Salmanul Farisi: Abin misali ga mai neman shiriya (3)

Lokacin da Salmanul Farisi ya shaida wa Fada bukatarsa ta ga wane ne zai yi masa wasiyya, sai Fada ya ce: “Ya dana! Wallahi ban san wani mutumin da yake kan abin da muke kai ba, sai mutum daya a garin Nasibin, domin haka ka koma wurinsa ka lizimce shi idan za ka iya zuwa.”Salmanu […]

Salmanul Farisi: Abin misali ga mai neman shiriya (3)
Salmanul Farisi: Abin misali ga mai neman shiriya (3)

Lokacin da Salmanul Farisi ya shaida wa Fada bukatarsa ta ga wane ne zai yi masa wasiyya, sai Fada ya ce: “Ya dana! Wallahi ban san wani mutumin da yake kan abin da muke kai ba, sai mutum daya a garin Nasibin, domin haka ka koma wurinsa ka lizimce shi idan za ka iya zuwa.”
Salmanu ya ce: “Lokacin da ya mutu sai na tafi wurin mutumin Nasibin da ke wajen Turkiyya na ba shi labarina. Da abin da Fadana na baya ya  umarce ni.” Sai ya ce: “Ka zauna a wurina.” Salmanu ya ce: “Sai na zauna a wurinsa, sai na iske shi yana kan abin da abokinsa yake kai na alheri. Bai dade ba shi ma sai mutuwa ta zo masa. Lokacin da na ga alamar mutuwar, sai na ce masa: “Hakika ka san al’amarina gwargwadon sani, to zuwa ga wane ne za ka yi min wasiyya?” Sai ya ce: “Ya dana! Wallahi ban san wani mutum da yake kan abin da muke kai ba, sai mutum daya a garin Amuriyya, shi ne wane. Maza ka tafi gare shi!” Salmanu ya ce: “Sai na tafi gare shi. Lokacin da na sauka a wurin Fadan Amuriyya, sai na ba shi labarinsa na kuma zauna a wurinsa. Sannan al’amarin Allah ya sauka gare shi. Da mutuwa ta bijiro masa, sai na ce da shi: “Lallai ne kai, ka san al’amarina, to, zuwa ga wa za ka yi min wasiyya?”
Allahu Akbar! Allah Ka kara rahama ga Salmanul Farisi kan wannan shiga da fita da ya rika yi ba domin neman kudi ba, ba domin neman suna ba, ba ma domin neman ilimi kawai ba, a’a sai dai domin neman shiriya! Ya kamata mu lura Salmanu ba ilimi kawai yake nema a wannan tafiye-tafiye nasa ba. Domin da ilimi ne kawai yana iya samunsa a Sham ko Iraki, ba sai ya kara zuwa wasu wurare ba. Amma da yake shiriya yake nema, sai ya rika bin kan mutanen kirkin zamanin daya bayan daya. Kuma yana yin haka ne ta hanyar neman masanin addini na lokacin ya shiryar da shi zuwa ga mutumin kirki a cikin malaman wannan addini. Ba neman wanda ya fi ilimi daga cikin malama yake yi ba.   
To da ya fada wa Fadan Amuriyya bukatarsa ta neman ya shiryar da shi zuwa ga wanda ya dace sai Fadan ya ce: “Ya dana! Wallahi ba san wani mutum da ya saura a bayyan kasa da yake riko da abin da muke kansa ba a yanzu! Amma sai dai ina ganin zamani ya kusanto da za a aiko wani Annabi da zai fito daga kasar Larabawa da addinin Annabi Ibrahim, sannan zai yi hijira daga garinsu zuwa wani gari ma’abucin dabinai. Yana da alamomin da ba su buya, su ne yana cin kyauta amma ba ya ci sadaka. Kuma a tsakanin kafadunsa akwai hatimin annabta. Idan za ka iya ka koma wadancan garuruwa to ka koma.”
Doguwar tafiya mai wahala, daga gari zuwa gari, daga kasa zuwa kasa, Salmanu yana keta mila-milai a hanyoyi yana tsallake birni zuwa birni, tambayar da yake yi ita ce ina Salmanu zai zauna? Ina tafarki madaidaici yake?
Kana dauke da abincinka, kana tafiyya daga kasa zuwa kasa daga gari zuwa gari daga Fada zuwa Fada daga addini zuwa addini, wani lokaci Majusanci, wani lokaci Nasaranci. Wannan kana yi ne ya Salmanu duk saboda kokarinka na neman shiriya.
Bayan mutuwar Fadan Amuriyya, sai Salmanu ya ci gaba da zama na tsawon lokaci a garin. Daga baya kuma ya fara yunkurin tafiya Jaziratul Arab bisa fatar haduwa da wannan Annabi da Fadan Amuriyya ya ce masa yana tafe.
Salmanu ya ci gaba da cewa: “Sai wasu ’yan kasuwa Larabawa suka zo wucewa, na ce da su ku dauke ni zuwa kasar Larabawa zan ba ku wannan saniya tawa da wannan tunkiya tawa.” Ya sayar da kayayyakinsa domin kwadayin isa ga shiriya.
Salmanu ya ci gaba da cewa: “Sai suka dauke ni muka tafi tare har suka isa Wadil kurra, sai suka ha’ince ni, suka sayar da nig a wani Bayahude, na wayi gari bawa abin bautarwa. Suka tafi da saniyata da tunkiyata. Suka sayar da ni sayarwa ta bayi. Na zamo bawa a wurin wannan Bayahude!”
Allahu Akbar! Daga gidan daraja da martaba da izza ya koma gidan bauta da kaskanci, bayan doguwar tafiyar da ya yi a kokarinsa na neman shiriya! Mutanen da aka yi masa albishir Annabi na gaba da zai ceto duniya daga bata zuwa ga shiriya zai fito daga cikinsu sun ha’ince shi a lokacin da ya ba su amanar kansa da dukiyarsa domin isar da shi zuwa ga kasarsu! Shin Salmanu zai canja ra’ayi daga neman wannan shiriya ne ko kuwa zai ci gaba, a bayan wannan cin amana da aka yi masa?
Bari mu ji daga bakinsa: “Sai na zauna a wurin wannan Bayahude a matsayin bawa, ina yi masa hidima a gonarsa da hidimominsa duka. Ina zaune a wurinsa a matsayin bawa ne sai wani dan baffansa daga Yahudawan Bani kuraiza da ke Madina ya saye ni daga wurinsa.”
Allah Mafi girma, Ya ga karfin niyyar Salmanu ta neman shiriya sai ya hukunta wanda zai saye shi na gaba shi ne zai zama silar haduwarsa da Manzon Rahama (SAW) a Madina a shekaru masu zuwa. Sai Allah Ya kaddara Bayahude ya sayyar das hi ga Bayahude. Sai Salmanu ya tafi tare da wannan Bayahude zuwa Madinatul Munawwara.
Lokacin da Salmanu ya isa garin Madina ya ga yanayin kasarsa, ya ga dabinan da ke cikinta da sauran siffofinta, sai Salmanu ya samu yakinin cewa lallai wannan rana da ya fito nema ta yi kusan fitowa, alfijir din wannan Annabi yana daf da bullowa, kuma lallai shiriya zuwa ga haske daga duhun kafirci da bakar rayuwa ta Jahiliyya tana daf da tabbata! Domin duk alamun da Fadan Amuriyya ya gaya masa ga su nan a Madina.
Sai ya rika tunanin a zuciyarsa cewa: “Nan ne kasata, nan ne iyalina, nan ne wurin zamana, nan ne iyakar burina da aljannata. Nan ne wurin shiriyyata kai nan ne wurin haihuwata kuma a nan rayuwata take. Nan ne hasken wutar bautar Majusu da na rasa yake. Nan ne hasken da zai kawar da gurbatar da ke cikin addinin Nasara, kuma nan ne wurin da zai kawar da lullube gaskiya da karya da Yahudu ke yi.”
Salmanu ya ce: “Sai na zauna a Madina a matsayin bawan wannan Bayahude. Sai aka aiko Annabi Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam a Makka. Ya zauna a cikinta gwargwadon zama ban ji an ambace shi ba, saboda abin da na shagala da shi na bauta.”
Har Annabi (SAW) ya yi hijira zuwa Madina Salmanul Farisi bai san da maganar hijirarsa (SAW), hijirar Annabin da yake cike da shaukin haduwa da shi.
Me Salmanu ya yi da ya ji wannan Annabi da yake jira ya iso Madina? A biyo mu mako na gaba in Allah Ya yarda.