Sallar Bana: Mazauna Abeokuta sun yi salla a kulle
A daidai lokacin da al’umar Musulmi ke ci gaba da shagulgulan Sallah karama, a wani yanayi na annobar coronavirus da ta sauyawa shagulgulan sallar fasali a fadin duniya. A Abeokuta mazauna jihar Ogun sun yi nasu sallar Idin ne a halin kulle, biyo bayan matakan da gwamnan jihar Dapo Abiodun ya dauka na kulle jihar […]
A daidai lokacin da al’umar Musulmi ke ci gaba da shagulgulan Sallah karama, a wani yanayi na annobar coronavirus da ta sauyawa shagulgulan sallar fasali a fadin duniya.
A Abeokuta mazauna jihar Ogun sun yi nasu sallar Idin ne a halin kulle, biyo bayan matakan da gwamnan jihar Dapo Abiodun ya dauka na kulle jihar a kokarinsa na yaki da yaduwar annobar.
- Hotuna: Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Plateau
- Hotuna: Yadda aka yi Idi a gidan Dahiru Bauchi da wasu jihohin Najeriya
Masallatan Idi a Abeokuta sun kasance a rufe, kana jama’ar yankin sun yi sallar su ne a gida cikin hakuri duba da rashin armashin sallar.
Ga dai wasu daga cikin hotunan
yadda lamarin ya kaya a Birnin Abeokuta.