu a bude take ga duk mai sha’awar taimakawa da abin da Allah ya hore masa a wannan aiki.”
Da yawa daga cikin marayun da suka amfana wadanda Aminiya ta zanta da su sun kasance cikin farin ciki tare da walwala ganin sun yi bukukuwan Sallah cikin walwala kamar takwarorinsu wadanda ke da iyaye hakazalika iyayensu mata da ‘yan uwansu sun bayyana farin cikinsu, inda suka yi addu’a ga wadanda suka ba da gudunmawarsu har tallafin ya isa gare su.