Sallar bana ta fi ta bara armashi — ’Yan Kasuwar Kudu

Sun ce duk da yanayin da ake ciki, Sallar ta f ta bara

Sallar bana ta fi ta bara armashi — ’Yan Kasuwar Kudu

Musulmi na jira a tayar da sallah ranar Idin Babbar Sallah a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba (Hoto: Musa Kutama – Tsohon hoto)

  • Raguna sun yi tsada—Masu saya
  • An samu karuwar tafiye-tafiye sama da bara

Wadansu ’yan kasuwar dabbobi a Legas sun yi ce Sallar bana ’yan kasuwar sun more fiye da bara duk da hauhawar farashin kayan masarufi, lura da yadda jama’a suke zuwa kasuwanni don sayen dabbobi da sauran kayayyakin masarufi domin yin Babbar Sallah.

A Babbar Kasuwar Dabbobi da ke Legas da wakilin Aminiya ya ziyarta ya zanta da wadansu daga cikin ’yan kasuwar wadanda suka ce a bana kasuwancin dabbobin ya fi garawa fiye da bara.

Malam Abdullahi Muhammad wanda ya kawo raguna daga Jihar Zamfara, ya ce kasuwar bana ta fi ta bara armashi domin a bara ’yan kasuwar sun yi kwantai, sun mayar da dabbobinsu gida Arewa, saboda ba su kare ba.

Ya ce a bana tun Sallah na da saura kwana 10 suka ga alamun kasuwar za ta yi armashi.

Ya ce babban rago a Kasuwar Abbatuwa ya kama ne daga Naira dubu 350 zuwa dubu 500, sai matsakaita ’yan dubu 120 zuwa dubu 250, ya ce kanana sun kama ne daga Naira dubu 50 zuwa 55.

Yayin da masu sayar da ragunan ke murnar samun kasuwa, masu saye kuwa suna kokawa ne kan tsadar ragunan inda suka ce kudin ya haura yadda suke tsammani, inda da yawa ke shiga kasuwar da niyyar sayen rago biyu sai su kare da sayan daya kamar yadda Baban Fatima ya shaida wa Aminiya.

Ya ce ragunan sun yi tsada kwarai, kuma tsadar ba ta rasa nasaba da tsadar man dizel da ake amfani da shi a mayan motocin da ke kawo dabbobin.

Malam Auwalu direban babbar mota ne da ke dakon dabobbi a Kasuwar Abbatuwa a Legas, ya ce a bara suna daukar dabbobin daga Arewa zuwa Legas a kan Naira dubu 300, amma a bana saboda tsadar man dizel a Naira dubu 900 suke dauka wato kudin ya ninka sau uku, don haka dole farashin ragunan ma ya ninninka. Aminiya ta leka kasuwannin kayan abinci na Mil 12 da ta Ilepo a Legas nan ma farashin kayan abincin sun dara na bara da tazara mai yawa.

A bangaren motocin sufuri kuwa masu harkar motocin sun bayyana wa Aminiya cewa a bana an samu karuwar tafiya Arewa a lokacin Sallah. Muhammed Fayama Jarimi, shi ne shugaban ’yan kwamasho da ke aiki a Tashar Isheri Kara a iyakar Legas da Ogun, ya shaida wa Aminiya cewa masu tafiya Arewa domin yin Sallah sun karu a bana duk da tsadar kudin mota.

Ya ce motocin safa-safa na zamani masu AC da ake kira loziriyus suna daukar fasinja daga Legas zuwa Abuja da Kaduna da Kano a kan Naira dubu 17 da 500 yayin da wasu ke dauka a Naira dubu 18 zuwa dubu 20.

Sai kananan motoci na dauka a kan Naira dubu 10 zuwa dubu 12, ya ce an samu karuwar masu tafiya Arewa daga Kudu domin zuwa gida yin bukukuwan Babbar Sallah.

A Jihar Kano, binciken Aminiya ya gano cewa farashin raguna da tumaki da shanu ya karu sosai idan aka kwatanta da farashin da aka sayar a bara.

Ragon da aka sayar a kan Naira 30,000 a bara, bana ana sayar da shi a tsakanin Naira 70,000 zuwa Naira 80,000.

Na Naira 50,000 a yanzu ya koma Naira 130,000 zuwa Naira 150,000. Haka lamarin yake kan farashin rakuma inda rakumin da aka sayar Naira dubu 100 a bara, a bana ana sayar da shi kan Naira dubu 200 ko sama da haka.

Mazauna garin Kano sun ce wannan tashin farashi cikin kankanin lokaci zai iya shafar kokarinsu na yin Layya inda mafi yawansu suka ce sun ajiye batun Layya a gefe.

Malam Ahmad Ali ya ce ganin yadda farashin dabbobin ya haure, a yanzu ba ya tunanin yin Layya gaba daya don a ganinsa ba zai iya sayen dabbar ba.

“Na fitar da rai ga yin Layya lura da yadda dabbobi suka yi tsada. ’Yan kudin da mutum yake da su ba za su ishe shi ya sayi dabbar ba. Ina ganin idan Sallah ta zo zan sayi kaji ne in yanka wa yara don kada su yi kwadayin na makwabta,” inji shi.

Malam Ali Muhammad, ya yi korafin cewa ya karade kasuwa na tsawon awanni don ya samu rago dan daidai, amma abin ya gagara.

Ya ce “Kafin in zo wannan kasuwar na je kasuwanni biyar ina ganin yadda farashin dabbobin yake amma sai na iske cewa kamar sun hada baki, don haka ina tunanin mutum ba ya da wani zabi illa ya sayi abin da halinsa.”

A daya bangaren kuma ’yan kasuwaar dabbobin sun alakanta tashin farashin da karuwar kudin safarar dabbobin zuwa Jihar Kano.

Malam Saleh Adamu ya ce batun karin ba laifinsu ba ne, domin suna yi wa dabba farashi ne daidai da yadda suka samu dabbar.

Wani mai sayar da raguna a Kasuwar Dabbobi ta Kwanar Badawa, Alhaji Ibrahim Ahmad, ya ce kudin kawo dabbobi a motar daukar kaya daga Maigatari a Jihar Jigawa zuwa Kano ya tashi daga Naira 150,000 zuwa Naira 200,000.

Alhaji Ibrahim, ya ce: “Ya kamata mutane su fahimci cewa ba haka kawai muke kara farashi ba, muna sayarwa ne daidai da yadda dabbobin suka zo mana.

“Muna kawo dabbobi daga garuruwa da kasashen da ke makwabtaka da mu, saboda mun san abin da muke da shi a kasa ba zai isa bukatarmu ba. To sai dai a inda gizo yake sakar shi ne kudin da muke biya wajen dakon dabbobin zuwa Kano,” inji shi.

Haka ’yan kasuwar sun koka game da yadda tashin farashin ya shafi rashin sayen dabbobin a Kano.

Malam Safiyanu Musa, wani mai kasuwancin dabbobi a Kasuwar ’Yan Awaki, Tinshama, ya ce tsadar dabbobin ta shafi kasuwancinsa domin mutane ba sa iya sayen dabbobin kamar a baya.

Malam Safiyanu ya ce a rago biyu kacal yake sayarwa a rana amma a bara yana iya sayar da guda shida zuwa bakwai a rana daya.

Wani mai sayar da dabbobi a Kasuwar Dabbobi ta Gwauron Dutse, Alhaji Abba Muhammad, ya shaida wa wakiliyarmu cewa raguna sun yi tsada sosai a bana, sannan ya dora laifin hakan a kan tsadar abincin dabbobi.

Alhaji Abba ya koka cewa kudin abincin dabbobi ya ninka a bana inda ake sayar da buhun kowar wake a kan Naira 6,000 sabanin bara da ake sayarwa a kan Naira 4,000 zuwa Naira 4,500.

Ya ce kaikayin dawa da ake sayarwa Naira 1,500 a bara ya koma Naira 3,000 a bana, Buhun dusa na Naira 3,000 a bara ya tashi zuwa Naira 6,000.

Ya ce baya ga tsadar abincin, karancin dabbobin ma ya taimaka wajen kawo tsadarsu a bana.