Sallar layya: Kiristoci sun yanka raguna domin Musulmi -Fasto ya ciyar da fursunoni da nakasassu abinci a Kaduna

Wadansu Yarbawa mabiya addinin Kirista a Kudu maso Yamma sun shiga sahun al’ummar Musulmi wajen sayen raguna su yanka suka kuma raba naman ga mabuka Musulmi a ranar Sallar Layya.daya daga cikinsu da ke zaune a Ibadan, mai suna Mista Lere Oba Ni Jesu, ya shaida wa Aminiya cewa, “ A kowace shekara ina sayen […]

Sallar layya: Kiristoci sun yanka raguna domin Musulmi -Fasto ya ciyar da fursunoni da nakasassu abinci a Kaduna

Wadansu Yarbawa mabiya addinin Kirista a Kudu maso Yamma sun shiga sahun al’ummar Musulmi wajen sayen raguna su yanka suka kuma raba naman ga mabuka Musulmi a ranar Sallar Layya.
daya daga cikinsu da ke zaune a Ibadan, mai suna Mista Lere Oba Ni Jesu, ya shaida wa Aminiya cewa, “ A kowace shekara ina sayen ragunabiyu ko daya mai girma domin koyi da ’yan uwana Musulmi in yanka in raba naman ga ’yan uwa da makwabta da sauran mabukata, kamar yadda na ga Musulmi suna yi. Ina yin haka ne saboda Allah Ya wadata ni da abin sayen ragunan.”
Mista Oba Ni Jesu ya ce, “An haife ni a Unguwar Toka da ke Gusau a Jihar Zamfara kuma a can na yi karatu da koyon aiki. Yanzu haka kannena suna can. A matsayina na Kirista na fara yin layya ne shekara 8 da wuce, wato tun ina can Gusau kafin in dawo nan Ibadan da aiki. Muna da yawa a cikinYarbawa mabiya addinin Kirista da muke shiga kasuwanni sayen raguna da shanu domin yin Layya a kowace shekara.”
 “Kamata ya yi manyan limamai na musulmi da kirista da mu duka mabiya mu rika yin bukukuwanmu tare, domin Allah daya muke bautawa. Ni dai na yarda cewa babu wani bambanci da zai rika janyo fitina a tsakanin musulmi da kirista, shi ne dalilin da ya sa nake yin layya a kowace shekara,” inji Oba Ni Jesu.
 Shi kuwa Joseph Alani Akamo da Aminiya ta yi kicibis da shi a cikin kasuwar Bodija, ya ki amincewa a dauki hotonsa amma ya ce, “Ai wannan ba sabon abu ba ne gare mu mabiya addinin Kirista a wannan sashi da ’ya’yanmu suke bin addinin da suke so kuma suke auren juna a tsakanin mabiya addinan biyu. Kuma muna yin shagulgulan bukukuwan Kirsimeti da Babbar Sallah ko karama tare, shi ne ma ya kawo ni cikin kasuwa domin sayen ragon da zan yanka da za mu ci naman da iyalina tare da rabawa ga mabukata.”
A Kaduna kuma wani limamin Kirista ya ciyar da fursinoni da nakasassu abinci saboda su ma su yi bukukuwan Babbar Sallah kamar kowa.
A lokacin da yake gabatar da abincin da sabulan wanki ga jami’an Babban Gidan Yarin Kaduna ranar Asabar da ta gabata, Fasto Yohana Buru ya ce “Na yi haka ne domin wadanda ke tsare a gidan yarin su fahimci cewa yau take Sallah kuma su ma mutane ne kamar kowa.”
Ya ce: “Mun yi wannan aiki ne saboda mu jakadun wanzar da zaman lafiya ne, saboda haka muka ga ya dace mu taimaka wa fursinoni da ke cikin kunci a nan wurin, musamman saboda yau rana ce ta nuna kauna da farin ciki. Da wannan muna ganin za a kara samun yarda da fahimtar juna tsakanin fursunonin da jama’ar gari da kuma tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kirista. Hakazalika, ya dace mu fahimci cewa mu ’yan uwan juna ne kuma wajibi ne mu rayu kafada da kafada da juna, dukkanmu asalinmu guda ne kuma gaba dayanmu ’yan Najeriya ne.”
Fasto Buru wanda shi ne Shugaban kungiyar Wanzar da Zaman Lafiya da Sasantawa ta (Peace Rebibal and Reconciliation Foundation) kuma limamin cocin Christ Ebangelical and Intercessory Fellowship Ministry da ke Unguwar Sabon Tasha, ya ciyar da fursinoni kimanin 300 abinci da kuma ba su sabulan wanka da wanki. Bayan haka ne, sai ya karasa gidan nakasassu da ke Kano Road, inda ya bai wa nakasassu kimanin 400 abincin Sallah da sauran kayayyaki bukatun yau da kullum.
Ya bukaci gwamnati ta kara himma wajen inganta rayuwar wadanda ke tsare a gidan yari saboda a cewarsa, “waje ne da ya kamata a ce yana gyara dabi’un al’umma da kuma samar da ci gaba.”